Monday, December 3, 2018

Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa Gaskiya
Sassan adabinmu na baka ba ƙaramar rawa suka taka ba wajen daidaita muna akalar rayuwa a kowane ƙarni muka samu kanmu. Lallai, ba don jiya ba, da yau ta yi masassara. Yunƙurin kyautata rayuwar yau kuwa, gobe ce ake yi wa shimfiɗar maraba. Sarrafa karin maganar “Sabo Turken Wawa” ya zama akalar jan zaren tunanin wannan littafi ya dace. Abin da aka saba da shi an san shi. Abin da aka sani dole an zaune shi. Abin da aka zauna, ya zama abokin rakiya sai a sake jiki, a miƙa wuya gare shi, har ya zama raƙumin makaho, kai ka gani ba ni ka gani ba. A ganina, burin littafin shi ne, a riƙa
Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa GaskiyaAliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, NijeriyaBitar littafan SABO TURKEN WAWA na Halimatu AhmadUmar Bunza wanda aka gabatar a bukin ƙaddamar da littafin ranar 1 ga Watan Junairu 2014 a babban ɗakin taro na Tsangayar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Ambasadar Shehu Wurno  da ƙarfe goma na safe

Da suna Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu ɗan Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabansa da waɗanda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.

Gabatarwa:
Sassan adabinmu na baka ba ƙaramar rawa suka taka ba wajen daidaita muna akalar rayuwa a kowane ƙarni muka samu kanmu. Lallai, ba don jiya ba, da yau ta yi masassara. Yunƙurin kyautata rayuwar yau kuwa, gobe ce ake yi wa shimfiɗar maraba. Sarrafa karin maganar “Sabo Turken Wawa” ya zama akalar jan zaren tunanin wannan littafi ya dace. Abin da aka saba da shi an san shi. Abin da aka sani dole an zaune shi. Abin da aka zauna, ya zama abokin rakiya sai a sake jiki, a miƙa wuya gare shi, har ya zama raƙumin makaho, kai ka gani ba ni ka gani ba. A ganina, burin littafin shi ne, a riƙa sara ana daban bakin gatari, domin a hangen zabiyar tashe cewa ta yi:
Jagora:        Bari wanka da tutu don a ga iska,
Yara:           Hadari yamma ba ruwa ke da shi ba.


Bita:
An tsara littafin Sabon Turken Wawa cikin shafuka ɗari da arba’in da shida (146). Goshin aikin aka tsettsefe shi da shafuka ashirin da shida (26). Bayan shafin farko na sunan littafin. Shafin da ya bi masa aka sadaukar da aikin wurin da ya dace domin babu mai nunin gidansu da hannun hagu. An yi nagartacciyar godiya ga kagunan da aka sha madarar karatu. Daga nan aka samu tofa albarkar masana addini Sheikh Kabiru Haruna Gombe, da share fagen nazari daga Farfesa Salihu Bala Aljannare, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya kakkaɓe wundin karatun domin abin aljihu na mai riga ne. Saboda cikon sunan makaho da waiwaya marubuciyar ta ƙara wata gabatawa ta daban. Yin haka, bai zama sabon salo ba, shiƙa da daddare in ji kaza, domin malammamu cewa suka yi, mai sanda ke da fasalin bugu.
Ainihin ƙunshiyar littafin an zuba ta cikin babuka goma sha biyu. Waɗannan babuka su suka ba da shafi ɗari da ashirin (120) na aikin. A hangen bita, na kasa su zuwa gida uku: Gida na farko babi na ɗaya da biyu, su ne goshin aikin. Babi na ɗaya ya taɓo tarbiya ta addini da al’ada. A ƙarshe, aka yi kwakkwahe da kunya domin ta zama madubi da ma’auni ga babukan da za su rako su. Babi na biyu ya kalli wayewa da wauta a idon masu ganin sun waye, ya kuma tabbatar da wautar wayayyin zamaninmu.
Kashi na biyu ya ƙunshi babuka shida (babi na 3-7). Waɗannan babukan su suka yi wa aikin susa gurbin ƙaiƙayi. An taɓo sadarwar zamani da irin bi-ta-da-ƙullin da ke ciki. An kalli tauraron ɗan Adam da idon tarbiya. An ƙyallaro yanar gizo da hankalin tuwo da na addini. An waiwayi zaman banza da sunan majalisa da holewa ta mahangar tabaran Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato, da ya ce:
Ga jin daɗin rayuwa samari ka bicewa,
Suna wasu ‘yan ƙwange-ƙwange don nuna ɓacewa,
Su sa takalmin da ba wuya za a karewa,
Su shawo tabar da hankali zai juyewa,
          Su gigice don su samu damar ɓacinmu.
          (Waƙar Zaman Ɓanza).

Rukuni na uku ya ƙunshi (babi na 8-12). A nan aka fito da sakamakon wayewa ga suturar mata da maza da kuma yankan ciki da ya yi wa matan wayayyi ma’aikatansu da waɗanda ke zaune gidajensu. Ga irin abubuwan da suka haddasu, aka naɗe karatun da faɗakarwa ga waɗanda abin ya shafa da kuma hukumar da ke kula da su, an dai gaji an dawo ga hasashen Alhaji Muhammadu Gambo Fagada da ke cewa:
Jagora: Wai ga maciji a ɗora biyas shayi da sanda,
          : To ga ɓarayi, shi mib biɗi mai waƙar ɓarayi?


Nazari:
Ga al’adar Bahaushe, idan aka ce sabo turken wawa, abin da zai bijiro ga tunanin Bahaushe na gidi shi ne, abin da aka saba da shi a koyaushe shi za a riƙa tunawa. Yadda aka san shi jiya, za a ga ko yau, yana nan ba sauyawa. Daɗin da aka sha jiya, gobe ana sa ran a sha irinsa ko wanda ya fi shi. Yadda duk ake ɗaure dabbobi a turke, su mai da turke wurin zama na sakewa da jin daɗi, haka ɗan Adam yake ga abin da ya saba. Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa ya kakkaɓe muna ƙura ga ma’anar kalmar “Sabo” yana cewa:
Na saba miƙa sheɗara
Ta tsaya tsaf babu tanƙwara
Ai waƙa ba ta gagara
Muddin na tashi fassara
          Wada duk nika so ina faɗi rarara.
                   (Waƙar Yabon Sarkin Gwandu Yahya)

Don haka, sabo sanin abu ne na haƙiƙa domin Hausawa cewa suka yi, ido wa ka raina? Ya ce: “wanda na saba gani koyaushe”. Bisa ga wannan riwayar magabata ke cewa, sabo da ci kwaɗai yake sa wa. Idan aka naƙalci abu sosai su ce, hannu ya iya jiki ya saba. Dalili da haka ne suke ganin sanin asali kan sa kura cin kanjilo (ƙonannen kashin shanu). Don me muke ganin, ɗan gafiya ko bai yi sata ba yana dogon aro? Don ya saba da ganin banza koyaushe a gidansu. Ashe gaskiyar Bamaguje da ya shiga birni bai ga rumbu da masussuki da ya saba gani ba ya ce, “Ana zaman ƙarya”. Tattara hankali wuri guda da ƙuƙewa ga ginan ɓera da gafiya da yanyawa da tsari da damo, ba dare ba rana, ya sa makaɗa Maitandu Shinkafi ke yi wa wani gwarzo take da:
Jagora: Tsohon tabuda tsohon sallatau
Yara: Uban na Nababa ya saba da gina,
Jagora: Na mai kiɗi kwana suya yakai,
Yara: Kitsen burgu hak ya kamma shi gabanai na naso.
Gindi: Ya fito ma kusa Hausance
          : Nababa ya saba da gina.

Ga al’adarmu, idan aka saba da abu, ba a gajiya da shi, in ji malamin kiɗi Narambaɗa:
Jagora: Uban Yari uban malami
Yara: Kowag gaji bai saba ba
Gindi: Koma shirin daga
          : Gwarzon bahago ɗan Iro.

Idan ana biye da zaren tunanina, za a ga, an fi son a saba da abin ƙwarai mai amfanin mai sabo ko jama’arsa. Idan abin da aka saba da shi, ba na kirki ba ne, ba a son a mayar da shi turke. Irin wannan turke shi Hausawa ke ce wa, turke mai caɓo (taɓo) marigayi Alƙali Bello Giɗaɗawa ya tabbatar da:
Idan dabba tana sauri ga turke,
Da amfanin da tas san za ta iske.
          (Bargon Hikima)

Marubuciyarmu ta hango turken da caɓo, don haka take ganin wawa kawai zai saba da shi.

Wane ne Wawa?
Duk da yake an yi ƙoƙarin a fayayce wawa sosai a littafin, ba zai hana a ƙara wa Borno dawaki ba. Wawa shi ne, wanda bai san ciwo kansa ba, bai san abin da ke cutar da shi ba, bale mai amfaninsa. Wawa shi ne, mai kallon mutane cikin wauta a ma’aunin wayonsa na wauta. Wawa ya fi mahaukaci ban haushi, da ban takaici, ga ayyukkansa, da lafuzzansa, da tunaninsa. A harshen Hausa, wawa ya fi kowane nau’i na mutane sunaye barkatai masu fito da sifarsa da ɗabi’unsa da ayyukansa.
Bayan sunansa na yanka “wawa”, shi ne solo, samɓalto, satoto, hauge, sangalaɓe, shashasha, sususu, sakarai, bi-nan, dabba’uuna, haure, leɓo, saleɓo, hangaham, santoɓilo, talallaɓiya, hoce, gabu, raƙumi, dambalalle, jiɓananne, makananne, ga su nan dai. Da wawa da mahaukaci da jahili, kakansu ɗaya, iyayensu mata ne suka fito gidaje daban-daban. Rayuwar da yaranmu suke a kai yanzu ta yi canjaras da faɗar wani makaɗi Zari da ke cewa:
Jagora: Ina nika samun mahaukacin yaro wawa?
Yara: Ya tankwahe wando ya sa ƙafa ramin kura.

Duk wani abu da ya shafi wauta a wajen Bahaushe abin zargi ne, abin kushewa ne, haraka ce ta komawa baya. Bahaushe bai tanada wa wawa wani gurbi ba a gurbin rayuwa, face na tir! Da assha! Da kayya! Da wayyo! Yaro ba ya son magaji wawa. Mace ba ta son miji wawa. Talakka ba ya son sarki wawa. Sarki ba ya son talakka wawa. Makaɗa Sa’idu Faru cewa ya yi:

Jagora: Wawa bai san gacte ba
          : Don an ce za a ba shi sarki
Yara : Hay yag gama da tuntuɓe.

Gindi: Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu
          : Karsanin gidan mai saje shirinka ya yi kyau.

Makaɗa Narambaɗa ya yi shakundun da cewa:

Jagora: Gidan ga mutum huɗu ba su sarauta
Yaro  : Da samɓalto da satootoo
          : Shi wanga na ukku ƙazami,
          : Na cikon na huɗunsu hawaa’i.

Gindin: Shiri bajinin Mamuda
          : Abu na Namoda tsayayye.

Wautar Yau a Hankalin Jiya
Hankalin jiya shi ne, tsararren tunani na girmama gabaci, da riƙon amana, da tsayar da gaskiya, da sanin ya kamata na kariyar mutuncin mutum, da gidansu, da zuriyarsa, da garinsu, da al’ummarsa. Hankalin jiya shi ne, kamalar mutum ta aiki da magana, a ji mutum, a ga mutum, a yarda da mutum. Hankalin jiya, wayonsa gudun kunya, da adawa da ita, da ɗiyanta, da kowane bagire aka san mazauninta ne na dindindin da na wucin gadi. Hankalin jiya, ba ya shan iska wuri ɗaya da ƙarya, kuma bai taɓa aminta su ƙulla zumunta ba, ko da ta hanya ce mai gamin zumuntar dole. Hankalin jiya, ba ya da kasala, bai yarda kwaɗai ba, ba su abota da rowa, ba unguwarsu ɗaya da zaman banza ba, har ya ƙaura, ba su ga-maciji da yawon dandi. Zanannen sunansa ladabi, laƙabinsa biyayya, don haka ake yi masa kirari da nagari na kowa mugu ko sai uwar da ta haife shi. Mutanen jiya sun saba da ɗansu sosai, suka wayi gari a yau, cikin wasu ‘ya’ya na daban, da babu nagari ga iccen kabari. Allah Ya shiryar da mu.
Wayon yau shi ne, ado da ƙarya babba da yaro. Yaudara samun sa’a. Amana ta koma ganina. Gabaci ya koma wasan yara. Nagarta ta koma kasala. Kamun kai, ya zama ƙauyanci. Sanin ya kamata ya zama wauta. Biyayya ga gabaci sunansa gidadanci. Tarbiyantar da yara da ladabtar da su ya zama dabbanci. Tsare mata a gidajen aure, da kare mutuncinsu, tsohon yayi ne, da tauye musu haƙƙi. Ba su damar gwada tsawo da ƙatta, da zaɓen abokin hulɗa, da tanada musu ma’aikatun renon shaggun da suka haifa, shi ne cigaba, da ‘yancinsu, a wayon ƙarshen zamaninmu. Tun gabanin Musulunci al’adunmu ba su yarda da hautsinan ƙato da ƙatanya ba, bale yau da rana tsaka a yi muna sakiyar da babu ruwa. Sa’idu Faru ya tababtar da cewa, ko wurin buki a tsarin Bahaushe mata da maza zaman ‘yan marina suke yi a faɗarsa:
Jagora: Dogon sarki yana da kyawo
          : Ranar da an ka je daba
Yara  : Ya yi kyau da riguna

Jagora: Shi wanga ɗan gajere
Yara  : Ku a je shi gun rabon dawo

Jagora: Shi kai ma wanga dunƙule
Yara  : Shi kai ma wanga dunƙule

Jagora: Matuƙar wurin akwai mata
Yara  : Hat tuman gadi shikai

Gindi: Ya riƙa da gaskiya Muhamamdun Muhammadu
          : Karsanin gidan mai saje
          : Shirinka ya yi kyau.

Me Ake Ciki Yau?
Ko kusa  , hankalin tuwo ba zai yarda da kushe ci gaban mai ginan rijiya da muke ciki a namu ƙarni ba. Mai hankali duk ya nace ga karatun jaridunmu, da sauraren kafafen yaɗa labaranmu, da tauraron ɗan Adam da ke shawagi da hotuna da labaran duniyarmu, da wayar hannu da ta zama lalura gare mu, zai tabbatar da ba ta mutu ba ta ɓalgace. Mai wayo zai gano cewa, an tashi bisa ƙasa an koma a kan daɓe. Mai hankali duk ya san, da lauje cikin naɗi. Duk wani mai bincike zai gano, da walakin goro cikin miya. Masana sun tabbata an ƙi cin biri an ci dila. Duk mai hankalin tuwo zai gano ko bayan tiya akwai wata caca. Matsalolin tarbiya da suka yi muna turnaƙu a yau, na mugun maƙwabci ne, ba ka da mata ana haihuwan ɗiya da kamar ka.
Daga cikin ribatarmu da Nasara suka yi cikin rigar waɗannan na’urori akwai: koya wa yaranmu ƙazantattar tarbiyarsu ta neman abin duniya ido rufe, da bugun gaba da uwa, don a ɗaure wa zina gindi. An koya wa yaranmu fashi da makami, da fashi da muƙami, da tabanjamanci da ɗan kamanci, da kwartanci da aƙidar kowa ya ɗebo da zafi bakinsa. Kyawawan al’adunmu na aure da haihuwa da mutuwa, an durmuyar da su. Tsarkakakkiyar aƙidarmu ta addininmu a ko’ina an yi mata raɓo, an saka mu cikin ɗemuwar da ta fi dogon suma haɗari. A cikin masalatanmu da maƙaabartunmu da makarantunmu muryoyin wayoyinmu ke cashe kiɗe-kiɗen arna da waƙe-waƙensu na gumakansu da shaye-shayensu. An mayar da Alƙur’ani da Hadisai da nassoshin shari’a busan sheshe a wayoyin hannu da sunan kishin addini. Mun manta da al’adunmu, waɗanda aka ara muna, mun kasa iyawa. Na tababta waɗannan abubuwa ne Halimatu ke yi wa shaguɓe da: “Sabo Turken Wawa”.
Muradin taronmu a yau, gano irin illolin da suka haifar. Da iyaye da hukuma da masana su tashi haiƙan faɗa da su. Ka da a aminta da kitsen rogo. A rege yaudarar ƙawalwalniya (ruwan faƙo). A fahinci katawar Nasara ta zamani. A lura, kama da wane ba wane ba ne.
A da, cikin shege abin kunya ne, a yau, ya samu karin magana shege kowa ya Yi. A da, an ce, gaskiya ka faɗa ba sanda ba. A yau, mun ce, faɗa da faskiya tsaro ne. Magabata sun ce, namu namu ne, mu kuwa mun ce, in ka ji namu da mai shi. Addu’ar magabata a koyaushe ita ce, Allah da Ya ba ka raƙumi ya ba ni Zakara. Mu ko cewa muka yi, Allah da Ya ba ka raƙumi Ya ba mu wuƙa zakaran ya ci Ubansa. Duk waɗannan musibun da makanantansu cuɗanyarmu da waɗannan na’urorin ya haddasa muna su.

Ina Mafita:
          Hausawa sun ce, duk wurin da aka hau ice nan ake sauka. Tabbasa! Karen da duk ya yi cizo da gashinsa ake magani. Masu jihadin ƙarni na goma sha tara Mujaddadi Ɗanfodiyo da mataimakansa sun ji muna wannan tsoro tun bai bayyana ba Uryanan (tsirara). Babu mafita face:
(i)               Girmama namu al’adu kamar yadda suke girmama nasu. Kowa ya yi doro da al’adun gidansu.
(ii)             Yin garkuwa da addininmu ga duk wani baƙon abu da zai shigo mu.
(iii)          Daina koyi da su a kan kowane irin sha’ani, dama kare jini biri jini aka rabu a goshin ƙarni na ashirin. In babu ƙira me ya ci gawai?
(iv)           Haramta wa rubuce-rubucensu da wasanni leƙa makarantun da muke koyar da yaranmu tarbiyarmu.
(v)             Fito da wani sabon salon yekuwar yaƙar rubuce-rubucensu da wasanninsu da suka yi kanta a zukatan matasanmu kamar irin yadda muka taru a yau.
(vi)           Samar da Hukumma ta musamman da za ta fuskanci yaƙi da rashin tarbiya da hana baƙin al’adu yin shigan kutse a ƙasashenmu.
(vii)        Ƙirƙiro darusa a kowane mataki na karatu da za su yi arangama da  waɗannan abubuwa har sai mun ga baya gare su.

Ana cikin Gina ga wutsiya:
          Sabon tsarin da ake son a tilasta a kanmu matsayin addini, wata dabara ce ta  yi muna kwanton ɓauna. Cikin tsarin ake son a tilasta mu watsi da al’adunmu kyaawawa da addininmu ya halarta muna. Idan ba ku manta ba, da demokradiyya aka koya wa matan arewa karuwanci. Da ita aka haramta wa musulmi arewa da kudu kullin matansu. Da ita, aka laɓe aka soke muna shari’ar mahaliccinmu. Da ita, aka laɓe a yau (2013/2014) aka haddasa yaƙi a arewancin ƙasar nan da ba a taɓa yin irinsa mai muni ba ga tarihin ƙasar nan. Gare ta aka laɓe, aka ƙirkiro muna sunan da ba mu sani ba, ana yi muna kisan kyashi dare da rana. An tozartar da shugabanninmu. An hana muna ‘yancin addininnin da al’adunmu. An tarwatsa muna tattalin arziki. An mayar da mu saniyar wane cikin ƙasarmu. An yi amfani da addini da ƙabilanci da ɓangaranci an raba ƙasarmu, an sa himmar gamawa da mu gadan-gadan. Mun kasa taɓuka komai har sai da Allah Ya kawo rundunarSa ta rusa rundunar zalunci, duk da haka ba a daina kashe mu ba. Idan ba mu sa wa jikinmu gishiri ba, a zaɓen 2015 tun ba a raba akwatunan zaɓe ba, za a rautsar da shugaban ƙasa, ya ƙarƙare regowar da guguwar BOKO HARAM da aka ƙirƙiro muna ba ta ida ba.
Wallahi! Sai mun ɗebe bambance-bambancen siyasar ta kowane fati, mun rungumi fatinmu mai suna, Addininmu, Al’adunmu, Yankinmu da ‘Yancinmu. Wanda duk ya karɓa wannan kira, shi ne namu ko da bante ko guntun wando ya baƙunce mu. Wanda ya ce ba haka ba, ba namu ba ne, komai kaurin alkibbarsa da tsawon gemunsa. Idan tabbatar da tutar Biafara ya faskara. Kashe Sir Ahmadu Bello kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabula. Yunƙurin Gadion Orkah, ya zama kuwa baya ga yaƙi. Almarar BOKO HARAM ba ta biyan buƙatu kudurin 2015 da yardar Allah. Marubuta, ga sabon fage nan na rubutu da ya fi fina-finai da na’urorin zamani zama annoba ga arewarmu da ƙasarmu.

Naɗewa
A gai da Halimatu, a girgiza mata da ƙwazonta da hasashenta. A gai da babanmu, kuma shugabanmu, mai Martaba Sarkin Musulmi ga yin tsayin daka ga jagorantarmu. Mu yi godiya ta musamman ga mai girma gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko ga gagaruman ayyukansa biyu da ya yi wa takwarorinsa fintinkau a demokraɗiyar zamaninmu: Na farko, kare martabar Cibiyar Musulunci, Sakkwato na hana matarsa tallar kitso da beje da sunan First Lady. Allah Ya biya shi. Na biyu, yin fito-na-fito, da tawaye, ga ƙarya da munafucci da zurmuguɗɗu da kisisiniya ba tsoro ba ja da baya. A bisa wannan, Allah Ya yi masa jagora mu karɓe goriba ga hannun kuturu. Masu sauraro malamin kiɗa na kiran ku da:
         
Jagora: Na hore ki gaskiya bari tsoron Ƙarya
Yara: Mai Ƙarya munafiki Allah su yaƙ ƙi

Jagora: Har yau ba mu ga in da
          : An ka yi mai ƙarya ba

Yara: Amma ita gaskiya
          : Gani da mutane tay yi

Gindi: Gwarzon shamati na Malam taron giwa
          : Baban Dado ba a tamma da batun banza.
Na gode

Manazarta

Banza, A.M. 2013 ‘Darussan Daular Sakkwato ga Musulman Nijeriya
na hijirar 1435 AH”. Takardar da aka gabatar a Joint Youth Islamic     Organazation, Zamfara Satate, J.B. Yakubu Secretariat, (Nuwamba, 4.)

Bunza, A.M. 2013 “Ido Mudu Ne: Ko Bai Ci Ba Ya San Abin Da Ke
Cika Masa Tumbi,” Takardar da aka gabatar don walimar Samun muƙamin Farfesa ga Farfesa Aminu Abubakar Illela, a Illela L.G Secretariat (Dec. 14,).

Bunza 2013 “Muhimmancin Hijira A Kwanan Watan Musulunci”,
Takardar da aka gabatar ga Ƙungiyar Ɗalibai Musulumai ta Najeriya, Jahar Kabi, a    masaukin Shugaban Ƙasa, BK. Dec, 19th.

Bunza, A.M. 2013 “Gurbin Ilimi ga Haɗin kai da Cigaban Al’umma”,
takarda da aka gabatar a Zauro Development Association (ZADA) Disamba, 27.

Bunza, A.M, 2013 “Promotable Promotion Promotes Progressive
Professionalism”. Beingtext of paper presented at special Fishing Festival Organized in honour of    Justice Faruku Hassan Bunza as High Court Judge, Kebbi State, April, 28th.

No comments:

Post a Comment