Thursday, December 27, 2018

Zaɓi Abokin Zama1.       Da sunan Ilaahu gwani karatu ya fara,
          Tsaya ɗan’uwana ga salati mu ƙara,
Buƙata mu samu tabarraki gun Tabara,
          Zaman duniyarmu da lahira mun biɗe shi.

2.       Karatunmu yau ga zaman abota ya raɓa,
Kiyaye zama bisa ƙa’ida kar a saɓa,
Da hulɗa da zance kar a kwaso a kwaɓa,
          A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.

3.       Abota zaman yarda da ƙauna aminci,
Ka cuɗanni in cuɗe ka ne ba butulci,
A baki da zuci a jittu shi ne zumunci,
          A koyaushe ɗaya ƙaunar yakai ɗaya ya gan shi.---------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
-------------------------------

1.       Da sunan Ilaahu gwani karatu ya fara,
          Tsaya ɗan’uwana ga salati mu ƙara,
Buƙata mu samu tabarraki gun Tabara,
          Zaman duniyarmu da lahira mun biɗe shi.

2.       Karatunmu yau ga zaman abota ya raɓa,
Kiyaye zama bisa ƙa’ida kar a saɓa,
Da hulɗa da zance kar a kwaso a kwaɓa,
          A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.

3.       Abota zaman yarda da ƙauna aminci,
Ka cuɗanni in cuɗe ka ne ba butulci,
A baki da zuci a jittu shi ne zumunci,
          A koyaushe ɗaya ƙaunar yakai ɗaya ya gan shi,

4.       Mutuncinku bakin gwargwado kun fake shi,
Ɗabi’u na juna gwargwado an sane shi,
Wuraren da an ka yi canjaras ba a fashi,
          Barafeshiya aka maƙura kar ta tashi.

5.       A kan kowace matsala a zan sa fahinta,
Idan zuciya ta zaburo kar a bi ta,
A sa hankalin natsuwa a kore fushinta,
          A bar bin halinta na son a yanka ta tashi.

6.       Abota ba za ta yi kyau ba in ba kusanta,
Tana wargajewa in ana sa husata,
Zama ba ya kyau in godiya ta ƙaranta,
     Zukata cikin gumuni gaba na ta nishi.

7.                 Abota ta na fi gabanka ta zan adawa,
Zaman ƙeta tarko ne mafarinsa rowa,
Zaman ɗari-ɗari aboki ya zan katawa,
     Zaman tsegumi da raɗa hasumi ka tashi.

8.                 Abokin aboki bai da babban muƙami,
Abokin rashin samun abokin kalami,
Yawaitan abokai don biɗan kai ga tsomi,
     Yana sa a gane halinka kowa ya ƙi shi.

9.                 Abotan biɗan a sani ka sa cin mutunci,
Abotan rashin ra’ayi ka kawo butulci,
Abotan maso wani ka ji raggon fatauci,
Kashe kanka za ka yi babu riba gare shi.

10.             Abota da manya tsegumi ke shigowa,
Abota da yara ga babba zargi ka zowa,
Abota da macce ka sa a hango kusurwa,
     Idan babu daudanci ƙazanta gare shi.

11.             Abokin buƙata lokaci ke gare shi,
Idan ta biya a ware a ture batunshi,
Idan ta ƙi jawo ruwa a nan za a ƙi shi,
     Abotan a so ka, a ƙi ka, ciwo gare shi.

12.             Abokin zaman ƙarya zaton za a samu,
Idan an ga ci sunansa Nasamu-namu,
Idan an ka tsinka wuya a ce: “wa ka kai mu?”
     Da an hangi zai zauna wuri sai a tashi.

13.             Abokin ƙabilanci bala’insa kissa,
Idan kar ta san kar, dole kowa ya ƙosa,
Maci goro bai riƙa gandi in ya ga marsa
     Zama kan ƙabilanci bala’i gare shi

14.             Abokan munafucci da tsince da giba,
Zaman zurmuguɗɗu da tsegumi bai da riba,
Zama juddadun a cikin zato yai musiba,
     Zaman an yi an ce, wa ka ƙaunar ya yi shi?

15.             Abokin da ke mazarin ya san tanadinka,
A koyaushe burinai ya rege cikinka,
Da duk za shi al’amarinsa bai son ganin ka,
Ka sa mai ido, ka bi taka hanya, ka bar shi.
16.             Abokin da harshenai yake zazzalowa,
Wajen ba da labarinka in ya ga sanwa,
Asirranka duk ya baza su gun ‘yan adawa,
     Ka kauce, Tabaraka zai yi ma maganin shi

17.             Abokin adawa ba ya ƙaunar a dace,
Ijabar da Jalla ya yo yake son ta noce,
Idan ya ga baiwa gun ka tamkar ya ƙwace,
     Hawaye kamar su zubo gaba na ta nishi.

18.             Aboki na tserereniya ba shi hanya,
Abin duk da kay yo, zan yi ya zan hamayya,
Ana tare an ƙi rufe takaici a ƙurya,
     Zaman so ya hurhura har ya koma na kishi.

19.             Zaman yaudara cutar abokin amana,
Ana zaune tare cikin gaba na ta kuna,
Da duk yag ga mai ra’ayin ka zai zo shi zauna
     Shi ɓata ka dama da hanni, wai don a so shi.

20.             Aboki ba zai ƙi zama da kai shawari ba,
Ba zai ƙulla al’amarinsa bamban da kai ba,
Ba zai so taɓin irlinka in ba ka nan ba,
     Da an so a muzantaka kai ka ba da bashi

21.             Aboki na gaske ba zai yi zargin mutum ba,
Ba zai yarda gun ka a zo da mugun zato ba,
Magabcinka bai ga wurin laɓawa garai ba
     Ina zai ganin sarari da fuska gare shi?

22.             Wurin kankajeli shirin abota ka ɓaci
Garin kakkaɓi motar abota ka faci
Katsal na zube wa zaman abota mutunci
     Kisisiniya na sa aboki a bar shi.

23.             Ka ce ba gawani a gare ka wa za ya so ka?
Rashin moriyarka na sa ana zulluminka,
A shaide ka ba ka da moriya ko ta tsoka?
     Abota da kai ƙarfin hali ɗai ka yo shi.

24.             Abota da Daɗin-kowa ɗai ad da ciwo,
Ya hau ɗan rabonka da ci kamar zai yi zawo,
Idan ya farauto nasa ya kama yawo.
     Shi ɓoye abinsa cikin akwatin gilashi.

25.             Abotar taho mu yi gardama kar ka yi ta,
Zaman tare ga a barambaram ba fahinta,
Ɗaƙoƙi su tashi kamar a miƙe a kwafta,
     Jiɓi na zuba kumfa ga baki na haushi,

26.             Abota da mai son kansa ɗai kar ka fara,
Bale zarumin rikici da dokin gadara,
Da wawa da shashasha ina mai dabara?
     Bale sakarai asheraru ƙarya gare shi.

27.             Da mai shishigi da yawan zaƙewa ga amri,\
Da mai faifeye abu dole sai ya ga sharri,
Da mai ba ka, in ka ɗaga ya far ma da gori,
     Da mai son a ce, ya fi ka kirki, ka bar shi.

28.             Butulci ka ɓata zama ka zan mai fahimta,\
Ana taimakonka kana ta ƙwazon ka cuta,
Tukuicinka cin zarafin abokin fahimta,
     Zaman ba ni in cuce ka ciwo gare shi,

29.             Tunanin da nay yi a da fahimtar aƙida,
Yana kankare gaba da mugun makida,
Wajen ‘yan abarba da masu lemo da gwadda,
     Maɗi bai kirari ga zuma na ganin shi.

30.             Ashe hadda mallamai abin ya shige su,
Abota kaman dai ta fi muni cikinsu,,
Faɗin na fi wane sani ka watse zamansu,
Karatun kirari babu lada gare shi.

31.             Ana mazhaba ɗaya ɗan shiri- sai shi ware,
Ɗarikunsu sun yi dubu wane za ka kare,?
Ga ‘yan ƙungiya da kwaɗai da son rai ya cure,
     Ana tare ci bamban takaici gare shi.

32.             A tarbe ka lablablab kaman babu kissa,
Idan an ka miƙe ƙafa karatun darussa,
Ga filin Ta’ala za a soko dasisa,
     Ta giba da ɓata, fashin baƙi sai a ba shi.

33.             Idan an ga haske gun samari na sunna,
Ƙira’a gwanin sha’awa da manya da gunna,
A fannin hadisi ya ci murya rawanna,
     Ana tare za ka ji gobe an sallame shi

34.             Abotar karatu yanzu ya zan na kishi,
Idan na karantarshe ka na ba ka bashi,
Abin duk da nac ce, so da ƙi, za ka bi shi,
     Kamar Rabbana kai ne ya aiko gare shi

35.             Wajen masu tinƙahon karatun shahada,
Abota a baki a zucci ƙllin makida,
Sanin yaz zamo tamkar karatun jarida,
     Abotar kwaɗai makasarta shagon farashi.

36.             Wajen masu mulki dubi saddan Husaini,
Zamanai da Tarikh munzu dogon zamani
A ƙarshenta yai sanadin kashewar Husaini,
     Tukuicin ga mai muni ina isalin shi?

37.             Hukuncin ga an yi irinsa Borkino-fasso,
Tomas shugabansu da shi da Kampore fasso,
Abotansu tai tsanani a Barkino-fasso,
     Ya harbe Thomas sai lahira babu fashi.

38.             A Nijar da Mainasara da Danda ƙasarsu,
Abokan ƙuƙut a firamare an ka san su,
Gari ɗai bukinsu guda ga sabgar garinsu,
     Ashe can a ƙirji ba ya ƙaunar ganin shi.

39.             Ya sa bindiga ta faɗa da jirgin sama’u,
Ta watse shi ɗaiɗai babu bakin buka’u,
Abota ta zan sababin bala’i fasadu,
     Ashe duk zaman da ake da ƙunshi cikin shi.

40.             Gawon yai irin ta ga Murtala kar ku manta,
Tsakanin Buhari da Iro in kun fahimta,
Zumuncin Abacha Husaini sun so kusanta,
     A ƙarshen abotar shan bala’in burushi.

41.             Ɗa Nzegu shi da Firimiya ba husuma,
Ya mai da shi tamkar ɗa ga aikin hukuma,
Da yag girma al’amarin musiba ya koma,
     Takaici daɗaɗɗe nan ya huce hushinshi.

42.             Riƙe wanga tarihi misali gare ka,
Aboki idan ya yi zamba yay yaudare ka,
Ka sa mai ido ka yi ƙoƙarin yafe naka,
     Tuwon yaudara tuƙinsa tilas ya tashi.

43.             Ka yafe ƙanana da manya-manyan jaza’i
Da mai yi duƙunce da wanda ke ta balli,
Ka saurari ƙarshen masu tunƙa da ƙulli,
     Da ‘yan sa’ido komai suke ba a fashi.

44.             Da Maula da Bn Ladan abin na da tsari,
Zama ne na Allah ba jiyewa da gori,
Zukatansu babu kwaɗai da gurin tujuri,
     Hakuncinsu kowane ittifaƙi gare shi.

45.             Suna nan a raye walau su kwanta shahada,
Ƙasa tasu ce komai tsanancin makida,
Irin shimfiɗar da sukai ta gyaran aƙida
     Jiragen Amerika babu mai kakkaɓo shi.

46.             Alu hayya! Kak ka aboci ƙaton bahili,
Ibadarku kowane lokaci kan ƙala’i,
Da mai tattalin Allah Ya koro bala’i,
     Ganin bai aje ba, baƙin nuhinai shi bi shi

47.             Abota da malammai tana sa muruwwa,
Karatu a kwasai arha sai an yi kuwwa,
A ƙauli guda an zargi laifinku rowa,
     Muridanku sun ka faɗi ga hanya na ji shi.

48.             Abokanku ladannai da ke ta da murya,
Da uttazu masu rabon nasiha a hanya,
Suna ƙorafin sadaka da zakka ta manya,
     A ɗan marmasa musu gwargwado don su san shi.

49.             Tsaya in taƙaita ma abokan amana,
Da mai son ka, mai sha’awar ka, kullum shi nuna,
Da mai son ganin ka a kulluyaumin ga sunna,
     Da mai kau da kai ga kurenka in ya yi girshi.

50.             Da mai tattalin ƙullum ka dace ga harka,
Da mai taulahin auki wajen arzikinka,
Da mai son ganin ka, kana cikin hayyacinka,
     Ka sa min da mai fatar ka samu ka ba shi.

51.             Idan kaɗ ɗaga kirkinka zai fassarawa,
Idan ka taho wa’azi yake nanatawa,
Da lurar da kai haɗarin zama ɗan adawa,
     Da tausan gabanka da hanƙuri don ka yo shi

52.             Shina son ganin ka cikin mutane na kirki,
Ga jaruntaka bai son ka gwabce da raki,
Rigayanka kuka zai yi in ya ga miki,
     Ya shafe jininka da kyau ƙuda kar su bi shi.

53.             Ku duba ga Makau Bawa babban ɓarawo,
Da Gambo ya gan shi cikin jini babu kyawo,
Ya rugo da shi asibitti yak kama yawo,
     Da rai ɓace ceton ran abokin zaman shi.

54.             Ashe Bawa baƙu yo ya lafe abinsa,
Da yal lura an watse ya niƙe jikinsa,
Ya ce: “Mai tafashe jijjiga babu kissa,
     Ka dahe su in suna ta gunza da nishi”.

55.             Abokin da duk bai kutso kai nai wurin ka,
Idan ƙaddara ta zo ya zo taimakonka,
Mutane su ƙi ka ya murje fuska ya so ka,
     Ya yo ma nasiha gwargwadon hankalinshi.

56.             Masoyinka ba ya gudunka komai musiba,
Tsayi zai yi sai an gane tsada da riba,
Abokanmu yanzu haƙiƙa in za ku duba,
     Ana zaune fuska goma kowa da nashi.

57.             Kirana gare mu a dole gyaran halinmu,
Musibar ga ta yi yawa haba ‘yan’uwanmu!
Haƙiƙan idan Ustazu ya tsai da gemu,
     Walankeluwa ga zama ya zan ya guje shi.

58.             A nan ɗan Naturai zai rufe ƙorafinsa,
Kwatancin Aliyu na Bunza in an ka bi sa,
Ana kai ga cin nasarar zama babu kissa,
Zaman nan na da, a fahinta, gyara gare shi.

                                           Aliyu Muhammadu Bunza.
                                           Alhamis 24/07/2014
                                           Sakkwato, Arkilla, 6:04.pm

No comments:

Post a Comment