Wednesday, December 26, 2018

Ba ta mutu ba ta Ɓalgace: (Tazarar Bi-ta-da-ƙullin Kafofin Yaɗa Labarai Na Waje Da Kafofin Sada Zamunta Na Zamani)
Duniyar ƙarninmu (ƙarni na 21) wata sabuwar duniya ce mai fassara zantukan hangen nesa na magabata; mai fashin baƙin kuramen nassoshin saukakkin litattafai da hadisai ƙiriƙiri. Musibun da suka yi muna katutu a al’ummarmu baya ta haihu ne na bayyanar huntu ubangijin mai riga (Bature) cikin bi-ta-da-ƙullin mulkin mallaka. Dasisar mulkin ci-da-ƙarfi na Bature, wata ambaliyar annoba ce, ga kyawawan ɗabi’u da al’adu; a kowace ƙasa aka girka shi. Ƙasashen da ke da kishin sana’arsu da ƙasarsu, tuni suka ankara, suka yi wa abubuwan tawaye a hukumance. Haka kuma, za a tashi tsayin daka a yaƙe su a ilmmance, da siyasance da aƙidance da al’adance da addinance, kamar yadda muka hallara a yau…
Ba ta mutu ba ta Ɓalgace: (Tazarar Bi-ta-da-ƙullin Kafofin Yaɗa Labarai Na Waje Da Kafofin Sada Zamunta Na Zamani)


Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato


Takardar da aka gabatar a taron wayar da kai da Ƙungiyar Dandalin Siyasar Kabi ta shirya ranar Assabar 26-9-2015 a Masasukin Shugaban Ƙasa, Birnin Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abubakar Na’amo Abdullahi da misalin ƙarfe 10:00 na safe.


Gabatarwa
          Duniyar ƙarninmu (ƙarni na 21) wata sabuwar duniya ce mai fassara zantukan hangen nesa na magabata; mai fashin baƙin kuramen nassoshin saukakkin litattafai da hadisai ƙiriƙiri. Musibun da suka yi muna katutu a al’ummarmu baya ta haihu ne na bayyanar huntu ubangijin mai riga (Bature) cikin bi-ta-da-ƙullin mulkin mallaka. Dasisar mulkin ci-da-ƙarfi na Bature, wata ambaliyar annoba ce, ga kyawawan ɗabi’u da al’adu; a kowace ƙasa aka girka shi. Ƙasashen da ke da kishin sana’arsu da ƙasarsu, tuni suka ankara, suka yi wa abubuwan tawaye a hukumance. Haka kuma, za a tashi tsayin daka a yaƙe su a ilmmance, da siyasance da aƙidance da al’adance da addinance, kamar yadda muka hallara a yau.

Lalurar Kafafen Sadarwa A Duniyar Mutane
        Idan aka bi diddigin al’adar sadarwa, mahaliccin halittu da kafofin sadarwa ya halicci hallittocinSa (baki, ido, kunne, hanci, hannu, ƙafa da kai). Daga gare su kowace hikima ta sadarwa jiya da yau ta samo tushe. Sadarwa tsakanin kowace irin halitta lalura ce. Bahaushe na cewa dole “lalura” domin ita ce uwar na ƙi. Babu zamanin da zai ci gaba babu nagartattun hanyoyin sadarwa ga waɗanda suka rayu a cikinsa. Abin kula a nan shi ne, a kowane lokaci aka ce, za a sabunta wani abu, dole sai wani abu sabo ya shigar katse a ciki. Dole in cigaba ya kasance na rage zango; irin na mai niyyar zuwa sama da ya taki faifai, in ko ya zamo na mai ginar rijiya; in ga tukunya in ga tulu, yara za su samu katanga. A duniyar ƙarninmu, cigaban sadarwa na kowace ƙasa da nahiya ya shiga wani mataki na kimiyya; wanda kunnuwa da idanu za su shaidi abin da ba su taɓa yin mafarki ba a ƙarnin da ya gabata. Bisa ga tunanin gabaci, banza ba ta kawo zomo kasuwa. A koyaushe suka ga baƙon abu sukan ce: “Da dalili jigida cikin gafakka”. Duk yadda suke son abu, suna ganin amfaninsa, ba sa rasa ɗora shi a kan ma’aunin; “Da lauje cikin naɗi”. A falsafarsu ta ganin; “Mai faɗaɗe ba ya tayar da hannunsa sama”, shi ya sa suke yi wa abubuwan zamani kallon mai bisa ruwa, idan lalurar shiga ciki ta kama su, sukan yi wa abin shiga ramin kura. Muradi dai shi ne, in an ga da amfani; a sunsuno a dawo, in ba amfani; a yi shigar shantun ƙadangare; wani ya gani wani bai gani ba; irin zuwan kare ga aboki. Ku ba ni hankalinku da kyau mu fara buɗa ƙofar sharhi.

Dalilan Kafa Kafofin Sadarwa
          Kafofin yaɗa labarai da sadarwa na kowace al’umma suna da alaƙa da siyasar hukuma. Na farko shi ne, a yaɗa manufofi da aƙidojin hukuma ga jama’a. Na biyu, a wayar da kansu kan dokoki da tsare-tsaren ƙasa. Na uku, su san da shugabanninsu. Na huɗu, yaƙar abokan adawar siyasa da aƙida. Na biyar, domin tallace-tallace, da yekuwar gangami ta aikin gayya, da yaƙe-yaƙe, da tsagaita wuta, da sulhu, da daba-shirin ko ta kwana. Na shida, bai wa talakawa da abokan adawar siyasa damar furta ƙorafe-ƙorafensu, na abubuwan da ke yi musu ƙaiƙayi ga tafiyar da ake ciki. A tsari irin na mulkin mallaka da jari-hujja da gurguzu. Kafofin sadarwa babban makamin cigaba da renon aƙida ne; ga zukatan mabiya da ‘yan-sa-ido. Bisa ga wannan ƙuduri ne Turawan Ingila da Faransa suka yi wa Afirka kashin dankalin baƙauye, suka kakkafa kafofin sadarwa cikin harshensu na mulki.

Kafofin Sadarwa Na Radiyo
          Babu yadda za a yi wa hanyoyin sada zumunta na zamani adalci, ba a taɓo tarihin gidajen rediyon duniya da suka haifar da su ba. Sadarwa ta rediyo, tana da sauƙi da arha da wadatarwa ta yadda saƙon zai kai ko’ina, cikin lokaci ɗaya, da murya ɗaya, cikin harshen da ake son a isar da shi. Tunanin ƙasashen Turai da buɗa Hausa a gidajen Rediyon BBC da Jamus da Faransa da Beijing da Mascow wani babban haƙo ne da yau, ƙasashenmu sun haɗiye ƙotonsu, an riga an kama su, abin da ya biyo baya cikon sunna ne makaho da waiwaya. Da baya ƙwarai, ƙasashe irin su Iran da Masar da Indiya da Sudan da Saudiyya suka ahumo bayan an kusan suɗewa. A sanadiyyar kafofin sadarwa na Turai na gidajen rediyo za mu iya cewa:
i.                   An sa mutane da yawa hasarar lokuta masu ɗimbin amfani a rayuwarsu wajen sauraron labarai.
ii.                 An dasa wa mutane da yawa aƙidun da ba su ko san kansu ba, balle su amfane su.
iii.              An cusa wa mutane ƙiyayya da ‘yan’uwansu, an sa su soyayya da maƙiyansu; an raba musu hankali biyu.
iv.               An gurɓata musu al’adunsu kyawawa da ƙazantattu.
v.                 An rusa musu nagartattun al’adunsu na gado.
vi.               An samu damar leƙo sirrin ƙasashenmu, wasu, mu da kanmu muka kai su ga maƙiya da sunan aikin jarida.
vii.            An haɗa mu yaƙe-yaƙe da zanga-zanga, in hayaƙi ya yi turnuƙu, a zo da ceton bisa mai kan uwa da wabi.
viii.         An zubar da girman gabaci gare mu, an muzanta jagororinmu, an kururuta martabar na wasu a kunnuwanmu.
ix.               Mun koyi tonon asiri da tabanjamanci da cin ido da cin mutunci da ƙididanci cikin salon wayewa.
Kodayake, a koyaushe rediyo yana da rawar da yake takawa, amma da aka yi masa rata kaifin nasonsa ga zukatan matasa ya ragu. Da ma, cutar wayewa zukatan matasa take nema; baba ɗan zamani an gama da labarinsa. Hausawa na cewa: “Ana cikin gina ga wutsiya”, abin nufi a nan, hankaka da mai aya an gana; ta bakin Dakarkari mai farautar ɓera ya gamu da gawurtaccen maciji; ya yi sa’a babba. Ana farautar mutane cikin duhu a rediyo, sai ga dabarar rediyo mai hoto da makamantansu 

Kafofin Sadarwa Na Majigi
          Bayan gayya ta gama aiki; sai ga wani sabon salo shiƙa da dare in ji kaza. A majigi, za a ga mai isar da saƙo, da waɗanda ake bai wa saƙo, da masu sauraron saƙo. Akwatin majigi, kamar akwatin rediyo yake, a da, a gidajen masu sarauta ake aje su a shaƙa wa gari gaba ɗaya barkonon tsohuwa. Samun manyan kafafe irin su CNN da BBC da Al-Jazeera, da sauran manyan tashoshin duniya; Asiya da Afirka da ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Turai ya gurɓata tunanin matasan duniya. Ta fuskar su ne aka samu:
i.                   Makaftacciyar soyayya tsakanin samari da budare; da ta saɓawa, addininmu da al’adunmu da wayewarmu.
ii.                 Suturorin bayyana tsiraici da batsa; da suka gargaɗi kunya daga idanun matasanmu, tarbiyarsu ta gado ta ruguje.
iii.              Sake raya duniyar bori da tsafe-tsafe, da addininmu ya yi wa koran kare a ƙasarmu, yau baya ta haihu.
iv.               Raya ta’addanci da fito-na-fito da hukuma, da yi wa doka takin izgili, da wulaƙanci ga gabaci.
v.                 Rashin gaskiya iri-iri, da maguɗi da zurmuguɗɗu da zamba cikin aminci, a nan ake karanto su, a aikata su a ƙasashenmu, “Ba mu ci ƙashi ba, a sa mu aman tsoka”.

Hanyoyin Sada Zumunta Na Zamani
          A tunaninmu na ɗaliban al’ada, da Namadina da Namakka da Na’Allah da Maimadina da Modu da Mamuda duk Muhamamdu suke ƙoƙarin fassarawa. Babu abin da ya bambanta gudu da sassaka face susan baya. Da hanyoyin sada zumunta na zamani; da kafofin sadarwa da muka ambata a baya, duk manufa ɗaya ce babu nagari ga icen kabari. Ga alama, Social Media manufarsu a bayyane sada zumunta da sadarwa ta gaggawa wadatacciya. Bayyanar na’ura mai ƙwaƙwalwa (computer) shi ya haifar da Yanar Gizo (internet) daga nan wayar hannu ta bayyana da hanyoyin sada zumunta mabambanta irin su:
1.     2go
2.     Facebook
3.     Twitter
4.     Mozat
5.     BBN
6.     Badoo
7.     Eskimi
8.     Palmchat
9.     Waplog
10. Instagram
11. Wechat
12. Nimbus
13. Mzeed
14. High fire
15. YouTube
16. Yahoo messenger
17. Whatsapp
18. Goggle
19. Email
20. Linkedin
21. Skype
22. Smsliɓe
23. Flicker
24. Hi5
25. Hotmail
26. Netlog
27. My space
28. Traɓbuddy
29. Playlist

Waɗannan tsakure ne kawai domin ba da misali. A koyaushe, suna nan jibge a wayoyin yaranmu da Yanar Gizon da suke dubawa dare da rana. Babbar matsalar da ke tattare da waɗannan hanyoyin sadarwa ita ce:
i.                   Sun mamaye dukkanin hanyoyin sadarwa da suka gabace su, kuma su ne yayin zamaninmu.
ii.                 Suna da sauƙin mallaka, da sauƙin sarrafawa, da saurin shiga kowane saƙo na ƙasa.
iii.              Sun samu karɓuwa a ɓangarorin yaɗa ilminmu; daga ƙananan makarantu har zuwa jami’o’inmu. Sun sa matasanmu tsaka.
iv.               Ana karanta saƙunansu, ana ganin hotuna, ana hulɗa ta kai tsaye da kowa ake son a yi hulɗa, irin ta faɗi-in-faɗi, da ga-ni-ga-ka.
v.                 Babu lokacin da ba a kama su, babu wurin da ba a saduwa da su, babban muninsu kaɗaituwa da mai su, su yi masa kisan mummuƙe kan a ankara ya fanɗare.
vi.               A yau, wai su ne wayewa; rashin kutsawa ciki ne ƙauyanci, a fagen neman tafiya da zamani, zamani ya tafi da hankalin mai su.

Ta-tsaka-mai-wuya
          Da haihuwar mutum ya yi wa duniya salamu alaikum, abubuwan da zai ci karo da su gabanin ya yi sallama da duniya su Bahaushe ke cewa; “Ta tsaka-ma-wuya”. Bayan muna a kan tarbiyarmu ta gargajiya gwargwadon hankalinmu da wayonmu, da aƙidarmu da tunaninmu. Cikin tsakiyar aiki da hankalin tuwo; hasken saukakkin addinai ya zo, ya gyara muna zama gwargwadon yadda mahaliccinmu ke son mu kasance. Bayan  mun miƙa wuya, mun daidaita siyasar rayuwarmu; sai kwatsam Yahudu da Nasara suka yi wa ƙasashenmu shigar kutse da yaƙi, suka tarwatsa muna tsari; suka wargaza muna addini; suka lahanta muna al’adu; suka ɗaga nasu cikin dasisar kafafen yaɗa labarai, da littattafai, da jaridu, da mujallu, cikin rigar karatun boko. Da suka fahimci sun kama mu a wuya; suka fito wa kusa (ɓera) Hausance da kafofin sada zumunta na zamani. Ta-tsaka-mai-wuya da muke ciki a yau sanadiyyar kafofin sada zumunta sun haɗa da:
i.                   Yawaita da bazuwar fasadin zina da liwaɗi da maɗigo a ƙasashenmu. Ƙungiyoyin da ke raya waɗannan bala’o’in suna da kafofinsu na musamman. Sannu a hankali yau ƙasarmu tana cikin sahun gaba na masu waɗannan ɗabi’u. Makarantun gaba da firamare da jami’o’inmu, sun zama dandalin karatun musibun. Hasali ma, yaranmu da muke Turawa waje karatu, sun zama ‘yan barandan yaɗa musibun.
ii.                 Duk mai karatun jaridunmu na gida, da sauraron kafofin yaɗa labaranmu, zai tabbatar da ƙaruwar matasa masu kashe kansu. Yaron da ya rataye kansa a fanka a Badarawa, Kaduna, da yaran da suka kashe abokin wasansu a Kaduna duk a shekarar 2014, duk sun yi iƙirarin a kafofin sada zumunci na zamani suka koya.
iii.              Ta’addanci da ke aukuwa na sace-sacen mutane (samame) a yau ya zama ruwan dare. Babu safiyar da jaridu ba su fitowa da labarin satar mutane da ayyana kuɗin da ake son fansarsu. An sha sace sarakai da tajirai da malamai da ƙanana yara da matan aure da wakilan tsaro. Gabanin cigaban ƙarninmu ba mu taɓa jin haka ba. Idan aka wuce yadda ake ciki a halin yanzu, sai fita waje ya gagari duk wani mai mutunci cikinmu.
iv.               Kisan gilla ga jama’a da ba su ji, ba su gani ba, yau shi ne aikin yi ga marasa aikin yi. Abubuwan da matasanmu ke karantowa, da gani, a saƙon internet, babu ƙarfin soja da ‘yansanda da zai iya murƙushe shi. Matsalar BOKO HARAM kamun ludayi ce, dahuwar da internet ke yi in ta nuna sosai, bindigar ‘yan tauri ce, ke gawa, mai ke gawa, abin da anka nuna gawa, gawa uku jere ga juna. Da mu, da su, da sojojinmu, da wakilan tsaro an gama yawo.
v.                 Yau, kunya an kunyata ta, ita ke jin kunyar marasa kunya ba marasa kunya ke kunyarta ba. Masu jin kunyar auka wa kunya, sun zama ƙauyawa. Sanadiyyar kafofin sada zumuntar zamani, duk wata ta’asar da muke jin kamar tatsuniya ce a da, a yau gamu tsamo-tsamo a ciki.
vi.               Ƙarya ta zama tobashiyar matasanmu. A saurari labarin ƙarya a yaɗa zancen ƙiren ƙarya wani sabon salon wayewa ne ga matasanmu da iyayen gidajensu.

Ba wai ina son in kashe abubuwan ba ne gaba ɗaya ba; amma duk abin da cutarsa ta bayyana, komai amfaninsa a yi taka-tsan-tsan da shi.

Ina Mafita? 
          Ba mu ne farkon shiga wannan lalura ba, hasali ma, wasu sun riga mu, kuma sun ɗauki matakan taho-mu-gama da ita. Irin wannan haɗuwar na daga cikin matakan yi wa matsalar kwanton ɓauna, idan ta zaburo, a yi mata koyon keken ƙato; da keke da ɗan koyo da mai koyarwa kowa ya ji a jikinsa. Bayan ɗaiɗaikun agaji da ake yi na ƙungiyoyi ya zama dole:
i.                   Hukuma ta fito da wani tsari da zai ceto matasanmu daga musibar da ta mamaye ƙasarmu.
ii.                 A fito da sabuwar manhajar karatun boko da za ta tunkari ire-iren waɗannan miyagun ɗabi’u da hana su tasiri a zukatan matasanmu.
iii.              Ya zama dole, iyaye da magabata su kula da ‘ya’yansu maza da mata ta fuskar binciken wayoyinsu da taƙaita musu lokutan hulɗa da su.
iv.               A fito da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin da jaridun ƙasa da jaha na kushe bi-ta-da-ƙullin kafofin sada zumunci.

Karen Da Ya Yi Cizo Da Gashinsa Ake Magani
          Idan za mu yi wa kanmu adalci, dole mu waiwayi baya da idon nazari;  mu hangi gaba da ƙudurin gyara. Babbar musabbabin dukkanin waɗannan matsaloli daga siyasar ƙasarmu ya tsira. Satar dukiyar hukuma wani abin bugun gaba ne mai jawo ɗaukaka ga irin tsarinmu. Mayaudara su ke samun cigaban muƙami a aikin hukuma. Wanda bai ƙasaita da dukiyar ha’inci ba kujerun muƙaman siyasunsu ya alluhe su. Ba mu taɓa ƙyamar mayaudara ba da abin yaudarar da suka yaudaro; yaya za mu ba zalunci tsaro? Dokokinmu don talakawa da marasa galihu aka tanade su, a kansu suke ƙarewa. Yaya za a yi talakawa da marasa galihu su harari idon masu doka da idon tausayi? Ga alama, yanzu abubuwa sun soma gyaruwa idan aka yi duba ga kujerar shugaban ƙasarmu da mataimakinsa da masu ba su shawara. In haka ta doge, wataƙila, hasashen Ra-ra-ra na faɗar masu gudu su gudu zai tabbata. Matuƙar aka gargaɗi zalunci ‘yan rakiyarsa rashin tarbiya da rashin kunya da ta’addanci sun yi hasarar mai masauki, birin su ya yi kuren rehe, dole su yi jagege (zagege) ta bakin Bafulatani da ya faɗo daga goriba ya zarce rijiya ya ce: “Jagege mun faɗo mun faɗa”.

Naɗewa
          Babban kure ne jibga wa Shaiɗan kurakuranmu na ganganci don mun san bai taɓa fitowa a yi sa-in-sa da shi ba. Idan mulkin Turawa ya haddasa musa taɓasgarar matasanmu, yau mu ke mulkin kanmu da kanmu. In dai A’isa ka ɓata rawa daga yau ta daina. Wa ke ba matasa kayan shaye-shaye su yi musu banga? Wa ke hayar‘yan ta’adda a kashe masa abokin adawa? Wutar nan mu muke hasa ta, mu za mu fara ganin hayaƙinta; mu ke iya ɗebo ta; mu kaɗai ke iya kasheta. Narambaɗa ya tabbatar da haka a waƙar “Ya ci maza”:
Jagora:        Shin ku taro na tambaye ku
          :Kowa yag ga wuta an ka ce: “A ɗebo”
          :Wa ke zuwa?
Yara:           Wanda yag gani ka zuwa
          :Ko was shaida shi ka shan rana
          :In bai je ba yai batun banza
          :Ko can yanzu shi batun banza
          :Daɗin hwaɗi garai
Gindi:          Ya ci maza ya kwan shina shire
:Gamda’aren Sarkin Tudu Alu

No comments:

Post a Comment