Monday, October 14, 2019

Gaskiya A Кi Ki, A So KiFarfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗu.GASKIYA A КI KI, A SO KI

1.                 RoƙonKa nikai Tabara ƙara basirata,
Ban hikima mai yawa ta gyara fahimtata,
Sa mini tsoronKa zuciyata Ka tsare ta,
          In bi umurninKa sau da ƙaf  ba saɓawa.

2.                 Mai rai duka na da lokacinai na taɓawa,
In waƙaci ya yi babu sauran walawa,
Komai ka gani a duniya zai ƙarewa,
          Ikon Allah kaɗai ya zan mai dogewa.

3.                 Halin jama’a yana ban tsoro sosai,
Ƙarshen lamari ka iske ya koma tausai,
Mai shawagi ka iske ya kasa ta kainai,
          Ya yi shiru babu wanda yaz zo cetawa.

4.                 Gawurtaccen azuraki dole gudun ka,
Mai son ƙarshen ƙwarai a dole ya ƙyale ka,
Halinka ya sa mutan ƙwarai na shakkar ka,
          Ka warwatse su makirai na ta matsowa.

5.                 Ramin ƙarya ba zai yi zurfi da yawa ba,
Ko an ga ruwa cikinsa ba za su daɗe ba,
Take su ƙwafe ba za ka iske guɓɓa ba,
          Кarshen ƙarya da masu so nata kokawa.

6.                 Ba matsiyaci kama da ƙaton mamugunci,
Mai haɗa cuta ya je ya noƙe ya yi ƙyarci,
Mai fatar mai akwai ya koma matsiyaci,
          Sharri ƙarshensa madugu yaka murɗewa.7.                 Ka haƙa rami cikinsa ka faɗi gigirce,
Son girma ya zubar da girmanka taƙaice,
Yau ga harshen maƙetaci an yi duƙunce,
          Ya shiga ramin da yah haƙa sai biznewa.

8.                 Yau ga giba da tsegumi an yi tsugunne,
‘Yan sauraro ba batun karkaɗa kunne,
Ga Suda ba ɗumi da hannu aka nune,
          Baki ɗaure wuya ya kai ba kubcewa.

9.                 Manyan iya ƙulle-ƙulle yau ta ƙulle su,
Ga su ga fili Huwallazi ya tona su,
Babu kare bin damo da su har tawagarsu,
          Кarshen ƙaiƙai kan masheƙiya za ya bicewa.

10.             ‘Yan a yi sai mun gani , ku zo ga shi ku shaida,
Mai kun-fa-ya-kunu Ya  gama kuma Ya yarda,
Mai tauhidi a dole zai dangane sanda,
          Alƙwalin Jalla fil azal bai tadawa.

11.             Ga wata ‘yar shawara aboki ta iyaye,
Kar ka yi sharri saboda ƙarshensa hawaye,
Fuska biyu na zubar da girma a kiyaye,
          Sai an tsare gaskiya shiri ke dacewa.

12.             Gaggawa ba ta yin kunu ba ta saba ba,
Saurin nema ba za ya kawo samu ba,
Kushe mutane ba zai hana su darajja ba,
Wa ya isa cewa lokaci ba ya tahowa?

13.             An shafa ma zuma ga baki sai hauka!
Had da kirari da ci da ƙarfi ga manyanka,
Romon sata ya sa ka kushe gabacinka?
          Ya zama wa’azi gareka ɗai ba ƙarawa.

14.             Tad da wuya dorina da kyau a ga fuskarki,
Wai gwanki ne ka tsegumin kyaun fuskarki,
Ya turo raƙumi a je a ga leɓenki,
          Wa ke da kamar ƙwarai cikinku ta burgewa.

15.             Hayyanka da ɓata ‘yan’uwa don a yaba ka,
Kaiconka da yaudara a san ta ga fuskarka,
In bone ya ci ka babu mai hoho kanka,
          Sharrin da ka haddasa mutane ka tunawa.

16.             Girman kai, ji da kai musiba ce babba,
Ɗanga, fahari, bugun gaba ba a gane ba,
Ni nac ce, wa ka yi idan ba ni ne ba?
          Кarshe bai kyau da rarahe aka ƙarewa.

17.             Wayon-a-ci, yanzu had da kai ga jidalin ga,
Ka gwaggeahe wuri kana ta baƙar darga,
Shaiɗan ya dambala ka had da sayo ganga,
          Gangumman Ɗan’ubayyu Malam ka kaɗawa.

18.             Girma ya ɓaci tun da Malam ya makabce,
Gemu, hana-ƙarya wanzamai sun kakkarce,
Ya baza hoda idon maza ya bobboce,
          Ya ce: “Jarƙaniya”, “A’uzu” muke cewa.

19.             Dole da takaici malami da shiga ɓanna,
Malam da kwaɗai da hasadar yankan ƙauna,
Kullum su ke gaban sahun suɗan kwanna,
          Ga rawani ya zube ana tattakawa.

20.             Kaza ‘yar tone-tone ta tone bonenta,
Ta ruga ya biyo har ya danne ta,
Ga zakaru na ganinta ba mai tanya ta,
Kowa ta gabansa yan nufa ba mai waigowa.

21.             Kura sunanki ko’ina mai-a-ci-wawai,
Mun ji awaki suna kashedi wurin karnai,
Sun ce, “Su yi hanzari su shaida wa bisaisai”,
          Ko ban fasa ƙwai ba ɗalibai na ganewa.

22.             Miƙe tsaye Rozo-rozo ai mun gane ka,
Buzuzu shi ya fallasa muna halinka,
Ya ce muna, “Dole-dole ta fita iskarka”,
          Shanshani ta ce, “Da kai da su ba ɗasawa”.

23.             Kasa ke ce uwa ga ƙwari mamugunta,
Ga Baƙi nan da Gajere ke sunka gabata,
Ke ƙyale Jannasuri ya faɗa asunta,
          Komarci ne munafuki ya ƙi tsayawa.

24.             Siffar Jimina haƙiƙa ɗai da ta tsuntsaye,
Jemage yay yi ɓad da sau ba tuntaye,
Shi Aku martabarsa na nan baka ɓoye,
          Hankaka, Zarɓi, Shamuwa ba ku iyawa.

25.             Kai tashi Biri maɓannaci an gane ka,
Je tambi Dila karo da mu ta ari hauka,
Kai dai Gafiya aradu ko mun ƙyale ka,
          ‘Yan sharanin maraice ba sa ƙyalewa.

26.             Ɓera ga saninmu ɗan hali ku ne manya,
Gafiya sunanka yai amo har a surayya,
Kun gama aikinku Mage ko ta tare hanya,
          In ku mayas, in ku dakata babu wucewa.

27.             Na tabbata sa ido kwaɗai yaka kawowa,
Baki da kwaɗai a nan saleɓa ka zubowa,
Lasan baki ga mai kwaɗai wa ka hanawa,
          Modibbo ƙuda wurin kwaɗai aka shurewa.

28.             Alhudahuda kau saninsa bai albarka ba,
Shehin masani halama dai ba a shirya ba,
Ni kau ga zaton da nay yi dai ba kai ne ba,
          Don alfarmar sani ƙana’a taka sa wa.

29.             Shashasha bunsuru akwai kissan kaura,
Kowa ya sanka kai kaɗai aka barara,
Ka ce: “Bana ka shirya wa fansarka ta bara”,
          Rago ya ce: “Maraba shege ka ƙiyawa”.

30.             Ba dai banza ba in ƙuda na bin walki,
In ba tusa ba to akwai warin baki,
Ko zawo ya tsure mu’anya tai tsaki,
          Ba shakka don gawai ƙuda ba su biyowa.

31.             Kura a yi hanƙuri abin daga Allah ne,
Suna ya ɓaci ko’ina ki biya nune,
Ke ci awaki da raguna had da mutane,
          Danƙa amana gare ki ba mai farawa.

32.             Giwa bukkar dawa karo ba ki saba ba,
Tilas namun dawa su yarda da ke babba,
Mai jayayya ya zaburo ban mu hana ba,
          Kashinsa da hannuwansa shi zai kwashewa.

33.             Ba wani naman dawa da zaki ka tsoro,
Кarya ce Cirza ke faɗa, ya fito taro,
Gwanki da Kada da Dorina sun ɗau horo,
          Sun ruga babu sallama ba su iyawa,

34.             Tsuntsun da ya ja ruwa, ruwa za su kashe shi,
Don iska, walƙiya da tsawa ka tare shi,
Saukan manyan ruwa su ɓata dabararshi,
Iccen da ya shekaro sani zai mancewa.

35.             Mun yarda haniniya Dawaki ke yin ta,
Bobbowa Raƙumi kaɗai yai gadon ta,
Hargowa na ga auraki ba ƙyafƙyafta,
          Ka ji caransu sai gari zai wayewa.

36.             Ban taɓa kwana da ƙin mutum a cikin rai ba,
Ni dai bisa nau sani, idan ban manta ba,
Ban taɓa cutar mutum saboda ƙiyayya ba,
          Ba wata matsala da Zil Ulaa  bai kwancewa.

37.             Wanda ya miƙa wa Jalla kai ya zama Shago,
Ba ya zama tunkiya a ja shi awa rago,
Don mun ƙi aron halin kare sheƙo, rugo!
          Za a haƙa min shigo-shigo ba zurmewa?

38.             Ba mai zance da ku ya kau ba ku sauya ba,
Ba alƙawalin da anka yo ba ku saɓa ba,
Babu amanar da nis sani ba ku cinye ba,
          Duk mai yin tin-da-tin da ku bai morewa.

39.             Sata da kwaɗai da raraka wayon zamba,
Son kai, son maguɗi, a ce ba mu gane ba,
Кarya ga tsegumi da tsince su yi kwamba,
          An ce a kula ya zan jidali na ƙurewa!

40.             To daɗa sai an jima Buwaye maci baƙi,
Katakoron Kare-ɓuki mai ɗan baki,
Je sannu katoɓara, gidoga a ci tsaki,
          Rana ta ɓaci gaskiya za ta fitowa.

41.             Tammat nai godiya ga Allah Makaɗaici,
Sarkin da Ya fid da mu ga hali matsananci,
Yai muna baiwa da gaskiya dole kwatanci,
          Duk ga maƙiyanta nan suna warwatsewa.

42.             Sunana Sha’iri Alu yaron Bunza,
Babban birni da ke gabas ƙauyen Geza,
Geza birnin kwalamshe mai suyan kaza,
          Yanzu ina Jami’ar Gusau bisa koyarwa.

No comments:

Post a Comment