Friday, December 28, 2018

Tsakanin Kabi Da Sakkwato: Kar Ta San Kar Aljani Ya Taki Wuta (Daular Kabi A Ma’aunin Bakandamiyar Buda Ɗantanoma)
Farfajiyar ƙasar Hausa tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin Bahaushe: Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[1][1]. A Kano, Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir, Jangwarzo ya hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna fintinkau. A Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin wannan takarda kallon Daular Kabi a dunƙule, tare da baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar bakandamiyar mawaƙin masarautarsa Buda Ɗantanoma mai take: “Gagara Ƙarya Sadauki; Sama Gwarzon Alƙali”. Alƙiblar nazarina ba ta rena...

--------------------------------------------
Daga 
Aliyu Muhammadu Bunza
Department of Languages and Cultures
Faculty of Humanities and Education
Federal University Gusau
----------------------------------------------------

Takadar da aka gabatar a Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University Sokoto, Second National Conference: Theme: History, People, Religion and Culture of Kebbi (Kabi) Kingdom since 1515, 10th-12th July, 2017
Gabatarwa
Farfajiyar ƙasar Hausa tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin Bahaushe: Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[2][1]. A Kano, Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir, Jangwarzo ya hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna fintinkau. A Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin wannan takarda kallon Daular Kabi a dunƙule, tare da baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar bakandamiyar mawaƙin masarautarsa Buda Ɗantanoma mai take: “Gagara Ƙarya Sadauki; Sama Gwarzon Alƙali”. Alƙiblar nazarina ba ta rena da kallon zubi da tsari, salo da sarrafa harshe da fyace diddigin jigo/jigogin waƙar ba. Na bar su ga ƙwararrun masana adabi su yi nasu buki a kan waƙar. A nawa tunani, zan yi amfani da ma’auni al’ada na biyar ƙididdiga da fashin baƙin kuramen ɗiyan waƙar da ke da ɗaukar hanakli da shiga zukatan waɗanda aka wa waƙar, da abokan gwagwarmayar su. Wanda duk ya saurari fasahar Buda cikin bakandamiyarsa ya san waƙar yaƙi ce, waƙar tarihi ce, waƙar tankiya ce, waƙar tawaye ce, kuma waƙar gwagwarmaya ce, kar ta san kar, aljani ya taki wuta.[3][2]  Waɗannan su ne gurabun da ake son a harara a cikin waƙar.

 
Wane ne Buda Ɗantanoma?
A iya sanina, Sa’idu Muhammadu Gusau ya sha cewa wani abu a kan Ɗantanoma a rubuce.[3]  Ƙari bisa ga binciken Sa’idu shi ne, Buda Ɗantanoma mutumin ƙasar Yabo ne. An ce, shi ne babban makaɗin sarkin Yabo Shehu. Tun fil azal makaɗin tankiya ne. Idan ya ɓaro kiɗinsa na tankiya ya yi jaye-jaye, ya yi wa Sarkinsa Shehu laifi aka koro shi, sai ya ruga Argungu ya ɓoye wajen maigidansa Muhammadu Sarkin Muza Bawaya. Da dubu ta cika, ya dinga yi wa Sarkin Kabi Sule habaici a waƙa aka tare shi aka karɓe turayensa aka rataye su gidan Sarki[4].  Bayan rasuwar Sarkin Kabi Sule, maigidansa Muhammadu Sama’ilan Nabame ya hau, ya dawo Kabi ya kama halinai.
Asalin sunan Buda Muhammadu, sunan “Buda” suna ne na yanayi na wanda aka haifa ana matsanancin hazo. A ƙasar Hausa, sunan “Muhammadu” ba ya ambatuwa ƙarara gaya domin kamar sunan uban kowa ne. Ana yi wa Buda laƙabi da “Ɗantanoma” ya yi rinjaye. Yana da ‘yan karɓi a waƙarsa, an ce, kotso yake kiɗa. Yana da ‘ya’ya biyu sanannu, ɗaya mace mai suna “Abingani” da namiji “Muhammadu”. Abingani a Argungu ta rasu, Muhammadu kuwa ya fara ‘yan waƙe-waƙen gado, ya bari, ya shiga duniya babu ɗuriyarsa. Akwai saɓani da yawa a kan barin waƙar Buda da rasuwarsa[5].
Salsalar Sarkin Kabi Muhammadun Sama (1920-1934)
Bayan Sarkin Kabi Kanta babu sarkin da ya yi amo a daular Kabi da zukatan Kabawa kamar Sarki Sama. Sarkin Kabi Sama’ila jikan Sarkin Kabi Sama’ila Karari ne kuma ɗan tsatso ga Sarkin Kabi Yakubu Nabame. Shi ya gaji Sarkin Kabi Muhammadu Toga. Yakubu Nabame yana kan karagar mulki daula ta rushe ‘ya’yan sarauta suka warwatse don kare mutuncin gidajensu ga hannun maƙiya. Wasu suka yi Mungadi, wasu suka doshi Kamba, wasu suka yi Argungu, wasu suka yi Arewa (cikin Arawa da Zabarmawa da Buzaye)[6]. Yakubu Nabame kakan Sarki Sama ya nufi Arewa wajen mahaifiyarsa Ba’ara. Da ya dawo Kabi da iyali ya dawo, ita ta haifa masa Sarkin Kabi Muhammadu Ba’are. Ya auri Bafulatana a Gwandu ta haifa masa Sarkin Kabi Sama (Mayaƙi).
Bayan da Nabame ya dawo gudun hijira daular Fulani ta kafu aka kama shi aka tura Sakkwato. A Sakkwato aka saka shi cikin mayaƙa, ya yi fice sosai[7]. A Sakkwato ya haifi Sarkin Kabi Sama. An ce, ɗai rana aka zana musu suna shi da Sarkin Musulmi Audu Ɗanyen Kasko[8]. Nabame a cikin gumuzun jihadi shi ya kashe wa Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo ɗa. Gorin da Sarkin Gobir Bawa ya yi masa ya sa, ya yi murabus daga sojojin Fulani ya nemi ya dawo gida, Sarkin Musulmi na wancan zamani ya aminta. Aka yi masa rakiya har Gande ya ƙaraso Gudale ya sauka. Daga nan, ya shigo Argungu ya fitar da su ƙangin Fulani ya ƙwato ƙasarsu ta gado duka ya kafa sabuwar duniyar Kabawa[9]. Bayan ya rasu, Yusuf Mainasara ya gaje shi. Bayan mutuwar Yusuf, Sarki Muhammadu Ba’are (ɗan Ba’arar da Nabame ya auro ƙasar Arewa) ƙasar mahaifiyarsa ya yi mulki. Daga gare shi sai Sarkin Kabi Abdullahi Toga wanda ya sa aka tsagaita wuta na yaƙe-yaƙe da Fulani[10]. Toga na gurgusawa Sarkin Kabi Sama ya hau karaga, ya tsinke/farke layar tsagaita wuta da Fulani ya ci garuruwan Fulani (99) da yaƙi.
Bayan rasuwar Sarkin Kabi Sama (1883-1915) ƙanensa Sulaiman ya gaje shi 1915-20. Bayan rasuwar Sulaiman, Muhammadu Sama ɗan Sarkin Kabi Sama ya dawo 1920-1934. Bayan wucewarsa ɗansa Muhammadu Sani (jikan Sarki Sama) ya hau 1934-1942. Daga riƙon Muhammadu Sani sai Sama’ila Mudi daga Kamba (fararen Lekawa) ya hau 1942-53. Daga nan, sai Muhammadu Shehe 1953-59 (kuma ƙanen Sama). Daga nan, sai Muhammadu Mera 1959-1996 (Tankaɗa Hauɓin Sama). Daga gare shi sai Sama’ila Muhammadu Mera (1996-yau) (Taka Kusheyin Sama) ya hau. A bisa diddigin tarihi Sarki Sama Mayaƙi har yanzu bai kau ba yaƙe-yaƙe kawai suka kau.
Na yarda da faɗar Aliyu Ɗandawo:
Gindi  :        Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
           :        Ila marin rugga ɗan Yakubu sa gurfani
Jagora:        Ko yanzu mai rabo ya samu ya gaƙe kowa an nan
Yara   :        Mahassada su kau an bar su suna shawagi

Hoton Daular Kabi:
Ƙasaitacciyar daula ce a ƙasar Hausa wadda Sarki Muhammadu Kanta ya kafa shekaru (502) da suka gabata. Farfajiyar daular ta kai har cikin Nguru ta daular Borno. Mayaƙanta sun dardaza faɗin ta har cikin ƙasar Oyo. Silalen ikonta ya kai har cikin ƙasashen Benin da Niger da Burkina Fasso ta yanzu. Sarki Kanta na daga cikin dakarun yaƙi na Sarki Muhammadu Askiyya. Da ƙarfi ya kawo tsoro ya ɗebe, ya ɓalle ya kafa tasa daula ta daban mai suna Kabi[11]. Daula ce da aka kafa tsakanin yaƙi, cikin yaƙi, da rigingimun hare-hare da ɗaukar fansa. Addinin Musulunci ya yi shekaru aru-aru a cikinta. Asalin sarautar Kabi takenta Amirul Muminiina, (Sarkin Musulmi)[12]. Ɗaya daga cikin manyan ƙabilunta Kyangawa, Sarkinsu Kyanga Manu ya yi aikin Hajji a ƙarni na (17ƙn)[13]. Daula ce da ta tattara Hausawa da Arawa da Zabarmawa da Nufawa da Dakarkari da Fulani da Azbinawa da Larabawa da Wangarawa da Shangawa da dai sauran ƙananan ƙabilu. A tarihance, daga Sarki Muhammadu Kanta zuwa Sarkin Kabi Sama’ila Muhammadu Mera (1996-yau) an yi sarakuna (33). Cibiyar daular ta taso daga Surame zuwa Birnin Kabi lokacin riƙon Sarkin Kabi Tomo, Sarki na (13). Ta sake dagargajewa Argungu lokacin Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na (22). Daular ta shigo mulkin Turawa lokacin  Sama (1883-1915) Sarki na (26). Gwagwarmayar Kabawa da Fulani ya sa daular durƙusawa lokacin Sarki Sama’ila Karari Sarki na (21) Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na (22) ya dawo mata da ruhinta[14]. Wannan gwagwarmayar ita ta haifar da darusan adabi da dama tsakanin Kabawa da Fulani wanda wannan waƙar da za mu yi nazari ta yi wa kakkaɓan gara[15].
Dabarun Bincike:
Tunanina na nazarin waƙar makaɗa Buda Ɗantanoma bai ba ni mamaki ba sai da na shiga aikin gadan-gadan. Na farko dai, Buda ba shi a raye. Na biyu, babu yaronsa ko yaransa na waƙa a raye. Na uku, Sarkin da ake yi wa waƙar shi ma ba shi a raye. Abin ban haushi, babu wurin da za a samu waƙar rerawar Buda da muryarsa. Don haka, dole matakin bincike na farko shi ne, neman ɗiyan waƙar ga waɗanda suka ji ta suka kama wani abu a ciki. Jerin kayayyakin rubuce-rubucenmu na bincike da kundaye babu wurin da za a tsinci waƙar bale bayananta. Dole na shiga masarautar Kabi da Gobir domin samun wasu ɗiyan waƙoƙin daga bakunan manya. Haka kuma, na dawo masarautun Sakkwato da Gwandu da Kano da Katsina domin samun wasu ɗiyan waƙar da ba a rasa ba. Na bi sawun tattaunawa da gidajen wasu fitattun mawaƙan masarautun Kabi da Gobir da Yawuri da Sakkwato domin samun ɗan abin da ba a rasa ba. Bayan tattaro waƙar, na sake tsara ta, da bitar ta, na kwatanta ta da ainihin tarihin da take son tabbatarwa. Wannan ta sa dole a tuntuɓi fitattun ayyukan da aka yi a kan daular Kabi domin kwakkwahe zaren tunanin Buda Ɗantanoma[16]. Shiga ɗakunan karatu da gidajen adana tarihi musamman na daular Kabi da Sakkwato ya agaza ainun. An tattauna muhimman mutane a fadar Kabi da Sakkwato da ke da alhakin sanin wani abu a kan daulolin da shi kansa Ɗantanoma da waƙoƙinsa. Na yi amfani da ɗiyan waƙar da na samo babbarkatai domin daidaita tunanin waƙar a tsarin salon waƙar baka.


Bakandamiyar Buda:
A tarihi, Kabawa ba su da wata waƙa a masarautarsu da ta cancanci sunan bakandamiya in ba wannan ba. Fitattun jaruman mawaƙan masarautar Kabi irin su Ata da Kaaree (makaɗin jama’a) da Aliyu Ɗandawo (makaɗin Mamman Shehe) da Gero Zarto da Ɗan Kawu da Jatau (makaɗin S. Shiko) da Ata (makaɗan Nabame) ba su yi wa masarautar Kabi waƙar ɗebe takaici irin waƙar da Buda Ɗantanoma ya yi ba. Gindin waƙar shi ne:
: Gagara ƙarya sadauki
: Sama gwarzon alƙali.
Asalin waƙar ita ce, bakandamiyar da yake yi wa Sarki Sama[17]. Babban abin da ya sa ta yi fice sosai shi ne, a taron dabar da aka yi a Kano zamanin Sarkin Kano Shehu na tarbon ɗan sarauniyar Ingila Prince Edward 1925. A taron, Sarkin Kabi Sama ya fita da doki (500) mayaƙa yan baka (500) masu harugga (500) dakaru (1500) ke nan. A gaskiya, Sarki Sama fitan yaƙi ya yi, don haka duk wani basarake da ya halarci taron tsawonsa bai kai na Sarkin Kabi Sama ba. Sarki Sama bai sauka cikin garin Kano ba, ya nemi a ba shi babban fage da zai sauka da dakarunsa. Sarkin Kano Shehu ya ba shi farfajiya babba a wajen birnin Kano aka sauke kayan yaƙi. Wurin ya zama wata babbar matattara, a zo a ga Sarki, a ji Sarki, a ga dakarun Sarki. Bayan ƙare taro, wurin ya zama babbar unguwa mai suna “Fage”[18]. Bakandamiyar ta kakkamo duk abubuwan da suka faru, tun fitan Sarki Sama daga Argungu har ya je Kano ya dawo, da abubuwan da suka faru a taron daba. Bakandamiya waƙa ce, ba dole duk abin da ta kamo iya tsawonsa da faɗinsa ke nan ba, wani a ƙara masa tsawo, wani a rage masa faɗi, wani a bar shi yadda yake. Duk da haka, bakandamiyar Ɗantanoma daular Kabi ta kasa a faifai ga mai tababa ko musun ɗaukakarta da ƙasaitarta a duniyar zamaninta.
Zaren Tunanin Bakandamiyar Buda:
Ga ɗan abin da na kalato na waƙar bayan na yi tankaɗe-da-rairaya sosai na riwayoyi daban-daban da na samo. A ɗan ma’aunina ana iya regon kayan cikin waƙar Buda kamar haka:
Ƙasar Kabi da Abokanta
A cikin amon turun Buda ƙasar Kabi ba ta da abokiyar da ta kai Gobir. Da Kabi da Gobir ba su taƙama da komai face yaƙi na kare martabar gida da darajarar kakanni[19]. Bugu da ƙari, da Kabi da Gobir su ne alaƙaƙai ga Fulani da mulkinsu tun gabanin jihadin ƙarni na (19ƙn) da lokacin jihadin, da kuma bayan jihadin. Da yaƙe-yaƙen addini, da na faɗaɗa ƙasa, da na mulkin mallaka suka lafa, aka share jini abin ya koma wasa. Buda ya taɓo wannan silalin tarihi a turunsa da ke cewa:
Jagora: Kanta da Bawa nis sani
          : Jangwarzo ba mu san Hillani ba
          : Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali
Wane ne Sarki Sama a Tafashen Ɗantanoma?
Sarkin Kabi Muhammadu ɗan Sama’ila wanda aka fi sani da Muhammadun Sama ko “Sama” kawai a tafashen Buda, ba kanwar lasa ga abokan adawa ba ne. Tsananin yaƙin Sama ya sa ake yi masa laƙabi da “Mayaƙi" Buda ya taɓo gwarzantaka da muhibba da buwayarsa kamar haka:
Jagora: Sama na Audu mai hawan ban kashi
          : Mai tamburran fama
Gindi: Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali
Jagora: Sama ɗan Nabame da dambun Masu[20]
          : Ba cin yaro na ba.

A ganin Buda, babu wani Sarki a farfajiyar Sudaniyya in ba Sama ba, domin jarunta ce sarauta, Sama ko a ko’ina ya kai. Dubi yadda Buda ke ciciɓa shi da faɗar:
Jagora: Sarkin sarakuna shiryayye
          : Ba kowa nan sai kai
Gindi: Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali
Jagora: Ka ji Sarki ka zo ka iske Sarki
          : Ba Sarkin ƙage ba.
Bayan Buda ya kore duk wani sarki in ba Sama ba, ya kuma jaddada faɗar duk wani sarki a sudaniyya in ba Sama ba ne Sarkin ƙage ne. Sarkin ƙage shi ne Sarkin da ke karɓar umurnin wani Sarki domin haka Ɗantanoma ya tabbatar da cewa:
Jagora: Ɗan nana Hausa ba a mai da awa shi,
          : Dac can kuma ba a yo ba[21].
Gindi: Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali.
Jagora: Mamman mai komi mai kowa
          : Kuma kai aw wan kowa
          : Ba matsuwa na Bubakar
          : Sa tuba ba sake faɗin na yi.
Waɗannan ɗiyan waƙoƙi duk suna hararar sarakunan daular Sakkwato ne da ke hannun Fulani. Don haka “kowa” ga Fulani take komawa. Haka kuma “Sarkin Sarakuna” ya haɗa da Fulani. Tirƙashi ji wannan:
Jagora: Mamman mai wada yas so
          : Sarkin ɗibah haushi[22].
Matsayin Sarautar Kabi:
A al’adance, sarauta ba ta amo ta yi tasiri sai ta yi gwagwarmaya da abokan hamayya ta fatattake su, a kama na kamawa, a kashe na kashewa, mai rabon ganin baɗi ya tsere ko ya yi hijira. Daular Kabi tana tinƙaho da nagartattun kakanni da ba su miƙa wuya ga kowa ba kamar ragon suna. Don haka, Buda ke kiran mai Kabi Sama da cewa:
Jagora: Sama maganin ƙiyayya rabuwa
          : Kore ƙaton banza
Gindi: Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali
Jagora: Sama kore tsagera ba ni gidanai
          : In sa turayena.
Ɗantanoma na tabbatar da cewa, masarautar Kabi ba ta da sauran maƙiya domin ta ƙore Fulani. An raba su da ƙasar Kabi, kare jini biri jini, don haka yake son a kore sarakunansu a karɓe gidajensu a matsayin ganima, makaɗan fadar Sama su samu wurin rataye turayen fama. Buda ya sake nuna irin matsayin sarautar Kabi da ta ci Fulani da karɓe musu tamburan kakaninsu.
Jagora: Ga wani ya ga tamburan kakanai,
          : Ba za a kiɗa mai ba.
Gindi: Gagara ƙarya sadauki
          : Sama gwarzon Alƙali
Dukkanin makaɗan masarautar Kabi sun tafi a kan cewa Sarautar Kabi ita ce shakundum. Da yawa sukan ambaci sarakunansu da: Shugaban dama da hauni, ko babban bajini, ko shugaban tahiya, ko sarkin sarakuna, ko mai dama da hauni ga su nan dai.
Kushe Sarkunan Fulani:
Babban dalilin da ya sa Buda Ɗantanoma da waƙarsa suka yi fice shi ne zambo da habaicin da yake yi wa sarakunan Fulani. Da Buda ya fara da babbar sarautar daula ya fara da ita wato sarautar Gwandu yana cewa:
Jagora: Sarkin Gwandu ya nashe mu da yula
           : Hat taf hwaɗa gulbi

Raddin da Buda ya bayar kan nashinsu da yula da aka yi shi ne:

Jagora: Sarkin Gwandu ɗan gajere
          : Daidai kwaɓin laka.

Bayan an taɓo Sarkin Gwandu, sai aka bi ƙananan sarakunansa, ɗaya bayan ɗaya, ana muzantawa. Ga ɗan abin da aka ruwaito daga Ɗantanoma:
Jega   :        
: Sarkin Jega yau tsawo yai kauri
                             : Daidai kamun kura.

Ɗakingari    :        
: Sarkin Ɗakingari dogo rusheshe
                              :  Daidai takin dambe.
         
Tambuwal   :
: Sarkin Tambuwal Ba’uden banza
                              : Sheshenai na jimen
                              : Runji shi ka wa yanka[23].
Alero :
                             : Alero nig ga guntun Sarki
                             : Daidai kwaɓin laka.

Ambursa:
                             : Ni na zo Ambursa na ga Sarki
                             : Da baƙi ƙoƙe ɗan mai shuni
                             : Sarki da ƙuraje ga jikinai
                             : Ƙoƙe ɗan mai ƙwarya.

Wajen Ƙasar Hausa:
Hatta da sarakunan da ke hulɗar arziki da ƙasar Gwandu Ɗantanoma bai sa musu ido ba. Da ya je Doso Zarmakwai ya ji an ce, yana zagin Sarkin Gwandu sai ya ji tsoronsa, ya ba shi doki kyauta toshiyar baka, kar a tallata halayensa ga abin da Ɗantanoma ya ce:
Jagora: Doso nig ga wawan Sarki
          : Shi had doki yab bai.
Yawurawa ba su ce masa uffan ba, amma saboda dangantakarsu kyawawa da Gwandu da kuma daular Sakkwato Ɗantanoma ke cewa:
Jagora: Ɗansanholama na bakin kogi
          : Ba mu san tushenai ba.
Gumuzun Sarkin Kabi da Sauran Sarakuna a Kano (1925):
Dabar da aka shirya Kano 1925 ƙasaitacciya ce. Kowane Sarki ƙwazo yake son ya yi, a ga ya cira tsara, a hawan dabarsa. A fagen dabar, babu Sarkin da Ɗantonoma ya ragawa, sai in bai gan shi ba. Ga yadda Ɗantanoma ya fasa baƙi.

Haɗuwar Sarkin Musulmi Tambari da Sakrin Gwandu Shehu da Sarkin Kabi Sama a Bunguɗu kan Hanya zuwa Kano
An ce, Sarkin Musulmi Tambari ya fara riskar Sarkin Kabi Sama a Bunguɗu. Ya zo ya tarar da su, karo na farko da suka fara gaisawa ta girma da arziki. Sarki Tambari ya ce wa Sarkin Kabi Sama: “Mai Kabawa muna lahiya”, Sarkin Kabi ya amsa da cewa: “Mai Hillani lahiya lau”[24]. Yana cikin motarsa, Sama na kan dokinsa. Nan Ɗantanoma ya ce:
Jagora: Ga wani ya shigo barayar kusa[25]
          : Yac ce mota yah hau
          : Ga wani ya shigo cikin kwandonai
          : Yac ce mota yah hau
          : Motar ƙwarai tana ga Nasara
          : Katako na Hausa.
Bayan da Sarkin Musulmi Tambari ya fito mota aka gaisa, ya shiga mota aka ruhe gam! Ɗantanoma ya ce:
: Mu sarkinmu bai shiga zunguru[26]
: Don ba balli na ba
: Ko dai an tai Kano da sauri
: Jayen munta an kai.
Jim kaɗan ga Sarkin Gwandu cikin mota “A kori kura” da shi da Sarkin Kabin Jega Modi suna gaba, sauran ƙananan sarakuna na bayan bodi zaune. Suka gaisa da Sarkin Kabi, sai kallo ya koma ga waɗanda ke cikin mota, ana ta kururuwa da mamakin yadda mota ɗaya ta ɗauko manyan mutane haka. Ɗantanoma ya hau bakinsa:
Jagora: Na hore ka kak ka sai katako
          : Saye ɗan Azbin Sarki!
: Doki shi ka taƙama a yi kallo,
: Ba katakon wofi ba,
: (Ƙyale iskan banza)
: Motaƙ ƙwarai tana ga Nasara
: Katako na Gwandu.
Ganawar Sarkin Zazzau da Kano da Sarki Sama:
An ce, sun zauna wuri ɗaya suna tattaunawa a dandalin taro. Sarkin Kano ya sha alkyabba da naɗi da sandar sarauta da kayan alfarma. Sarkin Zazzau ya shawo babbar riga mai aiki ɗaba-ɗaba a fuskanta mai ɗaukar hankali. Sarkin Kabi Muhammadun Sama ga al’adansa, koyaushe fararen kaya yaka yi ba su da aiki gaba da baya, tun fil azal malami ne. Da Ɗantanoma ya ga kallo ya koma sama shaho ya ɗauki raƙumi, domin aiki Sarkin Zazzau na riga ya burge ‘yan kallo sai ya ce:
Jagora: Ƙawa da ulu sai ‘yan mata[27]
          : Sai dottijon banza,
          : Kai Sarkin Kano taho ka ga Sarki
          : Ba ɗai ga waɗannan ba.
Shirin Hawan Sarkin Kabi Sama da Ƙwarjininsa:
A ganin Ɗantanoma wajen hawa wani Sarki ke tsere wani Sarki. Sarauta iko ce, iko ko da ƙarfi ake yin sa da gwarzantaka. Tun a cikin gida Fulani suka fara firgita. Ɗantanoma ya ce:
Jagora: Sarkin Isa ya ga damman masu
          : Bai san yaƙi na ba.
Da aka biyo ta Sakkwato suka firgice sosai domin ganin irin shirin da Sarkin Kabi ya fito da shi. Ɗantanoma ya ce:
Jagora: Hawan da yay yi Sakkwato
: Sada zumunta na
: Bai so su ji tsoro ba

Da aka shiga birin Kano cewa aka yi:

Jagora: An ce ba a wa Kano takakka
: Mamman ya tattake ta
:An ce ba a zo a Kano takakka
: Amma Mamman ya yi
: An ce ba a wa Kano takakka
: Sama ya tattake ta
: Don mun zo Kano da dambun masu
: Ba mu samo gaba ba[28].
Ƙarfin Sojan Daular Kabi:
Idan aka ce waƙa bakandamiya ce, babu abin da ba a iya samu a ciki. Ga al’adar waƙa, bakandamiya ba a ƙare ta domin duk wani muhimmin abu da mawaƙi ke son ya adana, a ciki yake kai shi. A cikin ƙoƙarin fayyace Dabar Kano, Ɗantanoma ya baje kolin irin ƙarfin dakarun daular Kabi da ya gagari Fulani, kar ta san kar! Dantanoma na cewa:
Jagora: Taron Kano da an ka yi
: Sama shi Allah Yas so
: Shi Sarkin Kano da yas san daidai
: Tarbon bahago yay yi
: Ko sarkin Kano da yas san daidai
: Tarben manya yay yi
: Sarkin Kano da shi da garinai
: Rannan daji yak kwan
: Malaman gari ka cewa Sarki
: Taso ka shige birni.
Iya irin makaman zamaninsu Daular Kabi ta tanada wa dakarunta, don haka ba ta kwana da fargaban  kowace daula ba, a ƙarƙashin kowane suna aka kafa ta. Ɗantanoma ya fi kowa sanin haka, don haka yake ce wa Sarkin Kabi Muhammadun Sama:
Jagora:        Gyara takubba na Yari tallabi masu
          :         Shiga birni ba kowa.

          Cikin ɗawainiyar tafiya zuwa Kano Buda na cewa:

Jagora:        Bahago ya zo Gusau da rarar ƙarfi[29]
          :         Ba a sake haye mai ba
          :         Nan yai karo da Sarkin Ƙaura
          :         Yaw watce mutanenai.
Ga alama, irin wannan arangamar ya sa Sarkin Bunza ya ji tsoron kai wa Gwandu gudunmuwa a yi karo da Sarkin Kabi. Buda cewa yake yi:

Jagora:        Bunza nag ga karnan Sarki [30]
          :         Ɗan Gurumaɗan Bunza
:         Da yaj ji za a gamamma
:        Rancen ciwo yay yi.
A tsarin ƙarfin sojan Sarkin Kabi akwai dawaki da raƙumma da dakaru ‘yan ƙasa. Da za a je Kano taro Buda yi lisafo su kamar haka:
Jagora:        Doki ya yi fiffike ya yi baƙi
          :         Ba mu gane iyaka ba.
          :         Dan nan baya raƙumi ya fi dubu
          :         Tsinin mashi zalla
          :         Can gaba ko uban dawa da ɗiyanai
          :         Tsinin kibiya zalla
          :         Ga sulke da bindiga ga masu
          :         Ga tamburran fama.
Taron Dabar Kano:
A hanyar zuwa Kano Sarkin Kabi sama ya bi hanyar Shuni ya sauka Dange wajen Sarkin Bauran Dange Hassan Ɗan’mu’azu (1931-38). Ya kwana Sanyinna da Shagari da Kamɓama da Tsamiya da Tureta da Murai da Bunguɗu da Kwatarkwashi da Gusau. Ya bi ta Tsahe da ‘Yankuzo, darzaje daki-daki[31]. Sarkin Kabi gamgami ya yi sosai zuwa taron domin Buda ya ce:
Jagora:        Daga Ilo hak Karekare
          :         Duka sun zo jiɗag gwannan farko.
Makaɗa Buda ya ba Sarkin Kabi haƙuri cewa ba kiran Fulani ne ba, taron gwannati ne.
Jagora:        In ba don yana kiran taro ba
          :         Sama ba mu zuwa Hausa
          :         Bahago kak ka ji komai
          :         Ba nasu kira na ba
          :         Mamman kak ka ji komai
          :         Ba su ka kiran nan ba.
Duk da haka, Ɗantanoma ya ce, su suka ci ƙwallo a taron domin a tasa faɗi cewa ya yi.
Jagora:        In a je gida a ce wa Tsahara
:         Mu namu nuhi ya kai
:         Don kai gwanna yam miƙa ma hannu
:         Sannan yab ba kowa.

A zaton Ɗantanoma, in an zo dabar Kano, Sarkin Nupe Kabi zai mara wa ba Sakkwato ba, domin daular Kabi ta kai har ƙasar Yarbawa kuma Nufawa sun more wa tsaron daular Kabi[32]. Da Ɗantanoma bai ga sarkin Nupe bayansa ba, ya ce:
Jagora:        Ga wani ya zo Kano
          :         Kamar bai zo ba
          :         Inda ɗan mai koko.
Ana wata ga wata:
Baya an kammala dabar Kano, aka fahimci akwai buƙatar a samu haɗin kan sarakuna gaba ɗaya, a share jini a koma wasa. Daga can aka shirya yadda za a yi sulhu tsakanin daular Kabi da Sakkwato kowa ya fahinci juna[33]. Wurin da Gizo ke saƙa shi ne: wace ƙasa za a yi zaman sulhu? Wa zai kira wa, a yi sulhu? Wa zai jagoranci taro? A wata riwaya an ce, da aka dawo daga Kano a kan hanyar zuwa gida a mararrabar Kanoma aka ce Sarkin Kabi ya biyo Sarkin Musulmi Tambari a bi hanya ɗaya. An ce, nan Ɗantanoma ya hana ya ce:
Jagora:        In an je gida a ce wa Tsahara
          :         Tabkin da tas sani bana ya koma laka
          :         In an je gida a ce ma Tsahara
          :         Kabi ta koma rugga
:         In an je gida a ce wa tsahara
:         Gaba ta koma baya
:         Don sarkinmu bai biyan wani Sarki
:         In ba Allah na ba.

Da jin haka, sai Sama ya ɗan jinkirta aka sake shawara. Da Ɗantanoma ya ga ‘yan shawara na son su ci nasara, a bi hanya ɗaya da Sarkin Musulmi, a fara shiga ƙasarsa (wato Hausa) yana gaba Sarkin Kabi na baya. Kai! Wane mutum in ji mutuwa, ya dafi tafashen fama ya hau bakinsa da cewa:

Jagora:        Haba Sama in biya ka kai
:         Ka zo ka bi Turai in san manya kab bi
:         Kanta da Bawa nis sani
:         Jangwarzo ban san Hillani ba.

Da furta wannan ɗan waƙa, miki ya koma sabo, aka tashi baran-baran, kar ta san kar, kowa ya kama hanyarsa.
Tsarin Hawan Daba:
An tsara hawan dabar bisa tsari irin na hukuma ba na gargajiya ba. A tsarin, Turawa ne na farko, don haka dai ana nan zaman bayinsu biye da su ake a koyaushe. Wannan abin ban haushi ne ga wanda ya fahinci wulaƙanci irin na mulkin mallaka. Wajen da aka taɓo Ɗantanoma sai aka ce, bayan Turawa sai waƙilan gwannati bayansu. Sarakuna su biyo baya a bisa tsarin darajar da gwannati ta yi. A tsarin Sarkin Kabi shi ne Sarki na goma sh uku (13). Ɗantanoma bai yarda ba, sai ya tsare ido a fagen, ana fara kiran Turawa ya dafi turunsa ya kira Sarkin Kabi Sama da cewa: (Sama/Haba!)
Jagora:        Zaburo biyo Turawa
          :         In san manyan Kab bi

Jagora:        Maza furce gabansu
          :         Bi ma Bature in san manya kab bi.
Wayyoyoyo! Ɗantanoma ya yi makaɗi: Sama ko ya yi Sarki ko’ina aka Sarki. Haba! in kai ne yaya zaka yi?
Barazanar Daular Kabi ga Daular Fulani (Hausa)
          A lisafin Kabawa, duk wata ƙasa da ba ta Fulani ba, kuma Fulani suka ƙwaci mulkinta sunanta “Hausa”. A tarihin artabun Kabawa da Fulani, Kabawa suna iƙirarin su suka ci nasara. Dalilan Kabawa kuwa shi ne, Sama ya ci garuruwan Fulani (99). Kabi ta ci Ambursa, ta kuwa ragargaza Fulani a yaƙin Alwasa. Ba za a musanta cewa, Fulani sun taɓa cin galaba a kan Kabawa ba musamman idan aka nazarci karon battan Sarki Muhammadun Sama da Sanyinnawa ƙarƙashin jagorancin Mijin Jewo[34]. A koyaushe, idan ana bukin shekara-shekara na salla da kamun kifi da shan kubewa da gaɗa da annashawa taken Kabawa shi ne:
Jagora:        Kabi ta ci Hausa
          :         Da mi tac ci Hausa?
          :         Da ƙarfi da yaji
Wannan barazanar har gobe ba ta guje ga bakunan Kabawa ba, wai ko ana taya fansa. Tsananin tsoron da ake yi wa Sama ya sa Ɗantanoma cewa:
Jagora:        Wani ya faɗi ya kare ga tsaratai
          :         Bai san rame na ba.
          :         Wani Sarki shina biɗan barwanai
          :         Bai san jama’atai ba
          :         Da dai a yamutsa na
          :         Da wasu sun yi baran ƙosai.
Matsayin Waƙar Buda Ɗantanoma a Ƙsar Hausa:
A wajen Buda da Kabawa babu wata waƙa da ta fi waƙar Buda tasiri. Waƙar Buda bakandamiya ce, komai ake son adanawa a ciki ake kai ta. A ɗan nawa bincike, tsofafi da Sarakunan Kabi na da wannan waƙa tarshe take bakunansu kamar Fatiha a bakin liman. A gaskiya, talakawa na ɗan jin tsoro rera ta saboda cin zarafin Sarakuna da ke ciki. Mawaƙan Gobir da Kabi, bayan mutuwar Ɗantanona suka dinga rera ta da muryoyi daban-daban da ‘yan ƙare-ƙare da rage-rage. Waƙar Ɗantanona wata taskar tarihi ce da ba a yi kamarta ba a gabaninta, a bayanta ba a samu ba. Don haka, za mu iya cewa; waƙar Gagara ƙarya ta Buda:
1.     A wajen Kabawa furen kallo ce domin kakaninsu ake zugugutawa da cicciɓawa a kan abokan adawa.
2.     A ɓangaren daular Sakkwato wani ƙalubale ne ga Sarakunanta da jama’arta a kan daɗaɗɗiyar adawa.
3.     Waƙar wata taskar tarihi ce, duk da sanin cewa, ba a rasa hazon soyayya da ƙiyayya a ciki, wanda zai kawo cikas ga haƙiƙanin tarihi.
4.     Waƙar wata allura ce da a koyaushe za a ji da sauran rina a kaba. Tattare da sanin cewa, rinar ta tafi abinta, amma waƙar Buda ta yi wa kabar da rinar ta yi wa gije kadada don tuna baya.
5.     A hangen Buda, abin da ke tsakanin Kabi da Sakkwato ba addini ba ne, siyasar mulki ce, don haka bai taɓa kawo zancen addini ciki ba, wannan wani haske ne na fuska biyu da wasu Hausawan ƙasar Hausa ke kallon jihadin ƙarni na (19ƙn)[35].
Sakamakon Bincike:
 Yadda jihadin ƙarni na 19ƙn ya yayatu a ƙasar Hausa; haka waƙar Buda ta yayatu a ƙasar Hausa. Da su Kabawa da Fulani duk suna rera ta a matsayin tuna baya da raha. Mafi yawan daulolin duniya da ƙasaitattun Sarakuna da masu mulki sukan yi amfani da haziƙan adibbai/mawaƙan lokacinsu domin kare kansu da sarautunsu. Da ba don waƙar Buda ba, da tuni an manta da irin artabun da Kabawa suka yi da Sakkwato. Daga cikin  abin da na hango akwai:
1.     Da ɗan gari akan ci gari. Asalin Buda ɗan Yabo ne ƙarƙashin riƙon Sakkwato don haka Kabawa ke amfani da shi a matsayin ɗan leƙen asirinsu.
2.     Bakandamiyar Buda tattare da farin jinin da ta yi a halin yanzu, babu ita a rubuce, babu ita a kowace irin taskar taskace adabi[36].
3.     Dalili da wannan sai a ga kowa abin da ya ga dama yake faɗi a kan sarkin da yake so ko baya so sai ya ce: inji Buda[37].
4.     Babu Bakaben asali da ke tir da waƙar Buda, haka kuma babu Bafulatanin ƙwarai da zai yi madalla da ita.
5.     Ɗa ba don Buda ba, da dabar da aka yi wa Prince Edward, a shekara (1925) ba ta samu shiga adabin Hausa ba.
6.     Da Kabi da Gobir yaƙi da Fulani ya haɗa su zumunta, kowanensu abokin adawa ne da daular Sakkwato. Haka kuma, daulolin biyu da yaƙi suke bugun gaba, makaɗin yaƙi ya fi karɓuwa gare su da samun yardarsu, don haka Buda ya samu karɓuwa kabi da Gobir.
Nasarar da wannan bincike ya yi ita ce ƙwaƙwalo ɓatattun ɗiyan waƙar Buda daga bakunan da suka san shi, suka ji shi, ko suka kwaikwaye shi. Samar da ɗan wani abu a rubuce nata cigaba ne tare da fashin baƙin kuramen wasu ɗiyan nata.
Naɗewa:
Raya daula da ɗaukakar martabarta yana a hannun masarautanta. Sarki shi kaɗai ba ya mamaye daula/ƙasa sai da cikakken goyon bayan mutanenta. Daular Kabi ta samu wadatattun Sarakuna ‘yan kishin ƙasa da amintattun talakawa ‘yan ga-ni-kashe-ni. Cikin wannan ɗawainiyar aka ci karo da fasihin mawaƙin tankiya da ba a yi kamarsa ba a ƙasar Hausa. Makaɗa Buda Allah Ya haɗa jininsa da daular Kabi, babu yadda Sarakunan Yabo ba su yi ba, su tsayar da shi ƙasarsu ya ƙi. Kabawan ma da suka yi masa ɗawainiyar nuna isa don ya tabbata ƙasarsu ya gaya musu cewa, ƙauna ce yake da ita gare su ba don abinsu ba, kamar yadda yake cewa:
Jagora:        Algargi ba ta wa mai turu
          :         Da ya koma Yabo[38].

Haƙiƙa, gawurraccen makaɗi shi ne rayuwar kowace daula da adana martabartar ta. Ba don Buda ba, da sunan Kabi bai mamaye ƙasar Hausa ba. Ba don Narambaɗa ba, wa ya san Isa da Sarkinta. In ba turun Dan’anace ba, sunan Shago ba zai wuce Mafara ba. Ba don Gambo ba Muhammadu Inuwa Danmaɗacci ko Jega ba a ji ɗuriyarsa ba. Lallai makaɗa Aliyu Ɗandawo ya tabbatar da ƙunshiyar bakandamiyar Ɗantanoma a faɗarsa.
Jagora:        In hadari ya taso
:         Cikin iyawar Allah
:         Giragizai su ka zuwa
:         Su taushe kaihin rana
:         Mutane waw waye duhu
:         Nabame yaw waye duhu
:         Yay yi ma azna fitila
:         Yag gaƙe Torankawa
:         Gudunmuwa kaz zaka ka ya ishe shi ya sha kaihi
:         Mutun guda ya hi gaban mutum dubu
:         Magabata abin da sun ka hwaɗi
:         Ai mai da hwaɗi ɓanna na.
Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
          :         Ila harin rugga ɗan Yaƙuba sa gurfani.


Manazarta
Adamu Mahdi 1978 The Hausa Factors in West African History, Zaria:
          Ahmadu Bello University Press.

Adeleye, R.A 1971 Power and Dipplomacy in Northern Nigeria 1804-
1906: The Sokoto Caliphate and Its Enemies, London: Logman Group Limited.

Al-jahh, M.A. 1967 “ A Seventeeth Century Chronicle of the Origins and
          Missionary Activities of the Wangarawa,”  Kano studies, 1,4.

Alkali, Muhammad Bello 1969 “ A Hausa Community in Crisis: Kebbi in
          the 19th Century,” MA Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.

Auta, A.L. 1986 “ Gudumuwar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da
          Adana Tarihi,” Kundin MA, in Kano: Jami’ar Bayero.

Balogun, S.A 1970 “ Gwandu Emirates in the Nineteenth Century, with
Special Reference to Political Relations: 1917-1903,” PhD Thesis Ibadan University of Ibadan.

Besmer, F.F 1971 “ Hausa Court Music in Kano, Nigeria,” PhD Thesis
Columbia: University of Columbia.

Birnin Tudu, M.S. 1984 “Kamun Ƙafa A Ƙasar Argungu Kundin BA
          Sokoto: Jami’ar Sokoto

Blackwell, H.F 1927 The Occuaption of  Hausaland, 1900-1904, Lagos.

Bunza, A.M. 2016 “Agitation and Dialogue in Hausa and Fulɓe
Encounters: (Reassessing the Hausa Version aa Depicted in Hausa Orature)” Paper Presented at International Conference or  Fulɓe Language, Literature and Culture Organized by the Centre for the Studies of Nigeria Language and Folklore, Kano: Bayero University 28th – 30th March, 2016.

Bunza, A.M 2016 “Ƙunar Baƙin Wake: Ƙalubalen Tsaron ƙasarmu
(Daba Cikin Tunanin Bahaushe: Abin da ya Karo Ɓera ya-------)” Takardar da aka gabatar  a taron ƙasa na ƙara wa juna sani a Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato, March, 2016.

Dokaji, A.A 2002 Kano ta Dabo Ci Gari, Zaria: NNPC.

Gusau, S.M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa Kaduna.  Fisbas Media       Services.

Hogben, S.G. 1967 An Introduction to the History of Islamic State of
          Northern Nigeria, Ibadan.

Hisket, M. 1994 The Sward of Truth, Evanson.

Hisket, M. 1984 The Development of Islam in West Africa, New York.

Hopen, C.E 1985 The Postoral Fulɓe Family in Gwandu, London.

Hopkins, A.G.H 1975 An Economic History of West Africa, London.

Johnston, H.A.S 1967 The Fulani Empire of Sokoto, London: Oxford
          University Press.

Johnston, Samuel 1921, The History of Yorubas, London.

Junaidu, Alhaji 1957 Tarihin Fulani, Zaria: NNPC

Last, Murray 1968 Sokoto Caliphate, Ibadan University Press.

Magaji, A. 1980 “Alhaji Kassu Zurmi da waƙoƙinsa,”  Kundin BA,
          Kano: Jami’ar Bayero.

Mangati, B. 1985 “Waƙar  Gagara Ƙarya Sadauki ta Marigayi Buda
          Ɗantanoma” Kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Meek, C.K. 1971 The Northern Tribes of Nigeria General Studies no 97
          vol. 1 Frank Cas and Co.Ltd.

Muhammadu, D. 1981 “Bakandamiya” Towards a Characteristics of the
Poetic Masterpiece in Hausa in Oral poetry in Nigeria (ed) Abalogun and Others Lagos: Nigeria Magazine.

Muri, Aliyu Muhammad 2003 “ The Defence Policy of the Sokoto
Caliphate, 1804-1903” PhD Thesis, Department of History, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.Nadama G. 1977 “The Rise and Collapse of a Hausa State : A Social and
Political History of Zamfara,” PhD Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.

Njeuma M.Z 1969 “The Rise and Fall of Fulani Rule in Adamawa, 1809-
          1901,” PhD Thesis London.

Raglan, L.F 1932 The Hero, New York: Oxford Univerdity Press.

Smaldore, J.P 1977 Warfare in the Sokoto Caliphate: Historical and    Sociological Perspectives. London: Cambridge University Press.

Smith, M.G. 1960 Government in Zazzau 1800-1950, London:
          University Press.

Smith M.G. 1997 Government in Kano 1350-1950, USA Westview
          Press.

Umaru, A.M.  2008 Daular Fulani a Kano, Kano: Bechmark Publishers

Usman, Y.B 1974 The Transformation of Katsina 1400-1883, Zaria:
          Ahmadu Bello University.

Zurmi, M.A. 1986 “Rayuwar Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa,”
          kundin BA,  Sokoto: Jami’ar Sokoto. [1] .            An yi ayyuka masu ma’ana a kan waɗannan dauloli. Fitattu daga cikinsu akwai: Dokaji, Kano ta
Dabo ci Gari da Smith, Government in Kano, da Usman, Transformation of Katsina, da Augi
“Gobir. Factor, “da Smith Government in Zazzau, da Nadama, “Zamfara in the 19th Century”,
1968.
[2] .            Gaba ɗaya wakar a kan Fulani ta ƙare da masu goyon bayan mulkinsu. Waƙar yaƙi ce mai
tabbatar da rinjayen Kabawa ga Fulani a fagen daga. Waƙar tarihi ce, domin ta yi waiwaye
ainun a kan tarihin yaƙe-yaƙen Kabawa. Waƙar ta tankiya ce, babban burinta ta hasa wuta a zukatan Kabawa su tsaya matsayinsu komi taka zama ta zama. Waƙa ce mai jaddada tawayen daular Kabi a kan daular Sakkwato da suke ganin daular Fulani ce kawai. Don haka, waƙar gwagwarmaya ce tsakanin ƙabilu biyu Kabawa da Fulani.
[3] .            Ya ambace shi cikin littafinsa S.M Gusau, Makaɗa da Mawaƙan Hausa, 1996, Kaduna; FISBAS
[4] .         Riwaya biyu ke ga wannan tarihi. Wasu kuwa ce wa suka yi, lokacin da ya rera wani ɗan waƙa:
Jagora   : Lamso nis sani da Tsahara
                                : Ban san kingin nan ba
Lamso da Tsahara su ne matan da ke yi masa kyauta. Da sauran matan kishi ya kama su aka ce musu “kingi” suka ce, a kawo turayen a rataye ya daina waƙa. Ya mayar da raddi da cewa:
Jagora    : Turu aka amsa a rataye
                                : Bakin Buda yana garai.
[5] .            Wasu mutane musamman Gobirawa suna cewa, Sarkin Musulmi Tambari ya sa aka yanka shi.
A nawa bincike a Argungu da Bunza da Dukishi da Geza da Zariya. Bayan mutuwar Sarki Sama
Buda ya yi hijira da yaransa zuwa yamma. Na sami wasu tsofafi a garin Dukushi da suka tabbata cewa, sun gamu da Buda da yaransa wani ƙauye mai suna Balu ta ƙasar Kabi a kan hanyarsa ta Kamba. Ana zaton can cikin ƙasar Kamba ko jamhuriyyar Nijar ya rasu. Wasu kuwa cewa suka yi, ya roƙi Allah ya kashe shi gabanin Sama Allah ya karɓi roƙonsa.
[6] .            Tattaunawa da Sulaiman Nabame, ɗan Sarautar Kabi kuma ma’aikaci a gidan Tarihin Kabi. Na
yi hira da shi cikin Gidan Tarihin Kabi kusan awa 2-3, ranar 20/06/2017. Suleiman yana da
digirin Hausa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, 2003.
[7] .            Dukkanin Kabawan da na yi hira da su, sun ce an yanke wa Nabame hukuncin kisa, daga baya
aka ce a tura shi fagen yaƙi ya mutu can a huta. Da Allah bai yi mutuwarsa ba sai da ya ɗauko fansa. Tattaunawarmu da Sambo Wali da Yakubu Bagaye da Suleiman Nabame ta tabbatar da wannan. 26/006/2017.
[8] .            Da Sarkin Kabi Muhammadun Sama (1920-1934) da Sarkin Musulmi Audu Ɗanyen Kasho (     
) duk rana ɗaya aka haife su.
[9] .            Sarkin Gobir Bawa ya gaya wa Nabame cewa,“Kana nan kana ƙoƙarin raya gidan wasu (Fulani)
ga naku gida can ya rushe, ƙasar kakaninka ta yamutse babu Sarki, ga su can suna yi wa Fulani bauta”. Daga lokacin jikinsa ya yi la’asar, ya nemi ya dawo gida. Hira da na yi da Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato, da Suleiman Nabame da Yakubu Bagaye (Masani tarihin  Sarautar Kabi) duk sun yi canjaras da wannan kalami, 26/06/2017 da 30/06/2017.
[10] .           Ana yi wa wannan tarihin tsagaita wuta da Fulani da Lafiyan Toga zamanin Sarki  Abdullahi
Toga (1963-1883) an yi Lafiyar Toga (1870-1878) Shekara 10 ana yaƙi.
[11] .           An ce, bayan da aka ci nahiyar da yaƙi kason da aka bai wa Kanta bai gamshe shi ba, bisa ga
irin famar da ya taka. Don haka ya yi wa Askiyya Muhammadu tawaye ya kafa ƙasarsa mai suna Kabi.
[12] .           A ƙarni na (16ƙn) Sarkin Musulmi na Maroko ya aiko wa Sarkin Kabi da wata wasiƙa ta
shawarwari. A wasiƙar an kira shi da suna Amiirul muminiina na Kabi. Wannan ya nuna daular Kabi ta riga ta Sakkwato karɓar Musulunci da kafa daular Musulunci. In babu ƙira me ya ci gawai?
[13] .           Kyangawa ƙarƙashin daular kabi suke, sun barbazu a Bunza da Kyangalwai da Kamba da Yelu
da Geshoru da Illo da Dukushi da Geza da Argungu da Kangiwa da Yeldu da Sauran manyan garuruwa da ƙauyukan Kabi da jamhuriyyar Nijar da Benin.
[14] .           Ya tattara ɗiyar sarauta suka tsayu a  babban gungun farfajiyar fadamar Kabi da ake yi wa suna
“Argungu” a yanzu. Wasu na ganin, daga yekuwarsa ta kiran danginsa Kabawa: “Ar! Ku zo nan gungu mu tsaya” ko “Ar! Ku zo mu yi gungu” aka samu suna “Argungu”. Akwai tatsuniyar cewa, wai haɗuwar da suka yi wuri ɗaya maƙiya suka hange su suka ce: “Ar! Sun yi gungu” wai daga nan aka samu “Argungu”. A nawa hasashe na ɗalibin al’ada, ina takin saƙa da su. Kalmar “Ar!” a Hausa kalma ce ta farga ko kuɓuta, kuma tana fita a fagen kirari. Gungu kuwa, in da tsibiri in kuwa taruwan jama’a mai jiran dako ko firgittu ko maɗauka fansa. Don haka, in dai ya kasance: “Arnan Gungu” waɗanda suka kafirce wa masu son su mallake su. Ko “Ar! Ga gungu” wato ga wurin da suke can; ko kuma ya kasance na “tsakar gungu in idan muka yi la’akari da tarihin cewa, Kabawan da suka zo Argungu sun tarar da garin “Buntsari”. Buntsari kuwa daga kifi sai naman ruwa ke yin sa a tsakiyar gurbi. Wato garin “Gungu” ne.
[15] .           Yaƙe-yaƙen kabi da Sakkwato ya haifar da karuruwan magana da tatsuniyoyi da tarihi da
tarihihi da wasan barkwanci da tashe da waƙe-waƙen yara maza da mata da waƙoƙin baka na manya kamar: Iyakar Kabi Sawwa; wurin da duk ka sha furar shinkafa nan ne Kabi gare ka;  ja ya faɗi ya ɗauke; dudduƙe har Kabi; da Kabi har Kabara karan gamba guda ne, ga su nan dai.


[16] .           Fitattun ayyuka su ne na Bello Alƙali da P.G Haris daga baya aka samu aikin PhD na Nasiru
Aminu, 2015.
[17] .           Buda ya yi waƙoƙi da yawa amma wannan kawai ce aka sani. Haka kuma, shi kansa Buda da ita
yake taƙama an ce duk lokacin da ya je waƙa in ba ita ya yi ba, ba ya tsima kowa. Da ya fara ta kyauta sai ya kau da kai.
[18] .           An ce, Sarkin Kabi cewa ya yi a sama masa “Fege” Kanawa ba su san “Fage” ba sai dai jeji/daji
ko karkara. Fage a Kabawa ana nufin babban wuri irin na noma shinkafa ko dandalin wasan dambe ko kokuwa yalwatacce. Aka fassara wa Sarkin Kano Shehu ya gane ya je wajen gari ya ba shi. Hira da Yakubu Bagaye Argungu 29/06/2017, gidan Sarkin Kabi Sama’ila Muhammadu Mera.
[19] .           Gobirawa da Kabawa abokan juna ne domin sai hali ya yi daidai ake abota, ‘yan kishin
ƙasashensu ne da ba su yarda da gurgusa in zauna ba, su dai biya ka wuce kamar kowa.
[20] .           Dambun masu ma’ana biyu ke gare shi: masun yaƙi a tarshe wani bisa wani tarshe ka ce damin
gero ko dawa, ana ce da shi dambun masu”. Akwai kifin da ake ce wa masu/harasu, mai ƙaya zargo-zargo in an yi miya ko dambun kifi yaro ba zai iya ci ba gudun ya laƙe masu ga maƙogoro.
[21] .           “Hausa” yana nufin Sakkwato da Ko’ina take riƙo a daularta. Fadar “Dac can” yana nufin
sauran ƙasashe masu ikon kansu irin su Gobir.
[22] .           “Mai wada yas so” wanda babu wani Sarki irinsa da zai tilasta shi ga abin da bai so ba,
Sarakunan ƙarƙashin mulkin Fulani sun rasa wannan. Idan sarkin Kabi ya faɗa babu wani Sarki a daular Kabi da zai faɗi akasinsa.
[23] .           An ce, a taron Sarkin Tambuwal babu sarkin da ya fi shi ‘yan busar sheshe ƙwararru. Asalin
sheshe kuwa Fulani Udawa masu kiyon tumaki zalla sun fi shahara da shi. Sheshen nan da ya burge ‘yan daba Buda ke son kushewa.
[24] .           Tattaunawa da Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato ta wayar hannu, a lambarsa
07034224741 ranar 26/6/2017 a ranar ina Gidan tarihin Kabi da ke garin Argungu.
[25] .           Motar ƙarama ce mai zurhi ciki, da ƙozo kamar kunkuru, ta yi kusa ga irin saƙar gidan ɓera
(kusa). Don haka aka kira ta “barayar kusa wurin hutawar ɓera cikin raminsa.
[26] .           Zunguru da duma ake yin sa, da shi mata ke sa lalle (ƙunshi). Yana da ɗan tsawo kamar shantu
ciki ake tura hannu a sa lalle. Hannu na ciki kamar kifi a cikin gora. Balli wani baƙin kifi ne mai rigima da karmanci irin na tafiyar karuwa. Kabawa na yi masa kirari da: Balli kamar kifi”.
[27] .           Ulu abin ƙawa ne ga mata a saka a wuya da kwankwaso a yi masu adandani launi daban-daban
da fari da ja da baƙi da algashi da shuɗi ga su nan dai. Dattijon banza shi ne Dandaudu ko cali na wasanni. Calin ‘yan dambe na sa ulu a kwankwaso ya yi rabaja. Ke nan da mata sai dottijon biri ke sa ulu.
[28] .           Kalmar “gaba” tsohuwar kalma ce, ma’anarta “yaƙi”. Asalinta rashin jituwa da juna da
hamayya da sa-in-sa da jayyaya da faɗi-in-faɗi.
[29] .           “Rarar ƙarhi” wato ƙarhin da ya yi gumuzu da garuruwan ƙasar Hausa da Zamfara da Ɓurmawa
bai ƙare ba. A wata fassara tana ɗaukar bai gaji ba
[30] .           “Karma” Kamar namiji mai kamar ‘yan mata da kasala irin ta ‘yan daudu.
[31] .       :Ranat Attanin na Yakubu yah hau
:Daga Sanyinna yak kwan
:Shagari ya’ aje yak kwana
:Ga Hausa tana kallo
:Tsamiya can uban Jibo yak kwana
:Ga Hausa tana kallo
:Ya kwan Tureta gagara ƙarya
:Ɓurmawa na kallo
:Murai can uban Jibo yak kwana
:Zamfara dut na kallo
:Bunguɗu can gadan-gadan yak kwana
:Zamfara duk na kallo
:Ga baƙon mutan Ƙwatarkwashi
:Sarki in don Allah ya so.
:Bahago ya zo Gusau da rarar ƙarhi
:Ba a koma haye mai ba.
:Nan yag game da Sarkin Ƙaura
:Yaw watce mutanenai
:Ni na so shi kwana Tcahe da yaz zo
:Sai yar raɓawatai
[32] .           Lokacin ana Surame tare da Nufawa ake. An ce, sun taɓa laifi har aka sa su yi yaɓin katangar
birnin Surame da man kaɗe. Dalili da haka, an share ƙarnuka da yawa kowace shekara idan zafin rana ya tsananta sai kufan ganuwar Surame ta nashe da masƙi. Bugu da ƙari, Nufawa abokan wasan Katsinawa ne, Kanta kuwa mahaifiyarsa Bakatsina ce. Bai kamata Nupe ta mara wa wata daula baya ba in ba Kabi ba.
[33] .           An ce, ƙoƙarin wannan sulhi shi ya haddasa aka ƙirƙiro bukin kamun kifi a Argungu. A dubi
Birnin Tudu, “Bukin kamun Kifi a ƙasar Argungu”, 1984, kundin BA.
[34] .           An yi artabu da Sarki Sama a wajen garin Sanyinna bayan ya dawo da kai Hari wajajen garin
Dono. A filin Fuloti na da, nan aka yi, gumuzun ɗebe takaici, kowanensu ya bar accakwama. An ce, shi ne yaƙi na ƙarshe da Sarki Sama ya yi a rayuwarsa.
[35] .           Idan aka dubi yadda tsarin sarautun daular ya koma bayan jihadi, babu shakka ƙabilanci da
tu’assubanci da ɓangaranci da zalunci ya yi katutu. Haƙiƙa, a kan haka ne Kabawa da Gobirawa suka ja daga cewa, kowa ya kare gidansu ganin abin ya koma yaƙi ba jihadi ba.
[36] .           Farfesa Ɗalhatu ya yi hira da Bango a Gobir da wani mai Molo a Argungu da suka rera waƙar
Buda sosai. Na amfana da ita duk da yake ban san shekarar da aka yi hirar ba. Ina godiya ga farfesa Magaji Tsoho Yakawada da ya nemo waƙar a Jami’ar ABU ya ba ni faifai na saurara.
[37] .       Na fahimci duk garin da na je, in na tambaye su abin da Buda ya ce a kan Sarkinsu, in mai muni
ne ba sa faɗa, sai su juya waƙar. Don haka, waƙar na buƙatar bincike na musamman a bi rariya-rariya a ƙasar Hausa a tattaro ɗiyanta a tace su. Misali wasu na cewa ya ce:
Jagora    : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
                : Runji shi ka wa yanke.
Haƙiƙanin gaskiya a ɗan bincikena ba haka abin yake ba cewa ya yi:
Jagora    : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
                : Sashenai na jimai
                : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza
                                :Tsoron Mamman yaj ji
[38] .           Da Buda Ɗantanoma ya je Argungu Muhammadu Sama ya sa aka ba shi Saulo (500) na gero,
Cukurfa (500) na shinkafa aka ba shi sarkawan da za su kai mai kifin miya da rundawan da zai kai masa mama. Ya ce, duk waɗannan ya baro su Yabo don haka shi jaruntaka da gwarzantaka ya biyo, soyayyarsa da Kabawa a zuci take.

No comments:

Post a Comment