Wednesday, January 2, 2019

Bugun Gaba (Salon A San Ni, A Ji Ni, A Gane Ni Ne Wane)Maƙasudin wannan xan bincike shi ne, yi wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe. An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An sarrafa karin magana (3), xiyan waƙar baka goma sha uku (13), rubutattun waƙoƙi huxu (4) domin a daddagi bagiren sosai a xebe kokanto...

Bugun Gaba
(Salon A San Ni, A Ji Ni, A Gane Ni Ne Wane)

Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato.
mabunza@yahoo.com Phone: 0803 431 6508

TSAKURE
Maƙasudin wannan xan bincike shi ne, yi wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe. An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An sarrafa karin magana (3), xiyan waƙar baka goma sha uku (13), rubutattun waƙoƙi huxu (4) domin a daddagi bagiren sosai a xebe kokanto. Sakamakon nazari ya tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba, don haka aka tanada masa turaku bakwai (7) na fexe shi da tsettsefe shi. A ƙarshe, aka shawarci masana da manazarta da xalibai da a saka shi cikin tsarin salailan da ake nazarin salailan adabi da su da cikakken sunansa na “Bugun Gaba” (BG).

GABATARWA
Zaman marina da masana da manazarta ke yi wa sha’anin ilimi wani babban cikas ne ga ci gabansa. Hausawa na cewa, hannu xaya ba ya xaukar jinka. A fagen karatu dole a samu kowa da irin wurin da yake sha’awa. Za a samu kowa da wurin da ya fi ƙwarewa. Masana, kowa da wurin da ya yi fice, ya yi zara, ya furce tsara. Tattare da haka, da za a sami ‘yar tazara a ziyarci fagen juna ba ƙaramar nasara za a ci ba wajen ciyar da ilimi gaba. A nazarin Hausa, fannoni uku, Al’ada, da Adabi, da Harshe, maƙwabta ne na ƙud-da-ƙud idan za a fahince su. Da masanan sun yi tsayin daka, sun yi wa nazarin Hausa taron dangi, da yanzu an wuce yadda ake a yau (2011). ‘Yar gudummuwar da nake so in bayar a nan ita ce, in yi amfani da fagen xalibta ta “Al’ada” in ƙyallaro fannin “Adabi” waƙa, in yi amfani da dabarun “Harshe” domin fito da wata gudummuwar da nake so in amfani fagen nazarinmu da shi. A kan wannan tunani na yi wa wannan takarda take: “Salon Bugun Gaba”.

WAIWAYE
Ina sane da cewa, masana da manazarta Hausa jiya da yau sun yi abin a zo a gani a kan tsettefe salo da yadda ake sarrafa shi a waƙoƙin baka da rubutattu da rubuce-rubuce da zube da wasan kwaikwayo. Jagoran kallo salo cikin rubutattun waƙoƙi (Muhammad, 1977) ya yi garkuwa da waƙoƙin Aƙilu Aliyu. Wanda ya fara dubansu a babban digirin waƙoƙin baka, (Gusau, 1986) ga waƙoƙi fada ya yi turke. Haƙiƙa (Birniwa, 1986) ya dube su a waƙoƙin siyasa. Bayero, (1986), ya hange su a Jigon Madahu. Bello Sa’idu, (1978), ya ruwaito su a waƙoƙin ƙarni na 19 da na 20. Birnin Tudu, (2002) ya nazarce su a Jigon Furu’a. Bello Bala, (2008) Mairukubta, (2010) da Maiyama, (2008) sun kalle su a waƙoƙin xaixaikun mawaƙa. Ayyukkan da suka fitar da salo a matsayin babban fagen daga su ne, Xangambo, (1980) da xalibinsa Mukhtar, (1987), a taƙaice, haka salo ya ci gaba da yaxuwa cikin rubuce-rubucen Al’ada da Adabi da Harshe na nazarce-nazarcen Hausa. Alhaƙiƙa, wannan yunƙuri ya cancanci a yabe shi sosai.

To! Da yake masana salo sun ce zavi ne na mai rubutu (ko mai magana ko mai aikata wani aiki) (Mukhtar, 1988), don haka ba ya da lokacin da za a ce, an kammala bincike a kansa. Haka kuma, ba ya da lokacin da za a daina yi masa salo ta fuskar ƙirƙire-ƙirƙiren sunaye ta hanyoyin da za a nazaarce shi. A ganina, ayyukkan da magabata suka gabatas, su ne xalibansu suka faxaxa, xaliban xalibansu suka ci gaba da laguda ana sarrafa hanyoyi irin na muryoyin xaliban Malam Zurƙe (Imam, 1966). Ban ga laifin haka ba idan an yi shi da manufar ƙara jaddada karatu da raya shi. Duk da haka, ai waƙa xaya ba ta gama niƙa irin na babban gida mai babban cefane (wato fagen nazarin Hausa). Matuƙar an yarda babban kifi na mai babban gora ne, to lalle kuwa babban kaya suna buƙatar babban gwammo. Ina ganin lokaci ya yi na a fara tunanin faxaxa wasu hasashe-hasashen nazari a ƙara musu tsawo, waxanda ba su da ƙafafun a yi musu, waxanda ƙafafunsa ba su tsayu ba a tsayar da su, waxanda aka tsayar da ƙafafunsu, a yi musu turke na mannanu in ji ƙuda da ya faxa ƙwaryar alewa.

HUJJAR BITAR NAZARI
Rubuce-rubucen magabatanmu na salo sun yi wa salo adalci, sun kuma rage ƙofar da xalibai za su iya su leƙa su tsinto wani abu ko wasu abubuwa. Sun yi nazarin ƙwaƙƙwafi a kan kamance da siffantawa da jinsantarwa da kambamawa da kirari da zuga da waskiya da adon harshe  da azanci da dai makamantasu. Abin ban sha’awa, kowane xalibi ya tashi nazarin Adabi ko Al’ada ko Harshe cikinsu yake sassaka ya kai ya komo da ‘yan dubarunsa. Cikas da na hanga ita ce, ban ga muna yawaita ƙoƙari na faxaxa waxannan makamam salon na magabata ba, balle mu ƙirƙiro wasu daga cikinsu ko mu ƙirƙiro sababbi da za su ƙara musu tsawo. Babban muradin malami ya ga xalibi ya fahince shi. Yadda zai tabbatar da ya fahinci malam shi ne, ya yi bitar karatunsa daidai ya ƙara kansa gaba bisa ga tafarkin da malam ya koyar da shi. Idan aka kula sosai, yawaitar mawaƙan baka da marubuta, da yawaitar littafain zube da na wasan kwaikwayo, da jaridu da mujallu da kafafen yaxa labarai da ake amfani da Hausa a yau abin lura ne. A auna tsawon gonan bana da igiyar bara da wuya a yi canjaras da abinda aka samu bara domin jiya ba yau ba.

BUGUN GABA
Ban ce ba a yi wani abu da ya yi kama da wannan ƙudurina ba. Na san an yi ayyuka da dama a kan kirari wanda a ƙarƙashinsa ake amfani da kalmomi irin washi, koxa kai, kambamawar zulaƙe da dai sauransu. Kirari kandamemen fage ne, idan aka dubi Kafin Hausa, da Mode, da Bunza, da dai makamantansu.
Ga tsarin kirari
a.      Mutum na iya wa kansa kirari
b.     Wani na iya yi masa kirari
c.      Ana yi wa wani abu/wasu abubuwa kirari

Idan aka zaburar da mutum ga abin da ya saba yi, ko ya shahara, ko ya buwaya, ko ya ƙware, idan kalmomin sun shiga jikinsa, sun tsima shi, su ne kirari. Idan ya furta wasu kalmomi domin tabbatar da abinda ake gaya masa, su ma kirari ne. Idan  ma wani dabba ko icce ko gari ko ƙasa ake yi wa wannan washin duk da yake ba sa ji, ba su mayar da martani, duk dai kirari ake yi musu. Ma’anonin kirari da masana da dama suka bayar za su hau wannan da’awar ta kiriri.
A tsarin Al’ada, “Bugun Gaba” mutum shi zai yi wa kansa. Mutum kaxai ke bugun gaba baya ga shi babu wani. Mutum shi zai yi bugun gaba da kansa, idan wani ya yi masa ya zama kirari. Ga irin tsarin al’adar Bahaushe ƙunshiyar “Bugun Gaba” za a ga:
a.      Za a yi bugun gaba da tushe (iyaye da kakanni)
b.     Za a yi bugun gaba da asali na ƙabila
c.      Za a yi bugun gaba da buwaya na magani/ tsafi
d.     Za a yi bugun gaba da fasaha ko basira ko hazaƙa
e.      Za a yi bugun gaba da ƙarfin jiki ko lafiyarsa
f.       Za a yi bugun gaba da duk wani abu da ake jin an rinjayi abokin magana ko jayayya
g.     Ba a bugun gaba da duk wani abu da al’ada ta tozartas sai fa a fagen shaguve

Asalin bugun gaba a al’da shi ne, mutum ya doki ƙirjinsa da tafin hannunsa na dama ya furta magana ga mai son rena shi ko rena masa wayo ko asali. Idan ya doki ƙirjinsa da hannun dama ya ce:
“Ni jikan Xanfodiyo za a gwada wa karatu? Littafi ya sha ƙarya da masu kuri da shiya!

“Ni Balaraben Makka, Buzu ke yi wa dubin hadarin kaji! Sai dai a fi mu ƙaton naxin hawa Geloba.”

Ire-iren waxannan ne Bahaushe ke cewa ‘bugun gaba’, da mutum ya furta su za a ce, “Ka ji bugun gaba”. Idan Bahaushe, ya doki gabansa da hannun hagu, galibi abinda ya gani, ko ya ji, ko ya karanta, ya ba shi mamaki ne, ko bai yarda da shi ba.
Ga al’ada, idan mutum ya samu karvuwa ga wani abu kamar ya samu shiga a hukuma ko wani shugaba ko fice a sana’a, idan ana furta wannan baiwar gaban idonsa zai xauki sigar kirari. Idan shi da kansa ke faxarsu ba da wata shigar washi ba ko alfahari ba ya zama “mamakar da kai”. Idan kuwa ya ji ana faxarsu ya sharve maganar, ya tabbatar da su, ya yi bugun gaba. Narambaxa ya fito da shi a sarari a waƙar, “Ya ci maza” yana cewa:
        Jagora: In ka ga mutum
                   Na ‘yan noƙe-noƙe
        Yara:            Sarki bai dara mai ba,
                   Ran da yad dara mai
                   Sai bugun gaba
        Gindi:           Ya ci maza ya kwan shina shire
                   Gamda’aren Sarkin Tudu Ali.

Idan Bafade bai samu shiga ga sarki ba yake kashe jiki. Da ya samu shiga sosai, ana yi da shi, maganganun da yake faxa na nuna da su ake yi, da doron da yake yi da sarki, su ne bugun gaba in ji malamin kixi na Sarkin Gobir (Narambaxa). Da fatar an fahinci wannan kalmar daxaxxiya ce cikin harshen Bahaushe da al’adunsa.

BUGUN GABA A MUDUN ADABI
Idan muka dubi bugun gaba da idon basira za mu fahinci babu sassa na Adabin Bahaushe da babu ratsinsa ciki. Ga wasu misalai kaxan cikin Karin Magana da suka shahara a bakin Bahaushe.
                                           i.            Muna wasa ne? Bagware ya ba da magani an sha an mutu ya ce, “A gama kuka a ba mu kuxinmu”.
                                         ii.            Annabijo dai! An ce wa takaren Xanfulani Alhaji.
                                      iii.            Gwamma ke san Allah? Ta ce, “Ga gidan ga gidan”.

Bagware da ya ba da magani aka sha aka mutu bai san laifi ya yi wa Bahaushe ba. A wautarsa, wai maganinsa katta’u ne don haka yake bugun gaba da cewa, “Muna wasa ne”? Da wani ya furta wannan zance a kansa da kirari ya yi masa, amma da yake shi ya furta da kansa sai ya zama bugun gaba. A zaton Xanfulani wanda ya je Makka sau xaya ko biyu shi ne Alhaji. Idan an je sau barkatai dole likafa ta ci gaba daga Alhaji zuwa “Annabi”. Don haka, da aka ce masa Alhaji, ko dai bai doki ƙirjinsa da tafin hannunsa na dama ba, faxarsa ta cewa, “Annabijo dai Moddibo” bugun gaba ne. Da maroƙi ya kira shi da sunan “Annabijo”, kirari ya yi masa. Gwamma Bagwara ce, ta yi gida kusan masallaci. Ana cikin zance da ita aka tambaye ta imaninta da faxar, “Ke san Allah”? Ita kuwa tana bugun gaban maƙwabciyar masallaci ce, sai ta ce, “Ga gidan ga gidan”? Wai ga gidanta ga xakin Allah, wa ya fi ta sanin maƙwabcinta? Gwamma bugun gaba take, a nan, babu batun  savo a wurinta.
Idan muka leƙa cikin labarun gargajiya da barkwanci, ba a rasa abubuwan tsinta ba a ciki. An ce, wata rana kuturu da makaho suna taxi bayan an dawo da yawon bara. Kuturu na yi wa makaho gori da cewa, su kaxai Allah Ya ambata a littafinSa a wurin da Ya ce, “Wal fuƙara’u wal masakina”. Kuturu ya ce, duk malamin da ke duniyar nan, ya san da kutare ake zance ba kowa ba. Makaho ya yi dariya domin a ganinsa ya fi kuturu hujja mai ƙarfi. Don haka da bugun gaba ya ba da bayani, ya ce: “Mu dai da Ya ce, “Walaƙad mannannaa alaihim”, za a yi wa kuri? Da an kula sosai amsar da makaho ya bayar ta bugun gaba ce, domin nassi ya fito ƙuru-ƙuru da faxar an manne musu idanunsu. Shi kuturu ina aka nuna an ƙiƙƙille yatsunsu?
Na so mu ziyarci littafin Ruwan Bagaja wurin da aka haxa Imam da Malam Zurƙe ƙure (maƙabala) da sarki ya so ya ji ra’ayi Imam a kan haxuwar sad a Malam Zurƙe ga yadda Imam ya mayar da gami:
“Ina tuna jahilan yaran almajirai ne masu ja da manya. Lalle dai ƙaramin sani ƙuƙumi ne.” (Imam, 1966:8)

BUGUN GABA A WƘOƘIN BAKA
A nazarin waƙa salo ya fi shahara da jan hankali. Da wuya a nazarci waƙa a manta da salonta abin ya yi armashi. Na fi ganin laifin xaliban nazarin waƙa da ke kallon jiya a yau  ba da idon ƙara wa jiya tsawo ba, ko a kakkave mata ƙura . A fannin waƙa, sukan sarrafa ‘Bugun Gaba” gwargawon iyawarsu.

MAKAXAN FADA
Makaxan fada sun yi fice ƙasar Hausa sosai domin sarakunan ƙasar Hausa suke yi wa waƙa. A tsari siyasar zama gari, ko ƙasa, ko wata gunduma, sarki ne na farko. Wanda duk ke cikin ƙasarsa talakansa ne. Xaya daga cikin makaxan fadar Isa, Makaxa Ibrahim Narambaxa na cewa:
        Jagora: Kak ku gama ni da yaro
        Yara:            Kun san yaro bai yi fasashata ba
        Jgora:           kak ku gama ni da yaro
        Yara:            kun san yaro bai yi zalaƙata ba
        Jagora: Kak kugama ni da yaro
        Yara:            kun san yaro bai yi kamab babba ba
        Jagora: Ƙaryar banza, ƙaryar wofi
                   Wane yaro inda Narambaxa
        Yara:            Mai tabarukun Sarki
        Gindi: Gogarman Tudu Jikan Sanda
                   Maza su ji tsoron xan Maihausa.

Narambaxa na bugun gaba da fasaharsa da basirarsa da daxewa cikin fagen waƙa tare da samun yardar sarki. Waxannan abubuwa da su Narambaxa ke bugun gaba, kuma da yake shi ke wasa kansa da kansa ya zama salon “Bugun Gaba”. Ta fuskar buwaya a fagen waƙa yana cewa:
        Jagora: Zamfara ba Makaxin da ka ja mini
        Yara:            Baya ga Xandawo sai ko Jankixi
                   :Sai Xandodo Alu mai Taushi
                   :Amma ba makaxin gayya ba.
        Gindi:           Gogarman Tudu jikan Sanda
                   Maza su ji tsoron xan Maihausa.

A bayyane za a ga kamar kirari makaxa ke yi wa kansa. A faifan nazari za a ga bugun gaba ne yake yi da zara takwarorinsa mawaƙa da ya yi a ƙasar Zamfara.

MAKAXAN MAZA
A tsarin rukuninsu makaxan noma da dambe da kokuwa da tauri da banga da mafarauta da masunta da maƙera duk suna shiga ciki. Ga abin da Makaxa Xan’anace ke faxa a waƙar Nadelu:
        Jagora:          ‘Yan makaxa ku na nan Arewa,
                   :Masu leƙa xan abin kixi
                   :‘Yan waƙoƙi ƙire-ƙire
                   :Makixa ku dai ka hassadanmu
                   :To mu dai ba mu hassadakku
                   :Hwaxa musu ko sun yi hassadanmu
:Ga banza an nan
:Makixa sai dai ku dangana
:Wani mai roƙo ba a …
:Ba a sake mai da kama ta Hausa
Gnidi:          Kai maza suka shakku ko can
:Kiro Nadelu kutunkun vauna

Alhaji Bawa Xan’anace yana bugun gaban cewa, idan yana nan da ransa, ko ya mutu, ba za a yi wani maroƙi irinsa ba a ƙasar Hausa. Da shi ake yi wa kixa, ya furta haka, abin zai tabbata kirari. Furta abin da bakinsa, kuma shi ne uban kixa, shi ya tabbatar da abin zaman ‘Bugun Gaba’. Wani takwaransa Yaro Hore Makaxin noma cewa yake yi:
Jagora:        Xan nan ha’ Ƙudus
          :Ha’ Kano Yaro Mani
Yara:           Ba a yi uban kixi
:Wanda yad doke min ba
:Sai dai yaro an fi mu…
:Gangunmman hira
Gindi:          Kama hakalinka kullum
:Ka sa gamba lauxi
:Za ni wurinka
:Xangarba gunguman noma

MAKAXAN JAMA’A
Masana sun saka duk wani mawaƙi da ya shahara wajen yi wa jama’a waƙa ba tare da rarrabe wani fanni da zai rinjayar da waƙoƙinsa ba cikin wannan rukuni. Wasu na hangen gefen da waƙoƙin suka fi yawa. Wasu na ganin gefen da ya fi shahara a fagen waƙa. Ga misali daga waƙar Halohalo ta Alhaji muhammadu Shata Katsina.:
Jagora:        Ba a samo canji na ba
:Belle in huta
:Belle in ce in sarara
:Yardar Allah ta fi ta kowa
:Na’abu xan Ibrahim
:Shata ne…
Gindi:          Halohalo mai ganga ya gode
:Yaran mai ganga sun gode

Alhaji Shata ya yarda da faxar wasu masu sha’awar waƙoƙin baka ke yi na cewa, shi ne shugaban ƙasan mawaƙa Hausa. Ban ce, ba shi ba ne amma nuna ya yarda da maganar, har yana bugun gaba da cewa, ba a samo “Canjinsa ba” balle ya aje waƙa ya zauna ya huta, ya sarara. Hangen da yake yi na wannan xaukaka har ya furta ta a waƙe da kansa ta bakinsa ba ta bakin yaransa ba shi ya mai da furucin “Salon Bugun Gaba”.

MAKAXAN SHA’AWA
Makaxan sha’awa galibi abinda ya burge su ko ya burge jama’a shi suka fi yi wa waƙa. Rukuninsu babba ne a cikin rukunan mawaƙan baka. Ga xan abin da Mamman Gawo Filinge ke faxa, a waƙarsa ta, “Ya Allah Gyara…”
        Jagora: Ku sauran ‘yan matan Gawo
                   :‘Yan ƙanana ne ba manya ba
                   :Ko nonon ba su fara ba
        Yara:            Manyan ba su fi mu fasaha ba
                   :In don kalamin waƙa ne
                   :Da Larabawa za a kara mu
                   :Mu da Bature sai Hindu
                   :Amma fa ba Tukuru ba
                   :A yee borki …
                   … … …
        Yara:            Mu mun iya ba mu koya ba
        Jagora: Haka nan na
        Gindi:           Ya Allah gyara
                   :Wahabu ka taimaki ‘yan Nijar

FANXARARRUN MAKAXA
Mawaƙan da ke yi wa abubuwan da al’adunmu nagartattun suka zarge su nake yi wa suna da “Fanxararrun Mawaƙa”. Cikin wannan rukunin kixin sata da kixin caca da kixin kwartanci da karuwanci da dai ire-iren su. Ga abin da Alhaji Gambo Fagada ke faxa:
        Jagora: Kway yi kixan sata ƙasag ga
:Bai yi wa Gambo mai kixa ba
:Ko an cira ni kixan manyan kalangai
:Ba ka sanin sunan varayi
:Kamaw wada Gambo ke faxin su.

        A wata rerawa yana cewa:
        Jagora: Don koway yi kixin sata irina,
                   :Ko ka yi kalangai ka cira ni,
                   :Ba ka sanin sata irina,
                   :Don ba ka hwaxin sunan varayi.
                   :Kamar wada Gambo ke hwaxinsu.

        Tabbas! Babu mai musun cewa, Gambo ya san sata, ya san varayi matacci da na raye da na xaure. Faxar haka da kansa bai bari a faxa ba, kuma a fagen waƙa, shi kaxai ya tabbatar da virvishin “Bugun Gaba”. Da ya ga ana son a rena imaninsa saboda irin kixan da yake yi, sai ya ce:
        Jagora: Hwaman ya’amal mis ƙaala zarra
                   :Wanda yas san Ƙur’ani irina
:Duniyag ga uban wa za shi tsoro

Ga al’ada, mai yi ba ya faxa, balle a fagen karatu da ake son ƙanƙan da kai. Faxarsa ta nuna cikakken masani Alƙur’ani ne, bugun gaba ne ƙarara a bayyane.

MAKAXAN TASHE
Binciken tarihin rayuwar wasu makaxan baka na ƙasar Hausa ya nuna waxanda ba ‘yan gado ba, da yawa, daga waƙoƙin tashe suka fara. Ga wani zance na mawaƙin tashe na Tungar Bella da Taƙaji, suna cewa:
        Jagora: Sai dai a hi mu
                   :Kalangu da kurkutu
Yara:           Amma ba a fin mu
:Daxin baki
Gindi:          Yau da borin Goje
:Kana da borin tashe

MAKAXAN GIRSHI
Zamani ya kawo mu yau da mutum ya yi tsintuwar fasaha sai ya zama mawaƙin girshi. Wani lokaci a ji waƙoƙin abin yabo gwanin ban sha’awa, wani lokaci ga su nan dai. Da yawa daga cikinsu xan lokaci kaxan suke su gama yayinsu a manta da su. Ga wani xa daga xiyan waƙar Ganxo Ambursa, cikin waƙar “Ba a gane manya…”
        Jagora: Musa uban kixi
:Ni ban san ka da shakka ba
: Na san wurin kixi
:Kai kan ka wuce ‘yan yara
:Ni ko wurin xumi ka san
:Na wuce ‘yan yara
:Ko manya-manya sai in sun
:Yarda mu sasanta
Gindi:          Ba a gane manya
                   :Sai ci ya samu

        Yaba wa Musa wajen kixa, kirari ne aka yi wa Musa. A vangare xaya kuma, faxar ya zarce yara wajen “xumi” (magana) da cewa ko manya sai dai a sasanta Salon “Bugun Gaba” ne.

JIRWAYIN BUGUN GABA A RUBUTATTUN WAƘOƘI
Ana yi wa waƙoƙin baka suna da waƙoƙin hululuwa domin kutsawar su ga al’amurran da addini ya yi hani. Rubutattun waƙoƙin su ne, waƙoƙin masana addini da almajirai da masoya makaranta. Yanzu, zamani ya kutsa cikinsu sosai, yadda duk ake samun salon “Bugun Gaba” cikin waƙoƙin baka, haka ake samu a cikinsu. Ga xan misali a kwatanta:

WAZIRIN GWANDU ALHAJI UMARU
An yi kundin digirin BA da PhD a kansa Ikara, (1982) da Usman, (2008). Cikin waƙar Yabon Sarkin Gwandu Yahaya, ya ce:
Na saba miƙa shexara
Ta tsaya tsaf babu tanƙwara
Ai waƙa ba ta gagara
Muddin na tashi fassara
Wada duk nika so ina hwaxi rarara
                   (Sa maza gudu)
Idan malami ya kai ga furta fagen da ya buwaya da bakinsa da iƙirarin cewa, ya wuce kure a ciki abin ya zama ‘bugun gaba’.

AƘILU ALIYU
An yi rubuce-rubuce da yawa a kan waƙoƙinsa, fitaccen aikin da aka yi a kan waƙoƙinsa shi ne, Muhammad, (1977) kundin PhD. A wata waƙarsa ta “Noma tushen arziki” yana cewa:
Na dai shiga takarar waƙe
Kaina tsaye zuciya miƙe
Ba jirge na zo ba ko duƙe
Tsini ba ya zama feƙe
Ba zan zama wai ga waƙa ba.
       
Wannan xangon dukkaninsa bugun gaba ne xango na ƙarshe ya fito ƙuru-ƙuru ga mai marare.


SAMBO WALI
An yi rubuce-rubuce da yawa a kan waƙoƙinsa. An rubuta kundayen digirin BA kusan 3 – 4 akansa. Shahararren aikin da aka yi a kansa shi ne, Bunza, (2002). A waƙarsa ta “Zaman Banza” yana cewa:
Idan an tabbai ka xan’uwa wat tsara ta
Wali Sambo ka tsara wagga muddin waƙa ta
Gixaxawa za ka je ki can na shiyata
Dawaman roƙon mukai Gwani don ya tsare mu

GARBA GWANDU
An yi aikin digirin BA a kansa, Balarabe (1980), an yi nazarce-nazarce da yawa a kan xaixaikun waƙoƙinsa. A waƙarsa ta “’Yan makaranta” yana cewa:
G. G. na Maikudu sha’iri ƙi fansa
Shi yay yi waƙar ‘yan sukul nan Hausa

SAKAMAKON NAZARI
Muradin shi ne a fahinci bambanci kirari da bugun gaba. Idan har kirari na da kasonsa mai tsoka cikin nazarin salailan adabi, ya kyautu a share wa Salon Bugun Gaba, fili mai faxi. A ganina, Salon Bugun Gaba, ya ratsa dukkan sassan Adabi da Al’ada da Harshe na Bahaushe. Da wuya a yi nazarin wata waƙa ta baka ko rubutacciya ba a ci karo da shi ba. Haka kuma, taskar karin magana da salon magana da shaguve da azanci da barkwanci da tatsuniya da labarum gargajiya duk ana samunsu a ciki. Rubuce-rubucen littattafanmu na ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo da finafinan Hausa yana ciki tsumbul ba tsintuwar dami a kala ba ne. tabbacin samuwarsa haka shi zai ba mu damar mu kalli kayan cikinsa kama haka:
                               i.            Tushe:         Iyaye da kakanni, d.s.
                             ii.            Asali:          Harshe da ƙabila, d.s.
                          iii.            Baiwa:         Fasaha da fahimta da sani, d.s.
                           iv.            Koyo:          Ƙwarewa da gogewa da iyawa, d.s.
                             v.            Togiya:       Hawa da nuna wuraren da aka fi wani
                           vi.            Suna:          Ficen suna da zarta tsara
                        vii.            Turke:         Za a yi turke ga abin nan da ake zance a kansa

Da wannan xan taƙaitaccen bayani zan ce, ya kyautu mu sanya ‘Salon Bugun Gaba’ xaya daga cikin salailan da ake tsettsefewa wajen nazarce-nazarcenmu. Gadon fixa da na zana bakwai, na zana su bisa ga xan binciken da na yi, da fatar za a taya ni gyare-gyare da ƙare-ƙare da rage-rage mu daidaitu mu ciyar da harshenmu gaba.

NAXEWA
Hausawa na cewa, zama wuri xaya tsotsayi in ji ƙuda. Na yarda da faxarsu ta cewa, da koyo akan iya. Yana da kyau masana da manazarta da mu xalibansu mu yi riƙo ga karin maganan da ke cewa, da rashin tayi akan bar arha. Haƙiƙa in dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Don haka, muna da jan aiki a gabanmu na zage dantse mu ga muna bitar ayyukan magabata, da niyyar ƙara kyautata su da inganta su domin su kasance wandon roba daidai da kwankwason kowane irin zamani. Na tava gabatar da wani salo kimanin shekara biyu da suka gabata, mai suna “Ingiza Maikantu Ruwa”. Na gabatar da shi a Jami’ar Umaru Musa ‘Yaraduwa, Katsina. Na kuma aika da binciken ga masana fannin waƙa fitattu domin su taya ni gyare-gyare, kuma an wallafa ta a mujallarsu ta HIMMA. Da fatar wannan ta shiga sahun waccan bayan na karvi gudunmuwarku. A taƙaice Salon Bugun Gaba shi ne:
“Furucin da wani mutum zai yi a cikin zancensa ko waƙarsa ko rubutunsa yana ƙoƙarin fito da irin martabarsa ko ƙwazonsa. Galibi idan fagen fasaha ne, mai bugun gaba zai yi bugun gaban da fasaharsa ne da ya yi fice da ita. Idan fagen awon mutunci ne da sauran sassan da gidajen shida za a yi iƙirari.”

MANAZARTA
Alƙali, A. (1989) “Cuxexeniyar Adabi: Tasirin Adabin Baka A Kan Rubutattun Waƙoƙin Hausa Dangane da Habaici da Zambo da Kirari da Karin Magana”, kundin digirin MA, Kano, Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (1994) Yaƙi da Rashin Tarbiya Cin Hanci da Karvar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace, IBRASH Lagos
Bunza, A. M. (2009) Narambaxa, IBRASH Lagos
Bunza, A. M. (2011) “Sakkwato ce Tushen Hausa In Ji Narambaxa”, Muƙala, Jami’ar Umar Musa, Katsina.
Birnin-Tudu, S. Y. (2002) “Jigo da Salon Rubutattun Waƙoƙin Furu’a na Ƙarni na Ashirin”, kundin digirin PhD, Sakkwato, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Birniwa, H. A. (1987) “Conservatism and Dissent: A comparative study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa 1946 – 1983”, unpublished PhD thesis, University of Sokoto.
Xangambo, A. (1980) “Hausa Wa’azi Verse from Circa 1800 – 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style”, PhD thesis, University of London.
Xangambo, A. (2007) Xaurayar Gadon Fexe Waƙa. Kaduna: Amana Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa Yanaye-yanayensu da Sigoginsu, Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zavavvun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Century Reseach and Publishing Limited, Kano – Nigeria.
Hiskett, M. (1975) A History of Hausa Islamic Verse, SOAS, London University.
Ikara, A. T. (1982) “Umaru Wazirin Gwandu da Waƙoƙinsa”, kundin digirin BA, Zaria, Jami’ar Ahmadu Bello.
Imam, A. (1966) Ruwan Bagaja, NNPC, Zaria
Muhammad, D. (1977) “Individual Talent in the Hausa Poetic Tradition a Study of Aƙilu Aliyu and His Art” PhD thesis, SOAS London, University.
Omar, S. (1983) “Style and Theme in the Poems of Mu’azu Haxejiya” MA, thesis, SOAS London University.
Sa’id, B. (1978) “Gudummuwar Masu Jihadi kan Adabin Hausa”, kundin digirin MA, Kano, Jami’ar Bayero.
Sa’id, B. (2002) “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin, A Sakkwato a Kebbi da Zamfara”, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Usman, B. B. (2008) “Hikimar Magabata” kundin digirin PhD, Sakkwato, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Yahya, A. B. (1987) “The Verse Category of Madahu with Special Reference to Theme, Style and Background of Islamic Sources and Belief”. PhD thesis, University of Sokoto.
Yahya, A. B. (2001) Salo Asirin Waƙa, FISBAS Media Services, Kaduna.

No comments:

Post a Comment