Thursday, January 10, 2019

Don Me Ake Karatun Hausa?

January 10, 2019 0Bisa ga al’adar ɗaliban harshen, ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe tarkakken nazarin da ɗalibi zai ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi in yi bara da Hausa.[1] Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[2] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu da neman shahara a ciki. A ganina, gajeren tunanin ‘yan bayan fage ga duniyar ilmi a koyaushe yana nuna musu, wace fa’ida ke cikin karatun harshenka na gado da ka tashi ciki, ka balaga ciki, kuma kana rayuwa a ciki?[3] Masu irin wannan fahintar…

Kuka A Faifan Nazari: Laluben Diddigin Bahaushen Kuka Da Ƙunshiyar Lafazinsa

January 10, 2019 0

A iya sanina, wannan ɗan bincike sabo ne, saboda rashin samun wani da ya gabace shi a fagen nazarin Hausa. Duk da haka, abin da aka gina bincike a kansa “kuka” ya girmi duk wani mai bincike da zai yi bincike a kansa. Tunanin kowane mai tunani, ba zai fice da’irar al’adarsa da adabinsa da aka gina cikin harshen da yake rayuwa da shi. Sanin haka ya sa na gayyato ƙwararrun mawaƙan Hausa (20) [14 na baka, 6 marubuta], na sarrafa ɗiyan waƙoƙinsu (34). Cikin wannan fafitikar, na yi garkuwa da karin magana (3), kirari (1), ƙagaggen labari (1), waƙoƙin dandali (3) domin daidaita akalar bincike. Bisa hasken waɗannan kayan aiki (62) aka ci nasarar gano…

Linguistic Spaces In Hausa Trado-Medical Antiquities: A Neglected Aspect In Hausa Anthropological Linguistics

January 10, 2019 1


 This paper is an attempt to peep at a forgotten and neglected aspect of Hausa linguistics in the name of Anthropological Linguistics. It is a study which sets out to provide an overview of the subject under review as suggested by the paper’s title: “Linguistic spaces in Hausa trado-medical antiquities”. The data are gathered from primary and secondary sources specifically during field work and several contacts with selected Hausa practitioners. The focus of the study include the relevance of language in the Hausa trado-medical heritage; the identification of the major historical landmarks of Hausa traditional medicine namely ancient and pre-colonial healing traditions. Likewise, this work traces the Linguistic spaces in the herbal and faith medicine (Bori and Tsibbu). These are then explored in three stages namely, the linguistic spaces in the medicinal sources; branches of Hausa medicine, and...

Hyperbole As The Peak Of Stylistic Adornment In Hausa Oral Songs

January 10, 2019 0

The study area of this paper is hyperbole in Hausa oral songs. In contemporary Hausa studies, it is named Kambamar Zulaƙe (exaggeration or overstatement). In the study of the style under review, it is discovered that the literal and technical meaning of hyperbole is far beyond exaggeration or overstatement. It is a popular style, deeply rooted in all the categories of Hausa oral songs. It traces in the most prominent styles in Hausa oral songs and its popularity in dispensing ideas and presenting facts in singing profession is a good point to be considered. The contextual meanings of hyperbole Hausa oral songs present it as evidently beyond mere exaggeration. In folkloric point of view, many of the said statements are well protected in worldview…

Wednesday, January 9, 2019

Bitar Karatun Hausa A Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙrn. 21): (Wurin Da Babu Ƙasa Ake Gardamar Kokuwa)

January 09, 2019 0


The paper is a historical review of Hausa studies in Nigerian academia. In the struggle, relevant related literatures were critically examined to justify the dare need of an updated progress report. In this study, an advanced Hausa study is the desired target to conjugate Hausa on the rating scale of Nigerian academic standard. Similarly, tertiary institutions, Universities and research centers handling Hausa academic Activities are the umbilical cord of the paper. To be more precise, the paper concentrates on the Nigerian factor in the subject under review. Gladly, it peeps through nineteen Nigerian Universities, thirty eight other tertiary institutions and four research centers to update the progress report of the journey so far. The review captures forty indigenous Nigerian Professors of Hausa studies, and forty…

From Zinder To Hausaland: (The Traces of Zinder Hausa-Muslim Scholars and Scholarship in Hausaland)

January 09, 2019 0

Migration is a universal culture across human history. The culture of migration is unavoidable in human history from time immemorial (evolution of mankind) to date. By definition, human migration is the movement by people from one place to another with the intention of settling, permanently or temporarily in a new location (Wikipedia). The said movement could be external, which is often over long distances or internal within a short range within the province, state or kingdom. Experts in the history of Hausaland observed that, one aspect of the internal history of Hausaland was large scale emigration from the area in the seventeenth century (Adamu, 1978:27). This paper is an attempt to study the religio-cultural impact of migration...

Wednesday, January 2, 2019

The Zarma Factor In The Kingdom Of Kanta

January 02, 2019 0


 Cultural relationship among African societies in sub-Saharan Africa is as old as the land itself. Brutal colonial policy on African cultures and traditions couple with wicked approach to the African ancient boundaries dealt a great blow to African history and development. Powerful kingdoms and chiefdoms were dismantled and dismembered into districts, regions and provinces. This resulted in a very sever cultural and linguistic endangerments in the affected kingdoms. Thus, historical origins and earlier intergroup relationship among African societies was logically distorted and the treasuries of its cultural values were led to rest. Zarma and the Kanta kingdom witnessed the aforementioned episode and struggled very hard to survive the inflicted injury...

Wane Ne 'Dan Ta’adda?sava

January 02, 2019 0

 Gajeren tunanin da ke ga ɗan Adam shi ya sa Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan, mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke wata nahiya mai riƙe da wani addini alhakin ringingimun da ke wakana a duniyar zamaninsu. Yau, babu, ɓata gari sai Musulmi. Babu ɗan ta’adda sai Musulmi. Bab...

Bugun Gaba (Salon A San Ni, A Ji Ni, A Gane Ni Ne Wane)

January 02, 2019 0


Maƙasudin wannan xan bincike shi ne, yi wa wasu salailan adabi sunan da ya dace da su domin ƙara faxaxa bincike da nazari. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da samuwar “Salon Bugun Gaba” cikin kowane sashe na adabin Bahaushe. An tsara aikin cikin manyan sassa tara (9), ƙananan sassa goma sha xaya (11). An ziyarci makaxan baka (8), marubuta waƙoƙi huxu (4), marubuci xaya (1) domin a tabbatar da samuwar Salon Bugun Gaba. An sarrafa karin magana (3), xiyan waƙar baka goma sha uku (13), rubutattun waƙoƙi huxu (4) domin a daddagi bagiren sosai a xebe kokanto...

Gurbin Sarkin Musulmi A Ganin Watan Azumi

January 02, 2019 0


Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin halittun da ba su ƙidayuwa ga wani bawa daga cikin bayinSa. Ya ƙago sammai ya ƙawata (ta duniyarmu) da hasken taurari domin amfaninmu. Ya ba mu rana da wata domin daidaita ibadojinmu gwargwadon savawarsu a duniyarmu. Burina a wannan ‘yar takarda shi ne, lalubo wasu matsalolin ganin watan Ramalana da irin gurbin da shari’armu ta yi wa Sarkin Musulmi na kowace ƙasa ta Musulmi a ciki. Wannan xan yunƙuri an yi shi da nufin cike wani givi daga cikin kusurwowin da Shaixan ke kutsowa ya yaudare mu ta fuskar haxin kanmu. Matsalolin da ke tattare da ganin wata a duniya…

Gudu A Bahaushen Tunani

January 02, 2019 0


Tunanin mutane da ke bayyana a adabinsu na baka, da rubutacce wata fitila ce, ta ƙyallaro al’adun rayuwarsu. Ƙudurina a wannan bincike shi ne, in yi garkuwa da sassan adabin bakan Bahaushe, domin in leƙo irin gurbin da al’adarsa ta yi wa “gudu”; yadda yake, da yadda yake kallonsa. A cikin wannan tunanin, na gayyato mawaƙan baka (12) na sassan rukunin mawaƙa (5). Na sarrafa xiyan waƙoƙinsu (24) domin tabbatar da hasashena. Na yi wa hujjojina turke da karuruwan magana (27), na yave su da kirari (2); na ƙawata ginar da ƙagaggun labarai (2) da wassannin yara (1). Da jimillar waxannan hujjoji (67) na yi wa sakamakon bincikena turaku (6) nagartattu. Binciken ya tabbatar da gurbin “gudu” a al’adar…

Mutuwa

January 02, 2019 0


Roƙo nika yi ga Wahidun mai gyarawa,
Sarkin da ya zarce masu ilmi ganewa,
Kai kay yi sama’u kay yi ƙassan zaunawa,
Kay yo Aljanna kai wuta mai ƙonarwa,
Kay yo duniya da rayuwa don zaunawa,
Kaƙ ƙaddaro lahira ga ƙarshen komawa,
Kowace rai la muhala ƙarshen ta macewa,
Tilas in ya mace ƙasa zai komawa,
Tsoron mutuwa ga masu rai bai ƙarewa,
Domin ba ta kure da ta zaka kamawa,
Ɓera bai ce wa mage sannu da hutawa,
In sun gamu hanya wa mutum sai rugawa,
Don me akuya ka ba da bai babu tsayawa?
In kura ta yi mui guda ba ta tsayawa.

Ta’aziyyar Mallam Ibrahim Awwal Albaani Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

January 02, 2019 0


1.       Shukura ga Allah guda masani halin kowa,
          Mai ƙaddarowa ta tabbata babu mai tsawa,
Ya mai hukuncin da ba makara da gaggawa,
Masanin da ilminSa ya wuce hankalin kowa,
          Subhaana lil laahi tsarki na ga Rabbani.

2.       Na yo salati ga Manzo shugaban bayi,
Ahalinsa dukkan sahabbai ƙoƙari sun yi,
Na riƙo ga sunna ta sadu da mu ruwan sanyi,
Mariƙa amana sahada kun riga kun yi,
          Matsayin shahidi ga nassi babu saɓani.

3.       Mai rai a ce ya mace ba al’ajab ne ba,
Mutuwar shahada buki ne ba na wasa ba,
Ita ce manunin aƙida ba ta yi ƙura ba,
Ita fassara ce mutum bai tabka shirme ba,
          Shaidarmu ke nan ga Awwalu namu Albaani.

Where Lies The Problem?

January 02, 2019 0The search for where lies the truth in the divine books revealed to mankind has been an everlasting discourse in religious studies. The debate had always yield a commendable result in terms of getting new converts, understanding our differences, developing awareness among the devotees, mutual understanding, and peaceful co-existence, which translate into tranquil atmosphere for the people of different faith. The more the debate, the more the understanding of the lapses, rifts, lacuna, controversies and contradictions (if any) in our faith. This intellectual write-up is meant for the consumption of learned authorities in the business, while the open-air and house-to-house preaching consolidate ordinary followers to the doctrine…
January 02, 2019 0


From the historical point of view, the enterprise of translation is as old as mankind, and from the perspective of religion, it dates back to the first prophet sent to mankind. In context of historical linguistics, it developed along with the evolution of human languages. Cultural critics view it as cultural development through contact by a variety of cultural groups in the struggle to meet unavoidable demands of socialization and acculturation among the contact groups. In fact, the scientific beginning of the art of translation and its earliest fathers are certainly under the cloud. However, the business of translation in this era is turning into a global issue and a serious academic affair in the international communities. Translation is now a necessity in our scientific world; it is the most powerful instrument in handling most sensitive issues of our security and diplomatic tie. It is the opinion of this paper that grammar and cultural barriers surrounding the message to be translated are always the problems in the transaction of the business. In this view, Hausa-English and English-Hausa translation trajectory would be the specimen to exemplify our opinion critically.

Tuesday, January 1, 2019

BA A WANE BAKIN BANZA (Gurbin Daular Gobir Da Gobirwa A Farfajiyar Sudaniyya)

January 01, 2019 0


Gobir tsohuwar Daula ce da ta shiga gwagwarmaya da daulolin duniyar Sudaniyya. Burin wannan bincike ƙyallaro wasu daga cikin dalilan da suka ɗaga Daular Gobir da Gobirawa sama ga sauran dauloli. An yi garkuwa da fitattun ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba tare da taimakon yawon rangadi da tattaunawa da dafa kafaɗar adabin baka da rubutacce. Binciken ya gano cewa, Daular Gobir cin gashin kanta take yi kuma Bahaushiyar Daula ce. Bugu da ƙari, ta ƙi ta aminta da tarihihin Bayajidda ya ratsa Daularta. Dabarun yaƙin Daular Gobir da siyasar sarautunta sun yi tasiri sosai ga daulolin Sudaniyya. Babu Daula daga cikin daulolin Sudan…

The Place Of Climate In Hausa Tradi-Medical Tradition

January 01, 2019 0


Human health and climate are very much related in the philosophy of Hausa healing tradition. Body temperature, circulatory and respiratory systems of body anatomy translate climatic conditions of the very environment we live in. In this respect, our tradi-medical heritage is scientifically and culturally controlled by the climatic condition of the region we found ourselves. The focus of this paper is to examine the relevance of climate change in sub-saharan Africa particularly in that northern part of Nigeria, known as the Hausaland, with reference to the ancient institution of traditional health care delivery. To be precise, the desired target is to read through the negative impacts of climate change to the medicinal plants and trees, special species and materia-medica with special reference to some climate sensitive…

The Death that Never was in Hausa Confrontational Songs (A study of four popular songs of four Hausa prominent Oral Singers)

January 01, 2019 0


Death, Faɗuwa or Fakuwa in classical Hausa, now mutuwa in modern Hausa, is the central issue of this discussion. “Death” is literally defined as cessation of physical life or extinction of anything. It is a total destruction and collapse of the general body system. It is therefore considered the terminal of the general activities of life. Scientifically, its remedy is yet to be discovered, and there is no identified cultural antidote to confront its scourge. In human culture, death remains an unavoidable battle and hence a serious debatable issue in literary revolution across the globe. In the field of research, it is everywhere and no where to be met physically or otherwise. The phobia of its unnoticed…

Laughter in a multilingual society

January 01, 2019 0Semantic is a major branch of Linguistics devoted to the study of meaning in language (Crystal, 1991:310). My intention, here is to look at laughter from Hausa cultural perspective with special reference to the semantic aspects of the subject. Meaning is so important as such, it occupies a significant position in human language, without it, it is difficult to comprehend verbal and non-verbal messages. In the affairs of grammar, literature and orature, it is meaning which leads the floor of discussion. Once meaning is distorted or not properly comprehended confusion may arise which could eventually provoke laughter among the discussants. My concern is with the meaning that provokes laughter in the intended message of the speaker, discussant, or a conveyor.