Sunday, December 2, 2018

Hutawa Ka Alewa Man Gyaɗa Ka Tuyar Ƙosai (Barazanar Yanayi da Kutsowar Lokaci ga Al’adunmu)Bincike ya himmatu ga nazarin musabbabin abubuwan da ke haifar da al’adun mutane na tafiyar hawainiya, da koma baya, a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙn. 21). Babu wata al’umma ta duniya da yau za ta bugi ƙirjin cewa, al’adunta ba su shiga irin wannan hali ba. Don haka, na himmatu ga ƙasar Hausa da Hausawa da al’adunsu a muzanin sikelin ƙarni na ashirin da ɗaya. An yi awon nauyin al’adun a kan sikelin yanayi da cuɗanya da mulkin mallaka. A ƙarƙashin yanayi, an kalli irin rawar da yanayi ya taka, wadda ta fi ƙarfin ɗan Adam ya tunkare su. Yanayin ya haifar da lokaci, lokaci ya haifar da mutuwa. Waɗannan abubuwa sun yi wa al’adun mutanen duniya barazana, kuma ba za su daina ba. A fagen cuɗanya, an sa…
Hutawa Ka Alewa Man Gyaɗa Ka Tuyar Ƙosai
(Barazanar Yanayi da Kutsowar Lokaci ga Al’adunmu)

Aliyu Muhammadu Bunza,
Department of Nigerian Languages,
Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina
Tel: 0803 431 6508
Takarda da aka gabatar a matsayin jagora a taron ƙasa da ƙasa mai taken “Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa A Yau”, ƙarƙashin kulawar Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina da Hukumar Kulawa da Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina, ranar Talata 25 – 26, Yuni 2013, a babban Ɗakin Taron Tsangayar Fasaha, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.

Tsakure:
Bincike ya himmatu ga nazarin musabbabin abubuwan da ke haifar da al’adun mutane na tafiyar hawainiya, da koma baya, a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙn. 21). Babu wata al’umma ta duniya da yau za ta bugi ƙirjin cewa, al’adunta ba su shiga irin wannan hali ba. Don haka, na himmatu ga ƙasar Hausa da Hausawa da al’adunsu a muzanin sikelin ƙarni na ashirin da ɗaya. An yi awon nauyin al’adun a kan sikelin yanayi da cuɗanya da mulkin mallaka. A ƙarƙashin yanayi, an kalli irin rawar da yanayi ya taka, wadda ta fi ƙarfin ɗan Adam ya tunkare su. Yanayin ya haifar da lokaci, lokaci ya haifar da mutuwa. Waɗannan abubuwa sun yi wa al’adun mutanen duniya barazana, kuma ba za su daina ba. A fagen cuɗanya, an sa wa baƙin addinai da baƙin al’adu ido ta fuskar rawar da suka taka, suka rikiɗa al’adun da suka yi gaba-da-gaba da zamaninsu. Bayan an ɗan lugude su, aka sake bitar su a ƙarƙashin sakamakon barazanar da suka yi wa al’adun Bahaushe daki-daki. A ƙarshe, aka kakkaɓe nazarin da waiwayen ina aka kwana? Daga nan, aka fito da tantangayar Bahaushe, da al’adun da yake takaicin salwantarsu. Daga cikin al’adun, aka ciri ɗaya kacal ‘gaskiya’ aka yi garkuwa da ita domin a tabbatar da man gyaɗa ka tuyar ƙosai. Waɗannan kai da kawo suka taimaka wajen fito da sakamakon bincike guda shida, tare da shawarwari guda huɗu da ake kyautata zaton za su share hawayen da ke zuba a halin yanzu. An kakkaɓe wundin karatun laifin ɗaƙilewar al’adun Hausawa a wannan ƙarni, idan ɓera da sata ko daddawa da wari. Ya kyautu, idan an ga ta ɓarawo a dubi na mai kaya, ina ya ajiye su? Wa ya ba ajiya? Wannan ta sa muka ga laifin masu karatun Hausa da Malaman Hausa da Masana Hausa da Shehunan Hausa, da suka ƙi yi wa zakaransu kirari a fadar Agadas, don ganin ɗirka-ɗirkan raƙuma da wagar kanwa. A gaya wa ayarin raƙuma Hutawa ka alewa man gyaɗa ka tuyar ƙosai.

Gabatarwa:
Ga al’adar ɗan Adam, idan zama ya yi daɗi, sai ya shagala, ya himmatu da abubuwan da ke gabansa kawai. Cikin haka, za a shafa’a da zangon da aka ciwo (watau baya), a daƙile ga ƙyallaro abubuwan da aka fuskanta a gaba. Ɗan zaman da ake yi na sake jiki, da yi wa yau hidima, da mantawa da jiya, da yin ko oho da gobe, shi magabata ke cewa, “hutawa ka alewa.” Idan ‘yan dabarun da ake ciki na yau suka ba da ruwa, suka kasa warware matsalolin da ake ciki, suka dabirta akalar tunanin masu hankali da hangen nesa, daga nan, sai a shiga tunanin gara jiya da yau. A duk lokacin da wayon mai wayo ya kai ƙarshe, ya tabbatar da, da tsohon zuma ake magani, har ya fara tunanin gara jiya da yau, a nan ne magabata za su yi na ƙadangare su ce;[1] “man gyaɗa ka tuyan ƙosai.” Irin damar da aka samu aka saki jiki, aka ragaice, aka dambale, aka sukukuce, sai zuciya ta dasƙare irin na alewa. Lokacin da aka gano Borno gabas take. Aka haƙiƙance maɗi bai kai ga zuma ba. Aka lura da mugun gatarinka ya fi sari ka ba ni. Halin da aka shiga na gaba kura baya sayaki, ɗaka zufa[2] waje sanyi, gado kazunzumi[3], zane kuwa ƙyaya, ita ce wutar da za ta ƙona man gyaɗa ya toye ƙosai. Don haka, gabanin a dubi man gyaɗa mu fara duba alewa.

Tuna Baya:
Ban ga laifin gyartai ba, lokacin da ya ci sarauta ya ce, a bar tuna baya. Kuskuren da ya yi shi ne mantuwa da cewa, tafiya da waiwaya tana maganin mantuwa. Bugu da ƙari, Hausawa na ganin waiwaye adon tafiya ne. Idan za a ci gaba da sara ba tare da duban bakin gatari ba, za a yi bindigar ‘yan tauri, ke gawa, mai ke gawa, abin da anka nuna gawa, gawa uku jere ga juna. Haƙiƙa halin da muke ciki a yau, mun yi saki zari kama tozo, ka ce ba cikin fasahar kakanninmu aka ruwaito kamun gafiyar Ɓaiɗu ba.[4] Halin da duniyarmu take ciki yana buƙatar agajin gaggawa na masu al’ada, da adabi, da harshe, a fitar da suhe wuta. A  gaggauta kai na hannu gida, kana a dawo a kama na dawa. Irin halin da al’adun mutane mazauna duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya ke shiga, wasu ke ganin taɓarɓarewa ne, wasu na ganin, ciwon ajali ne, wasu na ganin wayewa ne, wasu na ganin ci gaba ne, wasu na cewa; lokacin abu a yi shi, wasu na ganin faɗan da ya fi ƙarfinka, ka mayar da shi wasa, ga su nan dai.[5]
        Wanda duk ya san jiya, ya san na dauri[6] ba ku da raggo, ai shi ya sa, idan na jiya suka ga ko suka ji abinda ke faruwa a yau, sai su ce: “Jiya ba yau ba”. A hangena, gurɓacewar yanayin duniyarmu, ya ribanci rayuwarmu, da al’adunmu, da siyasarmu, da tattalin arzikinmu, da zamantakewarmu. Idan za a yi gwari-gwarin tarihin al’ada, za a ga, babu wata al’umma a doron ƙasa da ba ta fuskantar matsaloli irin namu ko fiye da su ba. Idan abu ya zama ruwan dare, ba ta fuskar taɓarɓarewa za a linƙaye shi ba, domin abin da duk ya yi kora shi ke nuna hanya. Idan mun aminta da karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani, dole mu aminta da cewa, mai ɗaki shi ya san gefen da yake tarara. Duk da haka, ba za mu musanta mai baibaya ba, domin ya san wuraren da ya toshe matararar ruwa. A taƙaice, da dahuwa, da suya, da banda, duk gashi ya fi su sanin asirin wuta.

Mene Ne Al’ada:
Al’ada wani kandamemen fege ne da ya ƙunshi rayuwar ɗan Adam ta gaba ɗaya tun haihuwarsa har zuwa kabarinsa.[7] Daga cikin “al’ada” ne harshe ke yaɗo da haɓaka. [8] A cikin bunƙasar harshe, addinai ke bayyana.[9] Bazuwan addinai ke haifar da dokokin hani da horo.[10] Dokoki su ke tabbatar da kafuwar dauloli. Kyakkyawan tsaro ke tabbatar da dogewan daulolin da al’adun mazaunansu.[11] Kowace al’umma sai ta kai ga irin wannnan matsayi za ta haƙiƙance yanayin al’adunta ga barazanar lokacinta. Idan haka ne, ashe al’adu ba taɓarɓarewa suke yi ba, sai dai su yi fafitikar gwagwarmaya da zamaninsu da takwarorinsu da suka yi musu shigan kutse. A nan, za su kara a fage huɗu: in dai su kara wajen gwada tsawo ko faɗi,[12] ko su yi kokawa ta fuskar dacewa da wayewa.[13] Samun rinjaye ga ɗayan huɗun nan ke sa, wata al’ada ta yi masassara, ko gajeruwar suma, ko doguwar suma, ko ta ƙaura daga wannan zamani a aikace, ko da tana ƙunshe cikin taskar adabinsu.
        Masana al’ada a kan gado biyu suke feɗe al’adun mazauna duniyar mutane. Na farko shi ne: Al’adun Fasahar Hannu; na biyu Al’adun Fasahar Baka.[14] Waɗannan fasahohi suna tafiya da zamunan da mutanen da ke aikata su suke ciki. Sauye-sauyen da zamani ke haifarwa yana shafuwar al’adun kowane mutum da ke raye a zamanin. Don haka, al’adun mutanen duniya gaba ɗaya suna cikin haɗarin barazanar zamanin da suke ciki.[15] Ba wata al’adar da ke da mafita face an ɗauka mata ƙwaƙƙwaran matakai irin waɗanda za a ɗauka a yau. A irin wannan binciken, da mai bincike, da abin da ake bincike, da wurin da ake bincike, duk bincikensu ake yi.[16]
        A fagen nazari, ana tantance al’adar mutane da ganin su, ta fuskar suturarsu da ƙimar zatinsu.[17] Idan suka yi magana, harshensu zai tabbatar da sunan ƙabilarsu. Idan ƙasarsu aka fara gani gabanin a girshe su, tsarin gine-ginensu na mazauni da na ma’danar abincinsu wani babban hoton al’adunsu ne.[18] Idan aka zaune su, hulɗarsu da siyasar rayuwarsu, da zamantakewarsu da junansu, zai ƙara fassara al’adunsu ga wanda ya zaune su. Wasu al’ummomi ficen da suka yi na kirki ko rashin kirki, ko yaƙi ko zaman lafiya, ko tattalin arziki ko tsaro, kawai za a ji a yi kirdadon al’adun rayuwarsu. Ta kowace fuska na bayan fage zai karanci al’adun mutane ba za su tsallake gurabu biyu na gadon fiɗa da masana al’ada suka ayyana ba. Ya kyautu mu ƙyallaro taskokin da mutane ke adana al’adunsu gabanin mu fayyace abubuwan da ke shiga ciki su gurɓata su.

Ma’adanar Al’adu:
Babbar ma’ajiyar al’adun mutane ita ce, fasahar sana’o’insu kamar noma[19] da ƙira[20] da saƙa[21] da sassaƙa[22] da su[23] da fatauci[24] da makamantansu. Cikinsu za a tsinci kalmomin fannu da camfe-camfensu[25] da asirransu, da dangantakarsu da juna, da amon da suka yi ga masu aiwatar da su, da masu amfana da gallonsu.[26] Rumbun al’ada na biyu shi ne “adabi.”[27] Cikin fasahar harshen mutane za a tsinci falsafar rayuwarsu, da tarihinsu, da harshensu da addininsu da siyasar zamantakewarsu. Nau’o’in sarrafa harshen mutane ta fuskar karin magana[28] da salon magana[29] da baƙar magana[30] da shaguɓe da raha[31] da barkwanci[32] da kirari[33] da surƙulle[34] da tatsuniyoyi da wasanni[35] da waƙen-waƙen baka na manya da yara[36], su suka adana al’adun da muke laguda a yau, suka ba mu labarin waɗanda suka gabata da halin da suke ciki a yau. Duk wata matsala da ta shafi al’adu tilas a tuntuɓi waɗannan ma’adanai domin a ji, ina aka kwana?
Waɗannan ma’adanai ba su salwanta ba duk da irin gwagwarmayar da suka sha da zamuna barkatai. Ba don su ba, da ba mu san yadda magabata suka tafiyar da su ba, bale mu yi tunanin gane wuraren da muka yi sake aka yi mana sakiya. Dace da rashin salwantar su wata babbar nasara ce gare mu mai suna tsintuwar dami a kala, a Basakkwacen hasashe a ce, tsintuwar guru cikin suɗi.[37] Da mun yi rashin arziki suka salwanta, kai da kawon da za mu yi na neman su, sai ya fi irin na mai neman gidan Alhaji a birnin Kano jewaɗi.[38]

Musabbabin Gurɓatar Al’ada:
A wannan ƙarni da muke ciki, babu wata al’umma ta duniya da ba ta shiga cikin halin gara jiya da yau ba. Ƙasashen Turai al’adun Afirkawa da Larabawa da Asiyawa, sun yi wa nasu shigan kutse.[39] Ƙasashen Larabawa al’adun Turai da Asiyawa da Turkawa sun yi masu turnuƙu.[40] Nahiyar Afirka, al’adun yammatawa da gabastawa da Asiyawa sun hana nasu sake jiki.[41] Sinawa da Asiyawa, al’adun Turai da Larabawa da Afirkawa sun hana a rarrabe ɗan asali da ɗan haye (shige).[42] Zancen gurɓatar al’adun mazauna duniyar mutane a goshin ƙarni na ashirin ruwan dare ne game duniya domin abin ya kasance ko’ina ga koma (homa) ƙulli. A ma’aunin dandi mu ce, shege kowa ya yi. Ga ‘yan abubuwan da muke hasashen su suka haddasa shigen burtun da baƙin al’adu ke yi wa ‘yan gida suna yi musu dodorido.
i.                   Yayanyi
ii.                Cuɗanya
iii.             Mulkin mallaka
Ina kyautata zaton idan muka tsura wa waɗannan abubuwa idon nazarin ƙwaƙƙwafi, za mu tabbata ba mu muka kashe zomo ba rataya aka ba mu. Ga abin da nake hange:

i.             Yanayi:
A Bahaushen tunani, yanayi da zamani ‘ya’yan tsatso ɗaya ne.[43] A ganin Bahaushe, lokacin duniyar da ake ciki riga ne, saboda wannan imani yake cewa, lokacin abu a yi shi. A aƙidance yakan ce, Allah ne zamani ruwa ne kifi. Don haka, a tunaninsa kowa ya ƙi zamani ya ƙi Allah. Wannan zamanin da Bahaushe ke nufi, ya ƙunshi yanayin da duniyar zamanin ta haifar.[44] A ɗan bincikena, yanayi shi ne ma’auni na farko da za a duba domin a tantance halin da al’adun masu rayuwa ke shiga.
Abu na farko shi ne, ita kanta duniyar da Bahaushe yake ciki ya kasa yanayinta gida huɗu: Bazara, Hunturu, Rani da Damina. Cikin waɗannan fasula na shekara ake samun ruwa da fari da zafi da sanyi cikin ƙayyadaddun kwanaki da watannin da aka saba da su  yau da gobe.[45] A yau, bakin zare ya fara ɓacewa, kwanaki sun fara shiga junansu, tantance lokutan fasulan ya fara gagara. Kaifin rana da ake da shi a Bazara a da, ya ragu ainun a yau. Tsananin sanyin Hunturu da cuce-cuce da ke ƙunshe da su, a yau sun kau. Yanayin yawan ruwan damina ya ragu.[46] Wuraren da suka yi suna da abinci a da, a yau, sun fara zama Sahara sai ƙaurace musu ake yi.[47] Gulaben da suka yi fice, yau sun ƙafe wasu sun koma tabki.[48] Manyan itacen da ke yi wa dazukanmu sutura mun ƙone su, dabbobi da ke ɓoye ciki sun kau, mun rasa ‘ya’yan itacen da magungunan da itacen ke yi.[49] ‘Yan ƙananan namun da ke ciki da ƙwari mun cinye su, wasu ƙunar dawa ta halaka zuriyarsu sam ba a samunsu sai dai adabinmu ya ambace su. A nan kaɗai, idan za a tsettsefe al’adun da suka ginu cikin waɗannan abubuwa da yanayi ya gama da labarinsu, sun isa ga duk wani manazarci ko mai bincike ya yi bincike.
Musibar da ƙunar dawa/daji, da yanayi, bayan hasarar itacen kansu, an rasa ‘ya’yansu da abubuwan da ake sarrafawa da ‘ya’yansu ko sansaminsu ko saiwowinsu ko itacensu da al’adun da suka rataya gare su.[50] A fagen dabbobi, wasu labarinsu sai a tatsuniya ko karin magana.[51] Idan muka dubi tsuntsaye dole ajiyar zuciya. Wasu zuriyarsu sun ƙare, wasu sai a gidan zoo za a gan su ko a wasu sassan adabi.[52] Haka ƙwari suka shiga cikin wannan yanayi lokaci ya gama da al’adun da ke rataye da su.[53] Dabbobi na gida da daji ba a bar su a baya ba.[54] Yanayi ya ƙare wasu da abubuwan da al’ada ta tanada musu. Idan muka leƙa kogi da halittun da ke ciki abin ya fi na dabbobi musiba da muni.[55]
Bisa sauyin yanayinmu, wasu cutuka da ke yi wa rayuwa barazana sun kau tare da magungunan warkar da su.[56] Wasu baƙin cutukan da ba a sani ba, sun kutso kai dole a yi aron hannu ga magungunansu a ƙara wa wata al’ada lamba.[57] Abincin da ƙasarmu ta saba da shi ba shi ake shuka mata ba,[58] wanda ake shuka mata ya fito da sigar namu ba kaman namu ba,[59] al’adun da za a bi a sarrafa abincinsu tun a nan an sa su masassara, daga nan, sai shiga suma. A ƙarƙashin yanayi muna da abin da muke kira:

a.    Lokaci:
Faɗar lokacin abu a yi shi, ta yi kusan ta kau domin lokutn fasulan shekara saboda sassauyawan lokaci sai sun shige ba a ankara ba. Idan aka kula, ƙwari da tsuntsaye da ake samu a goshin damina da masu rayuwa a damina sun fara yi muna ban kwana.[60] Shekarun da yaro ke ɗauka ya balaga yau ba a haka suke ba ga mata da maza.[61] Itacen da ke share da shekaru gabanin su yi ‘ya’ya a ci, yau za a sa su yi ‘ya’ya sau biyu a shekara, abu kamar mafarki.[62] Dabbobi da tsuntsaye an sassauya musu lokutan ɗaukar ciki, da haihuwa, da nasa ƙwai, da ƙeƙyashe shi.[63] Halama kuna zaton abin da ya shafi sauye-sauyen rayuwarsu ba zai yi amo a al’adunmu ba? Yanayin duk da ya shafi fasulan shekara zai shafi al’adun wasannin motsa jiki na yara maza da mata da na manya da bukukuwan da suka ratayu da su.[64] Ashe idan za a ɗauko ta da tushe, yanayi ya fara taɓin al’adunmu, abin da ya biyo baya za mu ce, ko da iska ya zo ya tarar da kaba na rawa. Idan lokaci ya yi halinsa sai a shiga cikin wani babban ruƙuƙi da ake cewa:

b.   Mutuwa:
Ga nazarin yanayin da al’adu ke shiga a ƙarnukanmu ba al’adar ke mutuwa ba, masu ita ke mutuwa, sai al’adun su suma gabanin a samu wanda zai yayyafa musu ruwa. Mutuwar tsofaffi tana salwantar da fasahohin baka da yawa.[65] Gushewar manyan makaɗa da mawaƙa na haifar da rushewar ƙungiyoyin waƙoƙinsu a rasa masu gado.[66] Faɗuwar shahararrun mutane da suka yi fice a yaƙi da jaruntaka ko fitattu a sana’o’in hannu ko sarauta ko mulki da sauran baiwowi da ake samu ko ake gado masu su na mutuwa abubuwan na komawa da baya a rasa masu gado. Idan aka kasa duban halin da al’adunmu ke shiga sanadiyyar wannan fuska, sai mu ce, ba a yi komai ba, an raki baƙo ya dawo. A kowane mataki na rayuwar al’ada mutuwa na da abin cewa.

ii.           Cuɗanya:
Komai tsufan da al’ada ta yi ba a rasa tasirin cuɗanyarta da wata ba, ta kusa ba ko ta nesa. Al’ada kamar maganaɗiso take da ƙarfe, ba za a iya tantance lokacin da za ta yi wa wata al’ada barbara ba. Da yawa daga cikin al’adun da ke shiga cikin halin a mazaya a mayar da iri gida ta fuskar cuɗanyarta da wata ne abin ke wakana. A ƙarƙashin wannan fasali abubuwa biyu suka yi zara ga masu binciken al’ada:

a.    Kutsen Baƙin Al’adu:
Babu al’ummar da za ta rayu ita kaɗai ba tare da agaji ko ceton wata al’umma ba. Zamantakewa da hulɗa irin ta kasuwanci, maƙwabtakan gari da gari, ko ƙasa da ƙasa ko ma unguwa da unguwa, duk suna sa wasu su yi sha’awar wata al’ada ta wasu. In su aro ta su ƙara da tasu,[67] ko su aro ta su watsar da tasu,[68] ko su yi kirɓin gumbar makauniya su cakuɗa su kashi ya game gaba ɗaya.[69] Tufafin Bahaushe sun isa misali a nan.[70] Auratayya, zamantakewa, soyayya da zumunci sun taimaka ga kutsen baƙin al’adu nagari da miyagu a ƙasar Hausa.[71] Hulɗar Bahaushe da maƙwabtansa na kusa kamar Fulani, Barebari, Dakarkari, Yarbawa, da Ibo da Nufawa da Gwari da sauransu. Haka kuma, abokan hulɗarsa na nesa kamar Asante na Ghana da Wangarawa da Buzaye da Larabawa da Turawa da Indiyawa, sun haifar da salwantar wasu al’adu da yawa na Bahaushe da aron al’adunsu da yawa da suka kutsa cikin na Bahaushe.[72]

b.   Barazanar Baƙin Addinai:
Wasu masana na lisafa al’ada a matsayin addini saboda aƙidojin da ke tattare da ita.[73] A nan, abin da nake nufi da baƙon addini shi ne, duk wani saukakken addini daga Allah da ya yi takon saƙa da addinan gargajiya da al’umma ta gada kaka da kakanni. Saukakkin addinan da suka ziyarci ƙasar Hausa akwai addinin Nasara da na Musulunci.[74] Waɗannan addinai sun tarar da Hausawa a lokuta daban-daban, kuma sun yi naso sosai a tafarkin rayuwarsu. Addinan sun raunana babar aƙidar Bahaushe ta bautar Tsumburbura daga madugunta Barbushe.[75] Da haka Bori ya karaya,[76] aka karya lagon camfe-camfe,[77] da tsafe-tsafe,[78] da duk wata aƙida da ta yi takin saƙa da aƙidar sahihin saukakken addini.
Aƙidojin saukakkin addinai sun gurgunta daɗaɗɗiyar aƙidar Tsafi da rehu da duba.[79] Haka kuma, ayyukan da ke zubar da mutunci na rashin kunya da shaƙiyanci ba a ƙyale su ba. Sannu a hankali Bashirwanci[80] da Shawai[81] da Ɗankamanci[82] suka shiga takaba. Girmama wasu tsaunuka da bukukuwa da yanke-yanke da ake gudanarwa suka ci gaba da raunana.[83] Aƙidar addinin Musulunci ta hana tarayyyar Allah da wani, da tilasta yi wa Manzo (SAW) ɗa’a ga dukkanin abubuwn da ya umurta, ko ya hana, ta sa dole wasu al’adu su bar gidan Bahaushen da ya miƙa wuya.[84] Babu shakka, duk wanda ke son sanin makomar sana’o’inmu, da al’adunmu na gargajiya a yau, dole ya dubi addini da idon natsuwa sosai.

iii.         Mulkin mallaka:[85]
Daga cikin abubuwan da ke haddasa wata al’umma ta yunƙura ta mamaye wata, ita ce ƙiyayya. Ƙiyayya ita ta haifar da yaƙe-yaƙen da suka wakana ƙasar Hausa da yawa.[86] Ba za a mamayi mutane ba, sai an yaƙe su.[87] Ba za a yaƙe su ba, sai sun ƙi ba da kai bori ya hau.[88] Ba za su ba da kai bori ya hau ba sai an rinjaye su sun ga ƙwal uwar bori.[89] Duk al’ummar da ta ci nasarar rinjayar wata da yaƙi, za ta bautar da ita.[90] Cikin bauta akwai cilastawa ga yi wa ubangida biyayya da bin tafarkin da rayuwarsa sau-da-ƙafa.[91] Bawa ko da yana da wata kyakkyawar al’ada akan ƙyamace shi, da haka sannu wasu daga cikin al’adun Hausawa na cikin gida suka fara salwanta. Wanda aka mallaka ya zan na hannu ba ya da ‘yancin al’adunsa da addininsa, sai abin da maigida ya aminta.[92]
Ana tsakiyar fitinar cikin gida, masu jihadan ƙarni na goma sha takwas (ƙn. 18) suka kawo ɗauki ƙarƙashin jagorancin Malam Jibirila.[93] Da yunƙurin ya ci tura, Mujaddadi Ɗanfodiyo ya karɓi tutar a ƙarni na goma sha tara (ƙn. 19). Cin nasarar jihadi ya rusa daulolin ƙasar Hausa irin su Gobir da Kabi da Zamfara da Kano da Zazzau da Maraɗi da Katsina, sai daulolin suka koma ƙarƙashin masu jihadi.[94] Yaƙe-yaƙen da aka sha gwabzawa sun tarwatsa wasu al’adu da yawa. Mulkin da aka shimfiɗa ya kawar da salon tsarin siyasar ƙasar Hausa ta gargajiya, addini da Larabci da Fulatanci da Azbinanci suka cakuɗe wuri ɗaya suka yi wa Bahaushiyar al’ada barazana.[95]
Bayan da masu jihadi suka fara miƙe ƙafafunsu, ƙasar Hausa da al’adun Hausawa sun fara shiga kwandon tarihi sai ga ‘huntun ubangijin mai riga’.[96] Mulkin mallakan Turawa bugu biyu ya yi wa ƙasar Hausa. Na farko, mulkin da aka yi wa Arewacin Nijeriya, ya mamaye manya-manyan daulolin ƙasar Hausa na gida Nijeriya ta yanzu.[97] Na biyu, mulkin mallakan da Turawan Faranisi suka yi wa Faransa ya gurɓata al’adun Hausawan da ke nahiyarsu gaba ɗaya.[98] Ga alama, salon tsarin mulkin Faransa ya fi muni, don haka al’adun wajensu za su fi jin rauni sosai.[99] Mulkin mallaka shi ne, shimfiɗa wani tsari da masu mallakar ƙasar suka zo da shi, wanda zai rusa duk wani tsari da ke adawa da shi, ko wanda bai kama darajarsa ba. Da zarar an rusa wa jama’a tsarin tafiyar da siyasar shugabancinsu, an gina wa al’adunsu kabari, sai dai wanda kwanakinsa ba su ƙare ba.

Sakamakon Barazanar Yanayi:
A kimiyance, yanayi ya fi ƙarfin ɗan Adam, sai dai ‘yan dabarun kyautata shi. Wasannin da al’adu da falsafofi da zantukan hikiman da aka gina a kansu kawai suka rage. Zuwa gaba kaɗan ko su za su ce, in babu ƙira me ya ci gawai.[100] Ƙwari da tsuntsaye, irin su ƙwaron damina da Barkonon-tsohuwa da Ƙillu-balau da jan Kyashi da Daidaiya da Rozo-rozo da Ƙudahi da Dole-dole da Buzuzu da Ƙazaza da Shanshani sun fara yin ban kwana da mu. Fasahohin da suka ginu a kansu da mahaɗin da ake da su na magani da adabi sun fara salwanta.[101] Tsuntsaye irin su Suda da Angulu da Shamuwa da Buƙuƙuwa da Bilbilo da Dale da Buwa da Zarɓe da Jimina sauran da suka rage da wuya su tsallake wannan ƙarni a yanayin da muke ciki.[102] Salwantarsu ba hasarar nama kawai ce ba, ruɓushin zai shafi harshenmu da adabinmu da tarbiyarmu.
Yanayin ƙarancin ruwan sama, da na ƙasa, ba fari kawai zai haifar ba, wasu al’adunmu tare suke tafiya. Ƙarewar ruwa ya haifar da raguwar ƙwari masu fikafikai da na ƙasa masu jan ciki. Yau mu dubi Ani da Tsari da Ahihiya da Kunkuru da nau’o’in macizai irinsu Kasa da Jannasuru da Takwasara da Mulwa da dai sauransu.[103] Masunta na kukun salwantar kifi irin su Talibamban da Faliya da Gwando da Takasa da Yauni da Mijirya da makamantansu.[104] Dabbobi irin su Jaki mai zuriya goma sha biyu[105] da Alfadari da nau’o’in dawaki sai dai a ji su a adabin baka kawai.[106]
A ɓangaren lokaci, abubuwa da yawa sun fara nisa. Mu dubi tsage-tsagen gargajiya na fuskokin zuriyar Bahaushe daban-daban hatta da gidajen sarauta an daina yin su.[107] Lokaci ya yi kusa gamawa da maduganci fatauci da jakkai da farauta da makaman noma da yaƙi.[108] Wasannin ƙaddara irin su Shanci[109] da Gardanci[110] da Damben ƙarhe da Kokuwar ƙarhe, Allah Ya gafarta musu. Lokaci bai bar mu da bante da yaba da walki da jigida da mundayen mai binbila da takalmn ɗangarfa ba.[111]
Mutuwa na kallon lokaci, bayan ya gama nasa aiki ta biyo baya. A wannan zamani namu, ɗan shekara ɗari abin kallo ne da alfahari ga al’umma.[112] Wannan ya nuna gaba ta riga ta wuce, kuma abin da ta bari ba zai maye gurbinta ba, sai dai a ce, kama da wane, ba wane ba ne. A fagen shahara, da gwarzo ya gama zamaninsa maye gurbinsa ya gagara, ya bar giɓi da rata ga fagen shahararsa. Faɗuwar Shago ta yi wa sana’ar dambe giɓi babba, mutuwar Bawa Ɗan’anace ta sa shi dogon suma.[113] Da wucewar su Narambaɗa da takwarorin zamaninsa sarauta ta shiga halin ban tausayi a ma’aunin adabi.[114] Ƙaurar su Aƙilu Aliyu[115] da takwarorin zamaninsa ya sa rubutattun waƙoƙin Hausa wani kogin wasan kwaikwayo.[116] Idan muka dubi daulolinmu, za mu ga a Gobir, Bawa Jangwarzo ne zakara.[117] A Kabi, Kanta shi ne Giginya.[118]A Kano, Bagauda ne gidauniya.[119] A Katsina, Ɗanwaire da Katsi su ne rumfarta.[120] A Maraɗi, Tsagarana ne tauraro.[121] A kula, duk abin da ya rage bayansu ne, kuma baya abin zai dinga ci, koyaushe gara jiya da yau. Wannan karatun zai bayyana mana cewa, yanayi ya fara yi wa al’adunmu barazana, kuma zai ci gaba da yi, ta rage gare mu, mu san matakan da za mu ɗauka mu taƙaita barazanarsa, madalla da wannan mataki da muka fara ɗauka na gane daji ya fara cin wuta an huta an alewance, tilas a nemi man gyaɗa ga tuyar ƙosai.Sakamakon Cuɗanya:
Cuɗanya ta riga ta wakana, sakamakonta shi ne rikita tarihin al’adunnmu, da gurɓata fasahohinmu. A halin yanzu, suturar jikinmu gamin-gambiza ce. Abincinmu ya zama gama gari, da mu da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari abincimu ɗaya ne, idan ka yi yunƙurin gyara a ce maka baƙauye.[122] Mawaƙan zamaninmu muryarsu ta Indiyawa ce, ma’aunin waƙoƙinsu na Turawa, kayan kiɗansu na Larabawa da Turawa.[123] Don haka, fasaha da salon waƙoƙinsu sun kasa biya wa mai sauraro buƙata.[124] Harshenmu ko’ina ingausa ne. Bayan Larabci ya yi kaka gida, Turanci ya zo ya yi baba gida, ƙananan harsuna suka kutso ciki, sana’o’i da harkokin kasuwanci suka cike ragowar wushiryar. Kalmomin Hausa na asali suka fara shiga duhu.[125] Auratayyarmu ta hana a san Bahaushe tsintsa sai dai barbarar yanyawa.[126] Idan aka haɗa cuɗanya da yanayi, me ya rage ga sauran al’adunmu da ba a yi wa miki ba? A gai da waɗanda suka yi tunanin wannan haɗuwar domin mu fara gane ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba.


Sakamakon Mulkin Mallaka:
Ɗan abin da ya rage na rayuwar al’adunmu mulkin mallaka ya zo ya gama da su. Mulkin mallaka ya rusa sarautun manyan daulolinmu na Kabi da Gobir da Kano da Zazzau da Katsina da Maraɗi da Yawuri da ƙananan da ke ƙarƙashinsu. Sarauta da daula wasu manyan rumbuna ne na al’adun mutanen da ke ƙarƙashinsu.[127]
Idan kaya ya tashi me ya bar ganmo/ganwo? A cikin wannan rutsi aka yi awon gaba da tarbiyarmu ta ladabi da biyayya ga gabaci.[128] Haka kuma, aka rusa duk wata martaba, ko wata ɗaukaka, ko wata al’adar da ake ganin idan aka bar mu da ita, muna iya jan silalenta mu ‘yantar da kanmu.[129] Dubarun yaƙe-yaƙen da tsarinmu aka rusa su domin kada mu yi amfani da su mu ƙwato ‘yancinmu.[130] Aka kawo tsarin maƙiyanmu aka tilasta ga kanmu. Aka yi wa al’adunu fitsari aka kawo masu kashi aka ba mu, aka ce mu riƙe.[131] Yau da tura ta kai bango muke yunƙurin ina mafita take?Ina Aka Kwana?
A yau dai karatunmu ya kai walan waladaina wala malam na ƙiya, mun dangane allo. Mun ga dole uwar na ƙi. Kwalliyar da muka yi ta kasa biyan kuɗin sabulu. Ɗabi’un da muke ganin wayewa ne ƙauyancinsu ya fara bayyana. Abin da muke ganin ci gaba ne, ta bayyana ci gaban mai ginan rijiya ne.[132] Duk da haka muka daure muka ce, ana wata haka, in ji gwanin rawa da ya faɗi. Mun fahinci rashin ba mu damar sarrafa al’adunmu yadda ya dace da mu, shi ne sanadiyyar matsalolin da muke fuskanta. Dole cikin buƙatocinmu akwai na gaggawa akwai masu jiran lokaci. Yanzu muna son mu fuskanci na gaggawa mu magance haɓo kada jininmu ya tarare lokaci ya gama da mu. Yanzu dai mun tabbata hutawa ka alewa, to, mu nemo man gyaɗa a toya ƙasan wake. Ga yadda ya kamata a ce mu yi tuyar:

A Ji Bahaushe A Ga Bahaushe:
Ba Bahaushe kawai ba, kowane mutum na kowace ƙabila, ƙabilarsa na son a ji shi, a gan shi da wannan ƙabilar, ta fuskar bayyana al’adunsa. Yadda Bahaushe ke son a ji shi, shi ne a ji harshensa ta bakinsa da waƙoƙinsa da kukansa da dariyarsa da kuwwarsa[133] fasahohinsa na baka babu tangarɗa. Idan ya samu haka, an ji Bahaushe. Ta fuskar ganinsa kuwa, yana son suturarsa da ayyukan gaɓɓansa na sana’o’insa na gado da hikimomin da ke cikinsu bai rage komai ba. A wajen hulɗa za a ga mutum a san shi, a fahinci hankalinsa, da wayonsa, da basirarsa, da wautarsa, da gaskiyarsa, da ƙaryarsa. A al’adance, Bahaushe na son wanda duk ya ji shi, in ya gan shi ya ƙara yabawa. Don haka ne, Bahaushe ba ya son, jin ka ya fi ganin ka.[134]
Hulɗa da mutane ke bayyanar da nagartar al’adunsa. Cin da yanayi, da hulɗa, da mulkin mallaka, suka yi wa masana’antun gargajiya da harshe da addinan gargajiya, bai kai ga barazanar da suka yi wa zamantakewarmu da tarbiyarmu ba. Waɗannan abubuwa biyu, suna cikin zuciyar kowane mai kishin kansa, da al’adunsa, da ƙasarsa. Makomar tarbiyarmu, da zamantakewarmu, ita ce babbar musibar da ke tayar muna da hankali idan muka kalli yadda ake fito a taskokin adabinmu da fasahohinmu.[135]
A aƙidar al’adar Bahaushen asali abubuwa uku ke sa a more zaman duniyar mutane. Na farko ita ce “lafiya” don haka yake yi mata suna da uwar jiki, da jiki ya rasa ta, ya rasa komai, saboda haka ita abokiyar kowa ce, babu mai hushi da ita.[136] Na biyu shi ne “zaman lafiya”, a wajen Bahaushe ya fi zama ɗan sarki. Na uku, shi ne “girmama gabaci”, a kowane mataki na rayuwa, tattare da sanin ya san gaba da gabanta, yake da fahintar na gaba idon na baya. Yana ganin abin da babba (gabaci) ya hango da zaune, yaro ko ya daka tsalle ba zai hango shi ba. Waɗannan abubuwa su ne tubalan ginin Bahaushen mazauni har ya kai ga zama daula. A halin yanzu, wai ko suna nan yadda aka ruwaito su daga magabata? Ga alama, ganin masassarar da ta kama su ya sa maka yi tunanin wannan gagarumin taro.
Mataki na biyu, Bahaushe na da ma’auni goma sha huɗa da yake ganin dole Bahaushen asali ya siffantu da su. Ɗayansu duk aka rasa tarbiyarmu da zamantakewarmu za ta shiga wani hali. A ganin Bahaushe, hankali mudun awon mutum ne, don haka yake cewa hankali ka gani ba ido ba. Na biyu ita ce gaskiya, da an rasa ta an rasa mutuncin kazarkazar, domin cewa ya yi, gaskiya nagartar namiji. Kunya na biye, a koyaushe yakan ce, kunya muka tsoro mutuwa ta zan gado. Kamun kai dole ne ga Bahaushe domin mutunci madara ne in ya zube ba ya kwasuwa. Kirki ke tabbatar da abubuwan da suka gabata, saboda son kirki yake cewa, ana barin na zaune domin na tsaye. Zumunci maganaɗison ginin Bahaushe ne, domin cewa ya yi, sanin asali kan sa kura cin kanjilo.[137] Taimaka wa juna na daga ciki, domin hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. A kodayaushe a same shi mai haɗiye kwaɗai, sanin cewa, kwaɗayi mabuɗin wahala ne. Guje wa son kai tilas ne, ai don haka ake ganin laifin tsohuwa da ta aje mutuwa, aka tambaye ta, ta ce: “Ba don ni ba, don matan ɗan ga (wato matan ɗanta)”.[138] A gan shi tsaye wajen mora wa kai, domin ya ce, zomo ba ya kamuwa daga kwance. Ya zama fitaccen ɗan kishin ƙasarsa da mutanensa, a al’adance, babu mai nunin gidansu da hannun hagu. Wajen sadaukar da kai za a tantance Bahaushen asali, a koyaushe aƙidarsa ita ce, ba a wane bakin banza. Ya zamo mai hangen nesa, domin ya ce, shirin shiga ruwa tun tudu ake yin sa. Idan ya ci nasarar samun wayo shi ne ma’aunin rufe ma’aunin farko wata “hankali”, saboda duk abin da wayo ya ɓoye, hankali na gano shi. ai shi ne dalilin Abubakar Imam na faɗar, banza girman mahaukaci ƙaramin mai wayo ya fi shi.[139]
Waɗannan dalilai ke sa duk wanda ya yi hulɗa da Bahaushe zai buƙaci ya ƙara. Haka kuma, su ne Larabawa suka tarar Addinin Musulunci ya ji sauƙin shiga zukatan Hausawa. Su ne Turawan Faransa da Ingila suka tarar, har Turawan Ingila suka bar ƙasar Hausa a kan kulawan shugabancinsu. Su suka sa Gwamna Lugga ya yi muna yabon da ba a taɓa yi wa wata al’umma shi ba a Nijeriya.[140] Waɗannan ɗabi’u su ke sa a ko’ina muke a ba mu gabaci, domin da abinmu aka gan mu. Me ya same mu yau, bakin wuta na son ya mutu a hannunmu? Daga cikin waɗannan abubuwan, mu ɗauki ɗaya mu yi karan gwaji da shi mu jinjini nauyin a al’adunmu.Gaskiya[141]:
Gaskiya ita ce man gyaɗan da ke tuyar ƙosai. Dalilina na kawo ta a nan shi ne, komai ya rikice wa Bahaushe, ba ya cewa, a gwada ƙarya, sai dai a ce, a gwada gaskiya. Bugu da ƙari, duk abin da ya lalace a kan zargi ƙarya da cewa ita ce musabbabi, don haka Bahaushe ke cewa, gaskiya mai korar ƙarya. Hatta a fagen yaƙi, Bahaushe na  ganin, babu makamin da ya fi ta amfani saboda faɗarsa da ke cewa, gaskiya ka faɗa ba sanda ba. Duk abin da aka kai ƙarshensa aka ga ba mai kyau ba ne akan ce, ƙaryarsa ta ƙare, amma ba mu taɓa jin wanda aka ce gaskiyarsa ta ƙare ba. Kayan alatun ƙyalƙyal banza da suka rufe ruhin kayayyakinmu na gado da muka gano dasisar a yau, wannan taro namu ya tabbatar da ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya. Gaskiyar da ta yi ‘ya’yan ga su suna yi mata yaƙi. Ina ‘ya’yan ƙarya? Da za mu yarda mu koma ga gaskiyar al’adunmu na da, babu wata al’ummar da ba za ta yi ƙorafin ganinmu ba.
Mu riƙi sana’o’inmu da gaskiya. Da tsara su da gudanar da su gaskiya ta yi muna limanci. Mu mayar da ita cikin siyasarmu da addininmu da tattalin arzikinmu, mu gani in ba ta yi halinta na sa ƙarya gudu ba da duka ba. Cikin al’adunmu, babu abin da ya kai gaskiya tagomashi da suna da jan hankali da yarda da yaɗuwa cikin kowane sassan adabi da sana’o’inmu. Ita kaɗai ta isa ta mai do da duk wani abu da muka jin ya haddasa cikas a cikin al’adunmu a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya. A ganin Bahaushe, babu abin da gaskiya ba ta magani, don haka yake cewa, ciki da gaskiya wuƙa ba ta fasa shi. Shari’ar Ɗankama da Liman ta tabbatar da haka.[142] A zamanance, sabuwar tatsuniyar jaki da akuya da kare da mota sun tabbatar da gurbin gaskiya cikin al’adunmu.[143]

Sakamakon Nazari:
i.    Matsalar gurɓatar al’adun gargajiya a wannan ƙarni ruwan dare ne, game duniya, babu wata al’ummar da ke kirarin tsira.
ii. Dalilan da suka haddasa gurɓacewar wasu al’adunmu har yanzu suna nan ba su gushe ba. Tunanin yadda za a fuskance su dole ne tun ba a ƙara zurfafa ba.
iii.             Wasu al’adu dole a bari su tafi abinsu domin lokaci ba zai yi abota da su ba idan aka auna nauyinsu ga sikelin addini da tarbiyarmu da kiyon lafiya da tsaro.
iv.              Al’adunmu ba taɓarɓarewa suka yi ba, mu da ke da su muka taɓarɓare. Babu wata al’adar da za a ɗauko, a taras, ta sauya suna, ko ta rage tsawo ko faɗi. Suna nan taskace cikin adabinmu yadda suke a da, mu dai ne muka yi halin ko oho!
v.  Kowace al’umma ke son ceto jama’arta ga barazanar zamani da al’adunta na jiya za ta yi garkuwa domin jiya ta gina yau. Komai gaggawan gobe dole za ta bar yau ta wuce.
vi.              Idan za a yi tsayin daka a fuskanci komai da gaskiya, a yi shi da gaskiya, a yi kira zuwa gare shi da gaskiya, ‘yan al’adun da suka rage a yi musu shaƙen gaskiya sosai, to yau za ta koma jiya, sai jiya ta shugananci gobe, da abu ya yi.

Shawarwari:
i.    Manhajar koyar da yaranmu karatun boko ta ƙunshi al’adunmu gadan-gadan. Harkokin kimiyya da fasaha duk ya kasance da namu na gida ake misali kuma akan su ake koyarwa. Idan aka kammala karatu, da su za a jarraba ɗalibi a sakamakon karatunsa. Da haka Turawa suka ci mu da yaƙin ruwan sanyi, mu mayar da martani da ruwan ƙanƙara.
ii. Tilas a gaggauta taskace waƙoƙin baka na mawaƙan kowane fanni su zama wani diwanin da za a adana al’adunmu da harshenmu da ci gabanmu da fasahohinmu.[144] Wannan ita kaɗai ce makamin yaƙi da mutuwa da ke ɗauke gwarajenmu ba zata.
iii.             Hukumomin fasaha da al’adu su fito da gasar nuna al’adun gargajiya a kowace shekara domin a zaƙulo masu gajeruwa da doguwar suma a kuma ribanta da fasahohin gwarajen.[145]
iv.              Hukuma da masu hannu da shuni su fito da wata gidauniya ta musamman da za ta ɗauki nauyin masu bincike a kan al’adunmu da ke cikin haɗarin zamaninmu. Domin tabbatar da, da gaske ake, a fara wallafa takardun wannan taron. Da fatar Jagoran Katsinawa Sarkin Yaƙin Hausa ya sadu da wannan saƙo.

Naɗewa:
Hausawa na cewa, wanda ya san daɗin sure shi ke yi wa Fadama shinge. Idan dai mun yarda da abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa, to, dole kuwa wanda ya ci ladan kuturu ya tanadi askar yi masa aski. Mai biyar sawun maciji, macijin yake kwarare, to makaɗa Gambo ya ce in an gan shi, da wane dalili za a ci gaba da biyar shayinsa? Matuƙar an yi tangam! Mai zuwa Hajji ya  gamu da Annabi (SAW), to, wace nasara ta fi ana cikin gina ga wutsiya? Idan har yanayi da lokaci masu laifi ne ga koma bayan al’adunmu, to masu karatun Hausa su za su ɗauki ragowar laifin gaba ɗaya. Da wace hujja mutum zai ƙyamaci abin da ya karanto yana cin abinci da shi? Ɗalibai da manazarta da malamai da shehunan malamai da Hausa ta yaye, ta yi musu ƙafafum suka koma baya, suna ci mata dugadugai, ba tare da sun tsinana mata komai ba? Waɗannan mutanen, su ne annobar da ke yi wa Hausa da al’adunta barazana, tilas a yi musu zaman kansu na wankin ɗan kanoma mashaya, domin gudun zakaran ahu ya haɗiye taro, a yanka shi, ya kasa yin kwabo. A gai da makaɗa Gambo:
Jagora:       Halin duniya na ba ni tsoro,
          :Wai ka iske mutane ba su yin abu,
:In an motsa za a yin abu,
:Sai su hana domin mugunta,
:Kaicon na kaina!
:Mai rai wada Allah Ya aje shi!Manazarta:
Abdulra’uf, A. Kowace Ƙwarya da Abokiyar Ɓurmin ta, NNPC, Zaria.
Adamu, M. 1978. The Hausa Factor in West African History. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Adamu, S. 2011. “Gurbin Ƙwari a Magunguna Gargajiya na Hausa”, MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Ado, A. 2009. “Gardancin Hausawa Jiya da Yau”, MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ajayi, S. A. 2005. “African Culture and Ciɓilization”, Ibadan: Atlantic Books in Association with Ibadan Cultural Studies Group, Faculty of Arts, Uniɓersity of Ibadan.
Aliyu, M. S. 1980. “Shortcomings in Hausa Society as Seen by Representatiɓe Hausa – Islam Poets from ca 1950 to 1982”, unpublished MA thesis, Kano: Bayero Uniɓersity.
Amadi, R. 1981. “Administration and Deɓelopment of Culture: The Nigerian Eɗperience”, Nigeria Magazine, 137: 60, Lagos: Federal Deɓelopment of Culture.
Bada, B. D. 1995. A Literary Study of the Theme, Function and Poetic Deɓices of Hausa Karin Magana”, PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Bello, S. & Nasidi, Y. (ed) 1991. Culture Economy and National Deɓelopment. Proceedings of the National Seminar Eɓents of NAFEST ’89, published by the National Council for Arts & Culture, Lagos.
Bello, S. and Augi, A. 1993. Culture and the Book Industry in Nigeria. Published by National Council of Arts and Culture, Lagos.
Benedict, R. 1959. Patterns of Culture. New York: Mentor Books.
Bichi, A. Y. 1982. “Mene ne Camfi?” cikin Harsunan Nijeriya. Ɓol. ɗɓ, CSNL, Kano: Jami’ar Bayero.
Birniwa, H. A. 1987: “Conserɓatism and Dissent: A Comparatiɓe Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Ɓerse from ca 1946 to 1863”, PhD thesis, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto.
Bunza, A. M. 1990. “Hayaƙi Fid da na Kogo”, MA, Kano: Bayero Uniɓersity.
Bunza, A. M. 1995. “Magani A Rubuce”, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. 1997. “Turkubulli: Naƙalin Maza Muradin Mata”, cikin Studies in Humanities, Nigerian Journal of General Studies, ɓol. 4: 117 – 129.
Bunza, A. M. 2002. “Baƙar Magana a Al’adar Bahaushe, cikin The Beam, Journal of Arts and Science. 5: 2, 136 – 140.
Bunza, A. M. 2005. “The Place of Culture in National Deɓelopment”, paper presented at the First Conɓocation Ceremoney, Argungu: Adamu Augi College of Education.
Bunza, A. M. 2006. Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Ltd.
Bunza, A. M. 2006: Yaƙi da Rashin Tarbiya Cin Hanci Da Karɓar Rashawa, Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace. Lagos: IBRASH, Publishers.
Bunza, A. M. 2010. “Dariya a Bahaushen Ma’auni”, muƙala, Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
Bunza, A. M. 2011. “Al’adun Hausawa Jiya da Yau: Ci Gaba ko Lalacewa?” cikin KADA Journal of Liberal Arts, Kaduna: Faculty of Arts, Kaduna State Uniɓersity.
Bunza, A. M. 2012. “Gudu a Bahaushen Tunani”, muƙala, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Cain, P. J. and Hopkins, A. G. 1993. British Iperialism. London: Longman.
Crowder, M. 1968. West Africa Under Colonial Rule. Eɓanston: Northwestern Uniɓersity Press.
Dokaji, A. A. 1978, Kano Ta Dabo Ci Gari. Zariya: NNPC.
Ɗanfodiyo, S. U. (n.d.) Nurul Albabi.
Ɗanfodiyo, S. U. (n.d.) Wasiiƙatul Ikhwaani.
Ɗangambo, A. 1984. Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishers Ltd.
Eɓans, H. G. J. 1976. “Culture and Ciɓilization”, Inuagural Lectures 1975 – 1976, Ibadan: Uniɓersity of Ibadan.
Fagge, U. U. (n.d.) Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Ltd.
Fan, K. T. 1971. Readings in US Imperialism. Boston: Porter Sargent.
Farguson, D. E. 1973. “Nineteenth Century Hausaland, being a descrption by Imam Imoru of Land, Economy and Society of his people.” Unpublished PhD thesis, California: Unɓersity of California.
Furniss, G. 1996. Peotry, Prose and Popular Culture in Hausa. International African Library, London: Edingburgh Uniɓersity Press.
Gidley, C. G. B. 1967. “ ‘Yankamanci The Craft of Haua Comedians”, African Language Studies 11: 183 - 90
Greenberg, J. 1941. The Influence of Islam in Sudanese Religion. New York: J. J. Augustin Publishers.
Greene, R. 2007. The 33 Strategies of War. London: Profile Books Ltd. 3A Eɗmouth House Pine Street.
Gusau, G. U. 2012. Bukukuwan Hausawa. Gusau: Ol-Faith Publishers.
Gusau, S. M. 1988, Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-yanayensu a Ƙasar Sakkwato, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Hill, P. 1972. Rural Hausa: A Ɓillage and a Setting, Cambridge.
Idowu, E. B. 1973. African Traditional Religions: A Defination. London: Longmans Ltd.
Imasogie, O. 1985. African Traditonal Religion. Ibadan: Uniɓersity of Ibadan.
Jaggar, P. J. 1994, The Blacksmiths of Kano: A Study in Tradition, Innoɓation and Enterprenureship in the Twentieth Century. Cologne: Rudiger Koppe Ɓerlag.
Kalu, O. U. (ed) 1978. Readings in African Humanities African Cultural Deɓelopment. Enugu: Fourth Dimention Publishers.
Kalu, O. U. 1977. “Gods in Retreat: Models of Religious Change in Africa.” Nigerian Journal of the Humanities, I/ I.
Last, M. Sokoto Caliphate. Ibadan: Uniɓersity Press.
Maguet, J. 1971. Power and Society in Africa. New York: Mc Graw Hill Book Company.
Mair, L. 1969. New Nations. London: Weiden Feld and Nicolson.
Malumfashi, I. A. 2009. Adabin Abubukar Imam. Kaduna: Garkuwa Publishers.
Mani, A. 1966. Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria; NNPC.
Meddleton, J. 1970. Black Africa: Its People and their Customs Today. London: Macmillan Co.
Middleton, J. A. and Cohen, R. 1970. From Tribe to Nation in Africa. Seranton and Chandler Publishing Company.
Nasidi, Y. and Igoil, I. 1997. Culture and Democracy. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity, Press.
Newman, P. 1996. African Linguistics Bibliographies: Hausa and the Chadic Language Family. KOLN: Rudinger Koppe Ɓerlag.
Pachai, B. Fall of Sokoto, paper, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto, 1982
Philips, A. 1989. The Enigma of Colonialism: British Policy in West Africa. London: James Currey.
Rodney, W. 1973. How Europe Underdeɓeloped Africa. Bogle and L’Ouɓerture.
Sa’idu, B. 1978. “Gudumuwar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Salim, B. A. 1981 “Linguistics Borrowing as Eɗternal Eɓidence on Phonology: The Assimilation of Loan Words in Hausa”, PhD, York: Uniɓersity of York.
Sani, A. B. 2012. Trade Diplomacy, Banking and Finance in the Trans-Saharan Trade: An Interpretation of Ahmad Abu al-Ghaith’s Ledger, a Trade Consul in Katsina 1824 – 1870. Kaduna: Pyla-mark Publishers, Supported by TETFund.
Smaldone, J. P. Warefare in Sokoto Caliphate: Historical and Sociological Perspectiɓes. London: Cambridge.
Sokoto, A. A. 1983. “Malam Maikaturu da Waƙoƙinsa”, BA, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto.
Sudan, I. A. S. 2013. “Muhallin Magani a Adabin Bakan Bahaushe”, Sokoto: Ɗundaye Journal of Hausa Studies.
Sulaiman, A. H. 1990. “Tsagar Gargajiya a Ƙasar Hausa, Nazarin Ire-irensu da Muhimmancinsu Tare da Matsayinsu ga Al’ummar Hausawa, MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Sulaiman, I. 1987. The Islamic State and the Challenges of History – Ideals, Policies and Operation of the Sokoto Caliphate. London: Mansell Publishing Ltd.
Tylor, E. B. 1891. Primitiɓe Culture. London.
Umar, S. M. 2006. Islam and Colonialism Intellectual Responses of Muslims of Northern Nigeria to British Colonial Rule. Brill: Boston.
Upadhyay, Ɓ. S. and Pandey, G. 1997. History of Anthropological Thought. New Delhi: Concept Publishing Company.
Wamba, B. Y. 2012. “Dangantakar Ganye da Rayuwar Bahaushe”, MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Yahaya, I. Y. 1971/72, Tatsuniyoyi da Wasanni, juzu’i na 6, Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.


[1] Na ƙadangare shi ne ɗaga kan da ƙadangare ke yi sama da ƙasa. A faɗar Bahaushe, wai, cewa yake yi “haƙƙun gaskiya ne.” wai lokacin da Manzo (SAW) ya yi hijira zuwa Madina, da suka yada zango Kogon Hira, aka zo ana nemansu. Da Laɗihu Sarkin duba ya ce, suna cikin kogon Mushurukan Makka suka ƙaryata shi. Wai, akwai ƙadangare nan (kiski) ya dinga ɗaga kai sama da ƙasa yana tabbatar da zancen Laɗihu. An tsinci wannan a bakunan mata cikin Kitabul Hamdari nasu barkatai. Don ƙarin bayani kan ire-iren waɗannan ƙissoshi a dubi, Albasu, M. 1993, Kitabul Hamdari: Karatun Mai Kwanciya Tsakar Ɗaki, muƙala, Jami’ar Sakkwato. A cewar su, wai wannanne dalilin da ya sa yara ke yawo “kashe ƙadangaru”.
[2] A Sakkwato ake cewa “zufa” wato “gumi” ko “jiɓi”.
[3] Kazunzumi, ana nufin Kuɗin cizo.
[4] Kamun gafiyar Ɓaiɗu shi ne a ɓata goma ɗai ba ta gyaru ba. Ba a ga tsuntsu ba a ga tarko. An yi saki zari kama tozo kamar yadda muka samu kanmu ciki a yau.
[5] Masu ganin ci gaba ne ko wayewa, su suka fara gano kurensu a yau. Ina tare da masu ganin ci gaban mai ginan rijiya ne.
[6] “Dauri” shi ne, “da” ko “a da”.
[7] Masana cewa suka yi babu yadda mutum zai rayu wajen al’adunsa na gado. Don haka, komai na rayuwa a al’adance mutum ke tafiyar da su, ya sani ko bai sani ba?
[8] Harshe wani babban ginshiƙin al’ada ne, da nahawunsa da tasarifinsa da ma’anonin kalmominsa da furucinsu da yadda ake gininsu duk al’ada na da ta cewa a ciki. A cikin harshe ne za a samu karin harshe da harshen rukuni da kalmomin fannu duk al’ada ke jaye da akalarsu. Don ƙarin bayani a dubi: Salim, B. A. 1981 “Linguistics Borrowing as Eɗternal Eɓidence on Phonology: The Assimilation of Loan Words in Hausa”, PhD, York: Uniɓersity of York.
[9] Duk wani addini na duniya da harshe aka karɓo shi, da harshe za a bayar da shi, da harshe ake shigan sa da harshe ake fitan sa. Harshe shi ne babban ginshiƙi na gudanar da addini. Irin dabaibiyar da al’ada ta yi wa harshe shi ne dalilin cewa harshe ba ya rayuwa sai da al’ada. Nassin Ƙur’ani ya ambaci harshe a matsayin masinjan addini,
[10] Ma’anar addini shi ne, yarda da umurnin hani da horo. Bauta shi ne, yin ɗa’a a kan hani da horo. Don haka wasu ke ganin camfe-camfen Bahaushe da Bori daTsafe-tsafe duk a matsayin addinai. Don ƙarin bayani a dubi: Imasogie, O. 1985. African Traditonal Religion. Ibadan: Uniɓersity of Ibadan.
[11] Babban salon magabata na tsaro shi ne, a tanadi sojoji na ƙwarai da makamai da asirrai a yi wa gari ganuwa da ƙofofi da kahi. Don ƙarin bayani a kan wannan a dubi: Hill, P. 1972. Rural Hausa: A Ɓillage and a Setting, Cambridge.
[12] Tsawo a nan ina nufin dogewa da tsawon rayuwa. Faɗi kuma maimayar da za su yi wa zamaninsu.
[13] Dacewa, ana nufin dacewa da zamanin da ake ciki. Wayewa na nufin hawa matakan ci gaban zamani da ake ciki. Abin nufi a nan, ya zama ba su yi takin saƙa da kimiyyar zamaninmu ba.
[14] Don ƙarin bayani a dubi: Ajayi, S. A. 2005, “The Concept of Culture” in African Culture and Ciɓilization (ed.): 1 – 11, Ibadan Cultural Studies Group.
[15] Zamanin da muke ciki ya tattaro dukkanin abubuwan da za su sa a yi wa al’adu koran kare tattare da sanin cewa, falsafar al’ada ce ake faɗaɗawa a fito da waɗannan ci gaban da ake ɓaɓatu.
[16] Yanzu kashi ya riga ya game. Masu binciken su kansu ba su san al’adu na haƙiƙa ba, domin rubabi-rubabi suka tarar. Abin da ake bincike na al’ada ya riga ya gurɓata sai dai a yi aiki da abin da aka riska. Wuraren da ake bincike yanayi da lokaci ya cinye su, saura kaɗan ya haɗiye. Ala tilas masu bincike su yi taka-tsan-tsan.
[17] A tsarin halittun mutane ana iya rarrabe zuriyarsu ta ƙirar zatinsu. Hausawa matsakaita ne sosai, Yarbawa gajeru ne, Buzaye dogaye ne, mutanen Senegal tsayayyu ne santam-santam ga su nan dai. Wani masani al’ada mai suna Boas ya yi irin wannan bincike a kan ‘ya’yan ƙasar Sin (Japan) da aka haifa a Amerika, ya gano yanayin mazauni na iya shafuwar ‘ya’yan da za a haifa ko da bai shafi iyayensu da aka riga aka haifa wani wuri ba. A dubi, Upadhyay, Ɓ. S. da Pandey, G. 1997, History of Anthropological Thought, Delhi: India, shafi na 124.
[18] Idan za a tuna shi ne dalilin Bamaguje da ya shigo birni ya ga babu rumbu, babu masussuki, ya ce: “Ana zaman ƙarya.” Haka ko aka yi tun da sassafe ya ga motoci da babura da kekuna aguje, wasu a ƙafa ana sauri zuwa ofis, sai ya ce: “Na san ana haka”, Wai, ya san gudu a bar garin dole ne.
[19] Don ƙarin bayani a kan noma a dubi: Gusau, S. M. 1983, Waƙoƙin Noma na Baka: Yanaye-yanayensu da Jigoginsu Musamman a Sakkwato, juzu’i na 2, kundin digirin MA, Kano, Jami’ar Bayero.
[20] Don ƙarin bayani a kan sana’ar ƙira, a dubi: Jaggar, P. J. 1994, The Blacksmiths of Kano: A Study in Tradition, Innoɓation and Enterprenureship in the Twentieth Century, Cologne: Rudiger Koppe Ɓerlag.
[21] Ban sami labarin aikin babban digiri ko ɗaya ba a kan ‘saƙa’. Tun a nan an fara sumar da ita, ya zama dole a samu wani ya yi aiki a kan ta.
[22] Ga alama aikin ‘sakke’ sassaƙa babu wani aiki na babban digiri da aka yi a kan sa, shi ma ya kyautu a ɗan ce wani abu. Da haka ne, za su ɓata.
[23] A halin yanzu wani ɗalibi mai suna Musa Fadama yana aikin PhD a kan sana’ar Su, a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, akwai zaton ya kamala a wannan shekara, 2013.
[24] A ƙarƙashin nazarin Hausa babu wani bnincike na babban digiri da aka gabatar a kan ‘fatauci’. A nan ma, sai a sa himma a gani.
[25] Don ƙarin bayani a dubi: Bichi, A. 1987: Mene ne Camfi, Harsunan Nijeriya ɓol. ɗɓ
[26] Gallo kalma ce mai ma’anar ‘gajiya’. Asalinta ruwan rakka ne da ke tarara daga gare ta idan aka karya ta.
[27] Domin ƙara tantance ma’anar adabi da rabe-rabensa a dubi, Ɗangambo, A. 1984, Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Kano, Triumph.
[28] Don ƙarin bayani a kan karin magana a dubi, Bada, B. D. 1995. A Literary Study of the Theme, Function and Poetic Deɓices of Hausa Karin Magana”, PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
[29] Ba a yi aikin babban digiri a kansa ba.
[30] Ba a yi aikin babban digiri a kanta ba, sai dai an yi binciken da aka wallafa, a dubi, Bunza, A. M. 2002. “Baƙar Magana a Al’adar Bahaushe, cikin –The Beam, Journal of Arts and Science. 5: 2, 136 – 140.                                                                                       
[31] Ba a yi aikin bincike babba ba a kan ‘shaguɓe’ da ‘raha’ ba sai dai sakaɗe cikin wasu ayyuka kawai.
[32] Don faɗaɗa bayani a kan wasannin barkwanci a dubi, Abdulra’uf, A. Kowace Ƙwarya da Abokiyar Ɓurmin ta, NNPC, Zaria.
[33] Don faɗaɗa bayani a kan kirari a dubi,
[34] Don ƙarin bayani a kan surƙulle a dubi, Bunza, A. M. 1990. “Hayaƙi Fid da na Kogo”, MA, Kano: Bayero Uniɓersity.
[35] Don ƙarin bayani a kan tatsuniyoyin Hausa a dubi, Yahaya, I. Y. 1971/72, Tatsuniyoyi da Wasanni, juzu’i na 6, Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.
[36] Don neman ƙarin bayani a kan waƙoƙin baka a dubi, Gusau, S. M. 1988, Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-yanayensu a Ƙasar Sakkwato, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
[37] Guru a Sakkwato shi ne soyayye ko dafaffa go gasassar kaza ɗaya duka ko rabi duk yana iya zama guru. A Kano kuwa layu da dagumi ko karho shi ne guru.
[38] Ka ce an tura baƙo Maiduguri neman Babagana ko a Sakkwato neman Cika, ko a Tambuwal neman Zaki, aikin shekara da shekaru ya same shi.
[39] Tun hulɗar mummunar sana’ar nan ta cinikin bayi al’adun Turai suka yamutse. Yaƙin duniya na ɗaya da na biyu suka ƙara dagula musu tunani.
[40] Larabawa a wajensa wayewa ce zama Bature don haka fina-finan Turai suka bazu a gidajensu daga nan aka koma Turawa.
[41] Afirkawa sun ɗauki Turai sama ƙwarai sai da baya aka dawo da rakiyarsu. Tun a shekarar 1975 da fina-finan Indiyawa da Sinawa suka fara tashe a Nijeriya al’adunmu suka dagule.
[42] Su kuwa Turai suka aura sosai suka sake kakanninsu. Yanzu haka, ba su dawo da rakiyarsu ba.
[43] Duk da yake ana iya faɗaɗa su daban-daban amma kallo ɗaya aka fi yi musu. Yanayi ita ce Hausa tsintsa, zamani Larabci ne.
[44] In ta haifi zafi ko sanyi ko biji ko hazo ga su nan dai.
[45] Idan zamanin damina ne akwai Marka da Iwa da Fasa bangaye da Sarfa da dai sauranu. Kowane zamani da taurarinsa, kuma tauraron da wuya ya wuce kwanaki 14, don ƙarin bayani a dubi, Sa’id, B. 1977, “Ilmin Taurari a Waƙoƙin Masu Jihadi” cikin Harsunan Nijeriya, 7:75 – 92
[46] Wannan shi ke sa kowace damina ba a da tabbas gare ta. An ce, magabata sun ce, alamomin lokaci ya gabato ne, ana kusa ga a sallame mu. Allah Ya cece mu.
[47] A can da nahiyar ƙasashen Agades ba su san da fari ba. Goshin ƙarni na ashirin bala’in ya fara ziyartarsu har ya zuwa yau.
[48] Babu garin da za a tarar da tabkin da ya yi shekaru sama da ɗari biyu. Gulabe duk yashi ya fara rufe su, alamar tabbacin cewa za a yi hasarar kiyafun da ke rayuwa a ciki.
[49] Icen Kalgo da ake asirin zaga da shi da Tuna da ake maganin atini da Ƙaro da ake ƙara maza da shi da Kukkuki da ake haɗa guba sun fara raguwa.
[50] Duk wani ice da ake ci ba zai rasa magani da amfanoni da yawa ba, a dubi, Wamba, B. Y. 2012. “Dangantakar Ganye da Rayuwar Bahaushe”, MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
[51] Irin su Karkandai da Jimina da Cirza da Maƙaya da Gyado sun ragu sai dai a gidajen Zoo na hukuma.
[52] Yau ina Cilikko da ɗan Ragguwa da Lileji? Yanayi da zamani ya fara sa su kwandon tarihi.
[53] Don ƙarin bayani ƙwarai a dubi aikin Adamu, S. 2011. “Gurbin Ƙwari a Magunguna Gargajiya na Hausa”, MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
[54] Don ƙarin bayani a dubi aikin, Kudan, M. 2013. “Dabbobi a Tunanin Bahaushe”, Takardar ƙudurin binciken PhD, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
[55] Aikin da na ambata na Musa Fadama a lamba ta 23
[56] A yau sai dai a ji zancen, Tunjere da ‘Yan birni da Ƙyanda da Kurkunu da Hangun da Ƙazuwa ga su nan dai. Magungunansu dole su ɓace domin kaya ya tashi me ya bar ganwo?
[57] A kasuwanninmu da dandali da ma’aikata da asibitoci magungunan Sinawa na son su gargaɗi namu musamman magungunan da suka shafi hulɗa da iyali, turƙubulli ko bi-ta-zai-zai. A dubi, Bunza, A. M. 1997. “Turkubulli: Naƙalin Maza Muradin Mata”, cikin Studies in Humanities, Nigerian Journal of General Studies, ɓol. 4: 117 – 129.
[58] Masarar da muka sani da dawar da muka sani da shinkafa da gero yau duk baƙin ƙasarmu ne, masu sababbin lokaci da yanayin nina daban da namu.
[59] Lalurar da ta shafi abincinmu ta shafi lafiyarmu, abin da ya shafi lafiyarmu, ya shafi al’adunmu.
[60] Shamuwa yau ba ita ce alamun damina ba. Dale ko gero ya nuna ba a ganin ta. Ƙwaron damina ja da ke fita a farkon damina yau yana batun ƙarewa.
[61] Wasu masana falsafa sun ce, yanayin abincinmu ne da muke takure wa tsawon lokacin da ya kamata ya ɗauka shi ya sa shekarunmu na takura. Da shekaru goma sha bakwai gemu ya fito wa yaro, ‘yar shekara goma nono na batun faɗuwa ga su nan dai.
[62] Abin da duk ya haifar da wannan dole ɗanɗanonsu da nagartarsu da amfaninsu ga jiki ya ragu. Ai wannan shi ne ya sa a yanzu cutuka suka fi yawaita.
[63] Kusan in ce yau, Shan Kabewa da Buɗar Dawa ko akwai wuraren da ake yin su ba kusa ba. Magabata sun tafi da abin su.
[64] Domin abubuwan da suka sani ba a rubuce aka sanar da su ba. Suna nan a ka kamar yadda aka ba su. In tsufa ya yawaita kan ya buga su salwance. In sun mutu a yi marus.
[65] Misali babba, yau babu kufan makaɗa Narambaɗa da na yaransa. Haka ma Ɗan’anace. Maganar Kurna haka take, bale Ɗandodo Alu mai taushi.
[66] Kamar yadda muka aro suturorinmu.
[67] Kamar yadda muka yi watsi da makaman noma da yaƙe-yaƙe.
[68] Kamar yadda yake faruwa ga fina-finan Hausa da ƙungiyoyin mawaƙan zamani.
[69] A yau Bahaushe ba a raga masa komai da ya gada na tufafinsa na gargajiya ba.
[70] Biranenmu duk sun shiga irin wannan hali.
[71] Don ƙarin bayanin are-aren kalmomi a dubi, Ibrahim, M. S. 1984. Are-aren Kalmomi cikin Hausa,
[72] Don ƙarin bayani a dubi; Adamu, M. 1978. The Hausa Factor in West African History. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
[73] A cikin littafan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Sardul Kalaam fii ma jaraa bainii wa baina Abdus Salaam, ya yi li’irabin sunan Abdus Salam sosai, wanda ya nuna akwai ƙanshin addinin Bani Isra’ila tun gabanin bayyanar Musulunci a ƙasar Hausa.
[74] Don ƙarin bayani a dubi, Dokaci, A. A. 1978, Kano Ta Dabo Ci Gari. Zariya: NNPC, Malam Sulaiman Ɗunɗaye mawaƙin PRP ya taɓa yi wa wani Gwannan siyasa na Kano habaici cikin waƙarsa ta ‘Yan Tsantsi kun zama yawa, yana cewa:
Jagora:           Tafi gindin Dala ka bushe,
                        Wai kai jikan Barbushe,
                        Tsumburbura ma ta bushe,
                                    Balle wani mai bautarta.
Amshi:           ‘Yan santsi kun zama yawa,
                        Da ma ba ma ƙaunar ku,
                        Mu mun koma NPN
[75] Domin samun cikakken bayanin Bori a dubi, Greenberg, J. 1941, Influence of Islam On a Sudanese Religion. New York, J. J. Publishers.
[76] A dubi takardar da munka ambata a lamba ta 25.
[77] A dubi littafin Lemu, S. A. Asirin Tsafi, Zariya, NNPC.
[78] Don ƙarin bayani a dubi, Bunza, A. M. 1995, Magani A Rubuce, kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
[79] Rehu shi ne caca. Duba, gano abin da zai faru gaba, Allah kaɗai ke da wannan ilimi. Wanda ya yi tarayya da shi ya kafirta.
[80] Bashirwanci shi ne mai wasa zawo a kasuwa.
[81] Shawai shi ne mai zagin iyayensa da yi musu ashar a kasuwa.
[82] Ɗankamanci a dubi, Gidley, C. G. B. 1967, “Yankamanci The Craft of Hausa Comedians, African Language Studies 11: 183 – 90.
[83] Domin kauce wa ƙa’idar “ridda” da “zindiƙanci” dole a gudani tsafi da shirka ɗari bisa ɗari.
[84] Mujaddadi Ɗanfodiyo ya yi nuni da haka a cikin Nurul Albabi, da Wasiƙatul Ikhwaani.
[85] Domin cikakken bayanin mulkin mallaka a dubi, Crowder, M. 1968. West Africa Under Colonial Rule. Eɓanston: Northwestern Uniɓersity Press; da Cain, P. J. and Hopkins, A. G. 1993. British Iperialism. London: Longman; da Umar, S. M. 2006. Islam and Colonialism Intellectual Responses of Muslims of Northern Nigeria to British Colonial Rule. Brill: Boston; da Philips, A. 1989. The Enigma of Colonialism: British Policy in West Africa. London: James Currey.
[86] Bayanin yaƙe-yaƙen ƙasashen Hausa suna a cikin, Smaldone, J. P. Warefare in Sokoto Caliphate: Historical and Sociological Perspectiɓes. London: Cambridge.
[87] Don haka Turawan mulkin mallaka a duk ƙasar da suka shiga, sai sun fara da ta’addancin yaƙi gabanin shimfiɗa mulkinsu. Yaƙin Satiru 1906, da Ningi da Haɗeja sun isa su zama misali. Don samun cikakken bayani dubi, Mani, A. 1966. Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria; NNPC.
[88] Haka ya faru a daular Sakkwato. Don cikakken bayani a dubi, Pachai, B. Fall of Sokoto, paper, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto, 1982; da Last, M. Sokoto Caliphate. Ibadan: Uniɓersity Press.
[89] Duk ƙasashen da Turawa suka shimfiɗa mulkinsu da ƙarfin makamai da yaudara suka ci masarautun da talakawansu.
[90] Asalin bauta a ƙasar Hausa ita ce wanda aka kai wa hari aka yi galaba a kansa ya zama bawa. Duk da yake mun san akwai hanyoyin gargajiya da yawa na mallakar bayi.
[91] Ai shi ne dalilin da ya sa Turawan Faransi suka fito da tsarinsu wai shi Assimilado (Assimilation). Wai a mayar da kai Bafaranse a jiƙa da aƙida, domin ka riga ka zama bawa.
[92] Asali Durugu da Abbega, yaran da suka fara rubutun Hausa a duniya Musulmai ne. Da aka kai su Jamus bauta tun suna ‘yan shekaru 10 – 15 aka kiristantar da su. Da Abbega ya dawo Lokoja yana ɗan shekara 70 – 75 a shekarar 1912 ya Musulunta ya ci gaba da limanci, a dubi; et – l’Afriƙue, H. B.  2006. Koln: Rudiger Koppe, Ɓerlag, shafi na 130.
[93] Malam Jibirila shi ya fara yin yunƙurin jihadi ƙasar Hausa. Da Allah bai ba shi nasara ba, Mujaddadi Ɗanfodiyo ya biyo baya ya yi, ya ci nasara a ƙarni na goma sha tara (ƙn. 19).
[94] Masu jihadi suka dinga aika wakilansu suna sarauta a ƙasashen da aka ci. Wannan shi ne tushen sarautu irin su Sarkin Yamma, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, Sarkin Arewa, Sarkin Gobir na Isa, Sarkin Gobir na Gwadabawa da dai sauransu.
[95] Dukkanin waɗannan harsuna ana samun nasonsu a harshen Hausa sosai. Masu jihadi sun yi rubuce-rubucen waƙoƙi da ajamin harsunan sosai. Don ƙarin bayani a dubi, Sokoto, A. A. 1983. “Malam Maikaturu da Waƙoƙinsa”, BA, Sokoto: Uniɓersity of Sokoto.
[96] Bature shi ne huntu ubangijin mai riga.
[97] A dubi, Mani, A. 1966. Zuwan Turawa A Nijeriya Ta Arewa. Zaria: NNPC.
[98] Har yanzu Hausawan da ke zaune ƙasar Faransa ɗabi’unsu da harshensu da tarbiyarsu ba irin ta Hausawan Ingilishi ba ce.
[99] A Faransi, Hausawa kowa shi kaɗai yake zama a ƙofar gida da rediyonsa wai shi Bafaranshe. Wannan ɗabi’ar ta Turawan Faransa ce.
[100] A halin yanzu a birane wasannin kamar babu su. Haka za su dinga tararewa har a lalube su a rasa.
[101] Mafi yawan itace da tsirran magani suna da kirari ko karin magana nasu na kansu. Za ka ji “Aduwa” a ce, addu’ar ma’aikin Allah. ‘Tuna’ a ce, tuna itace. ‘Hano’ a ce, Hano hana zamba. Ga su nan dai.
[102] Barazanar magungunan Sinawa da na Dakarkari da Buzaye da wuya ya bar su.
[103] Macizan sai dai ga gardawa ko a gidan zoo.
[104] Talibamban da shi yara ke turu. Faliyo faɗi gare ta kamar faifai. Mijirya jan jini take yi kamar wutar lantarki. Ma Mijirya ake haɗa maganin Sagau/Ƙago.
[105] Nau’o’in jakkai kamar yadda Maitandu ya ruwaito su akwai: Goho da Maziki da Jangora da Kwaki da Magoshi da Tantabar da Akaza da Ɗanbuhar da Fari da Duna da Ukar da sauransu.
[106] Daga cikin nau’o’in dawaki akwai; Akayara da Gunya da Juru da Akawal da Hurde da Bidi da Alshan da Danda Fari biyat, da dai sauransu.
[107] Dukkanin zuriyar Bahaushe da tsage-tsagen su na gargajiya ake rarrabe su. A yau duk wani basaraken da bai haura shekaru 60 ba da wuya a tarar da shi da tsagar gidansu. A dubi; Sulaiman, A. H. 1990. “Tsagar Gargajiya a Ƙasar Hausa, Nazarin Ire-irensu da Muhimmancinsu Tare da Matsayinsu ga Al’ummar Hausawa, MA, Kano: Jami’ar Bayero.
[108] A da Madugan Zamfara Katsina suke zuwa, na Sakkwato Bidda, na Kabi Zabarma, na Katsina su yi Kabi. A yau, sai dai labari. Karnukan farauta sun ƙaranta. Manoman asali da ake kira Aranan Gona yau sai dai a garuruwan Maguzawa in akwai.
[109] Shanci, an ce sara jiki ake yi a cire hannu da hanci da kunne da sauransu. An ce, ana yin sa a Bichi da wasu garuruwan Kano. Ni ban shaida ba, kuma ina ganin akwai ayar tambaya a ciki.
[110] Ƙarin bayanin ‘gardanci’ a dubi, Ado, A. 2009. “Gardancin Hausawa Jiya da Yau”, MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[111] Mundayen sun ɗan makara ga Fulanin daji wajajen shekarun 1960, amma da samun ‘yancin kai suka fara barin ƙasar Hausa.
[112] A yanzu su ake nuna wa a jaridu ana ƙalubale. Na yi hira da ɗan shekara ɗari da talatin da wani abu mai suna Umaru Kundila Gardi cikin ƙasar Raha ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bunza. Wasu na ganin ya rasu da shekaru ɗari da arba’in, bai ruɗe ba kuma bai naƙasa ba.
[113] Yanzu duk yaransa sun mutu.
[114] Yau a ce wai, ‘yan mata ke yi wa sarakai waƙa da bujadala da tamburan Coci. Mu je zuwa dai, lokaci bai bar kowa ba.
[115] Aƙilu Aliyu da Yusuf Kantu da Shekara Sa’adu da Mudi Sipiki da Aliyu Namangi duk zamani ɗaya suka rayu kuma suka ƙaura.
[116] Sabon salon rera rubutattun waƙoƙi a yau da kiɗa da amshi da ‘yan mata.
[117] Tun wucewar Bawa sai dai a yi kama.
[118]  Yanzu haka Sarkin Kabin Argungu an mayar da shi Kanta domin tuni da gwarzonsu.
[119] Yau a Kano da wuya a samu mai suna Bagauda, duk da sanin cewa, shi ya sara Kano tana dajinta sannan babu kowa. A dubi waƙar Bagauda.
[120] Ɗanwaire sai dai jikoki, Katsi kuwa sai labari.
[121] Tsagarana biyu aka yi Maraɗi. Ɗankulodo da ya buwaya jikan su ne.
[122] A haɗa shinkafa da ganye da ‘ya’yan itace da hakukuwa da nama da ƙwai wuri ɗaya don kiyon lafiya. A da, da ka ba mutum ai ba zai ci ba, tsoron in ba jifar sa kake son ka yi ba.
[123] Waƙoƙin fina-finan Hausa, mafi yawa da muryoyin waƙoƙin Indiyawa aka gina su.
[124] Domin wani lokaci sai an kasa kunne sosai za a ji Hausar da suke yi, duk muryar Indiya ta juye Hausar.
[125] Domin kalmomin da suke aro na Turanci ne da Indiyanci da sauran harsunan Asiya.
[126] Yau samun Bahaushe gaba da baya, kaka da kakanni, a jera su biyar zuwa goma, abu ne mai wuya ainun.
[127] A can da, gidajen sarauta su ne rumbun adana al’adun mutanen daularsu. Da Turawa suka zo, suka ƙona wasu, suka sace wasu, suka ɓoye wasu. Suka yi wa saura furjin kyanwa.
[128] Wannan shi yake tayar wa duk wani mutumin kirki hankali.
[129] Duk wani aiki da zai amfane mu sai a sa doka a harantar da aikata shi.
[130] Har Turawa suka gudu, ba su bari wata ƙasa ta ƙera bindiga da kanta ba.
[131] Dokokin ƙasar Turai ai kashi ne idan aka dubi dokokin da suka tarar da Nijeriya ta Arewa da su.
[132] Ai bayan an yi nisa da mu, muka waigo duk da ganin zangon mai tsawo ne,muna son a koma mayar da hannun agogo baya mu gaji kakanninmu.
[133] Don ƙarin bayani a kan kuka da dariya da gudun Bahaushe a dubi; Bunza, A. M. 2012. “Gudu a Bahaushen Tunani”, muƙala, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
[134] Idan ana labarin ƙwazon mutum, Bahaushe ya gan shi gajere, ko kyarce, ko wada, zai ce; jin ka ya fi ganin ka ne.
[135] Dubi zancen, ‘ɗa na barin halas don kunya’ yau tana aiki a ƙasar Hausa? Dubi batun, ‘bin na gaba bin Allah’, da ‘na gaba idon na baya’, da ‘babba ba ya amai ya lashe’, da ‘dottijo ba ya batu biyu’, ai a yau sai dai idan an je a makaranta a koyar da ɗalibai.
[136] Waƙar Ɗangiwa ta tabbatar da haka domin cewa ya yi:
Jagora: Lafiya uwar jiki
            :Babu mai hushi da ke
Gindi: Na taho in gaishe ki
            :Lafiya uwar jiki
            :Babu mai hushi da ke
[137] Kanjilo shi ne busasshen kashin shanu da aka ƙona. Sanin asalin wurin da ya fito shi ya sa kura ta bi shi da ci.
[138] Me ya sa ba ta ce, don ɗanta ba, ko don jikokinta? A al’ada, matan ɗa suna kishi da surukansu. Ita kuwa don son kai da kishi ta aje mutuwa domin matan ɗanta. Assha!
[139] A cikin Magana Jari Ce, aka kawo ƙissar, fitaccen aiki a nan shi ne; Malumfashi, I. A. 2009. Adabin Abubukar Imam. Kaduma Garkuwa Publishers.
[140] Ya tabbatar da babu al’ummar da ta kai mu gaskiya a Afirka. Kuma ya ce, mace na ɗauko zinari daga Sakkwato har ta kai Bida ba tare da samun wani ya tare ta da sunan sata ko fashi ko fyaɗe ba. Tirƙashi! Me ya fi haka ga ɗa a duniya?
[141] An yi aiki na musamman a kan ta, a dubi, Safana, “Gurbin Gaskiya cikin Adabin Hausa”, MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[142] Ɗankama ya lura da duk liman ya zo sayen haki sai ya jinjina ya ji mai nauyi ya saya. Da ya kawo hakinsa sai ya sa babban dutse ciki ya ɗaure. Da Liman ya jinjina ya ji nauyi, ya ce: “Danƙari! Ɗankama abu kamar dutse?” Ɗankama ya ce: “Dutsen dai ne Liman”. Liman ya saya ya biya ya je gida ya kwance ya ga dutse, nan take ya juyo ya tarar da Ɗankama ya ce: “Yaya aka yi haka?” Ɗankama ya ce: “Haba! Liman ai da ka ce:” ‘Abu kamar dutse?’ Kowa ya ji na mai da jawabi na ce: “Dutsen dai ne Liman”. Liman ya shaidi gaskiya ta ci shi, ya sa kai ya bar Ɗankama da kuɗin haki dole.
[143] Wai sun ce: Dalilin da ya sa idan kare ya ga mota ya bi ta aguje, kuɗinsa ya biya ba a ba shi canji ba, don haka gaskiya gare shi. Ita kuwa akuya abin da ya sa take rugawa, ba ta biya kuɗin mota ba, rashin gaskiya gare ta. Jaki kuwa abin da ya sa ba ya kauce wa mota, kuɗinsa ya biya. Gaskiya gare shi dole a ɗauke shi ko a ba shi jallinsa.
[144] Madalla! Da namijin ƙwazon Farfesa Sa’idu Muhammadu Gusau da Malm Ibrahim Sheme, idan an bi rawarsu an warkar da wannan miki
[145] Ban rena da ƙwazon Hukumar Al’adu ta Tarayya take yi ba na bukin NAFEST shekara-shekara. Idan aka ƙara matsawa za a kai ga nasara.

No comments:

Post a Comment