Monday, December 31, 2018

LINGUISTIC BALANCED SHEET OF KYANGA: (Between Endangerment Status and Extinction)

December 31, 2018 0Human languages develop alongside with the life span of their speakers. It’s the speakers that motivated its development and other wise. If they are strong, courageous, and intelligent, their language would be strong enough to be well placed and wide spread beyond their political boundaries. Less privileged languages belong to a very minority group politically marginalized and socially isolated, economically below average and educationally left behind. These are the situations critically observed by the experts to classify languages at various endangerments status. In the assessment of this essay, Kyanganci or the Kyanga language is seen as one of the…

Agitation and Dialogue in Hausa and Ful’be Encounters: (Reassessing the Hausa Version as Depicted in Hausa Orature)

December 31, 2018 0


Folklore as a discipline is an important historical source in the territory of Oral tradition. Whatever shortcomings we may think is possible in self-styled narration of the history and happenings in our societies, it is very unlikely to make any significant input in our history outside the speculations of the popular oral sources. Fulbe and Hausa, though of different historical, cultural and linguistic backgrounds, are today socially integrated in Nigerian context and generally named as Hausa-Fulani. I do not contest the Nigerian factor behind the tag-name but the fact remains that, Hausa and Fulani of the northern region of the country are very close associates from time immemorial. Dandatti (1975) as per the role of oral singers in Hausa-Fulani societies…

Sansamin Gamji Mai Cika Bakin Akuya: Bitar Littafin Sanyinna District: Events, Trends and Turning Points

December 31, 2018 0


Ficen mutane da ɗaukakarsu a duniyar zamaninsu yana cikin tarihinsu. Tarihinmu wani madubin ƙyallaro asalinmu ne da ɗabi’unmu da dangantakarmu da zamaninmu. Wanda ya taskace tarihinsa, ya kundace shi, ya hutar da al’ummarsa, ya agaza wa ƙasarsa, ya rage wa zuriyarsa dawarar kalato gutsattsarin labarin kunne ya girmi kaka na taliyon sama wa kai tushe cikin ƙila-wa-ƙala. Tsaftatacciyar hanyar da za a yi wa Turawan mulkin mallaka zanga-zanga, da tawaye, da ature, ga bahaguwar fahimtar da suka yi wa Daular Sakkwato cikin ƙazantaccen harshe a rubuce, ita ce, ma’ilmantar kowace ƙasa, da gunduma, su sake kakkaɓe kundin tarihinsu. Tabbas, babu…

Sakkwato Ce Tushen “Hausa” In Ji Narambad’a: (Laluben gudunmuwar mawaƙa a kan asalin Bahaushe da harshensa)

December 31, 2018 0


Irin matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniya ya kyautu a ce, an kakkaɓe buzun karatun binciken tarihin asalinsu da harshensu tuni. Matsalolin da suka yi wa binciken asalin Bahaushe tarnaƙi sun haɗa da; shigan sharo ba shanu da wasu masana fannoni ke yi wa karatun. Haka kuma, ƙarancin masu bincike, da kasa daidaita akalar bincike, da ƙin aminta a yi taron dangi ga abin da ake bincike cikas ne babba. Babbar matsala duk ba ta fi saki zari kama tozon da aka sha yi wajen assasa tushen bincike ba. Ga maciji ana gani a dinga biyar shayinsa da sanda wai don nuna ƙwarewa, a ƙarshe, ya tsere, a yi ɓatan ɓaƙatantan. Wannan takarda ta himmatu ga tauraro ɗaya Ibrahim….

Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe

December 31, 2018 0


Matakan rayuwar Bahaushe ba su samu kulawar masana da manazarta da ɗaliban nazarin Hausa sosai ba. Wannan takarda ta lalubo matakan rayuwar Bahaushe uku: aure, da haihuwa, da mutuwa. Ta ɗauki kayan cikin littafin Ruwan Bagaja gaba ɗaya ta ɗora su a kan waɗannan turaku uku. An nazarci rawar da suka taka wajen kai littafin zama zakaran gasar 1933. An yi garkuwa da matanonin nassoshin littafi wurare ashirin (20) a ƙunshiyar kayan cikin takardar. An gano wurare goma sha uku (13) da aure ya taka rawar gani. An ƙyallaro saƙonni goma sha uku (13) da aka isar ta fuskar haihuwa. An tantance wurare ashirin da bakwai (27) da aka yi garkuwa da mutuwa domin isar da saƙo ga masu karatunsa. A jimlace matakan rayuwar…

Makamin Dimokraɗiyya A Falsafar Al’ada

December 31, 2018 0


Gudunmuwar al’ada ga haɓaka dimokraɗiyya daji ne ba ka da gambu. Don haka, na zaɓi in yi masa gambu:[1] “Makamin Dimokraɗiyya a Falfasar Al’ada”. Muradina shi ne, sai na harari makaman da ke a hannu. Mu ga irin kaifinsu, da rawar da suka taka ta gara jiya da yau. Daga nan, mu ɗan linƙayi matsalolin da dimokraɗiyya take ciki a yau, da irin barazanar da masu hangen nesa ke ganin za a fuskanta. Idan shimfiɗarmu ta daidaitu, sai mu yi karan gwajin dahi da ma’aunin al’ada ɗaya da muke ganin, zai yi wa matsalolin, da barazanar, walki daidai da kwankwasonsu. Ƙunshiyar kayan cikin wannan takarda, ba za su yi muna susa gurbin ƙaiƙayi ba, sai mun yi fashin baƙin fitilun kalmominta, domin karen da ya yi cizo da gashin da ake magani.

Huce Haushin Rashi A Kan Mai Samu

December 31, 2018 0

  
A fahintar ɗaliban al’ada, a kodayaushe akan tsinci al’adun mutane cikin harshensu da adabinsu. Al’ada kandamemen fage ne da babu wanda zai rayu a wajen ta, komai dabararsa sai an ga gurabunta a rayuwarsa. Don haka, ɗaliban al’ada ke ganin waƙoƙin baka wani babban rumbun kinshe al’ada ne da bai kamata a bari su salwanta ba a kowane zango na rayuwa. A rayuwar kowane mutum abu biyu ke tare da shi a cikin fafitikar rayuwarsa: ‘samu’ da ‘rashi’. Ga al’adar nema, tushen neman wani abu shi ne ‘rashinsa’. Ko dai babu shi, ana son a samo shi, ko kuma an same shi, ya ƙare, ko yana barazanar…

Sunday, December 30, 2018

Maƙarƙashiya

December 30, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ya”. Yawan baitocinta hamsin (50). An kammala ta ranar Lahadi 25/05/2014 daga Masar zuwa Katsina, an haɗa ta a Kano, Mumbayya House, BUK, ɗaki na 10. Ga dukkanin alamu kashe-kashe da zubar da jini da ta’addancin da ake son a liƙa wa musulmin Arewacin Nijeriya, maƙarƙashiya ce. Tilas, a sake zama a nazarci matsalolin da idon adalci a ɗebe bambancin addini da aƙida da siyasa da yanki da ɓangaranci. Zancen Boko Haram wata sabara ce da ake fakewa da ita a harbi barewar da ake son a kashe. Idan haka ne kuwa, ya zama dole a sake lale ‘yan dara, a hura wuta kowa ya ga rabonsa, komi taka zama ta zama.

Ganin Ido Nassi Ne Da Babu Ƙila-Wa-Ƙala

December 30, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “wa” yawan baitocinta saba’in da ɗiya (71). An kammala ta ranar Larba 8/01/2014 a kan hanya tsakanin Katsina zuwa Sakkwato. Burinta kakkaɓe ƙura ga ‘yan kurakuran da suka gabata na rikicin ganin watan Ramala na shekarun 2012, 2013 da 2014. A shari’armu, yaƙinin ganin wata ya kore kowane irin tawili. Ana dogara da yaƙinin gani a kawar da maganar kowa, komai nauyinsa a sikelin zamaninsa. Idan ganin ido ƙuru-ƙuru ya tabbata zancen kalanda da kwamfuta da hisabi ba su da gurbin zama in ji Manzon Allah (SAW). Ƙaryata yaƙini domin sauraren umurnin wani ko wasu cin dugadugan Manzon Allah (SAW) ne. Fatawa da tawili da ƙiyasi da duba zuwa ga al’adar ƙasa/jama’a na siyasar shugabancinta duk ganin yaƙini ya haramtar da su. Dogara ga ganin ƙasa mai tsarki ko kirdadon ibadojin da ake gudanarwa ciki na tsayuwar Arfa da yanka ba ya da madogara ga littafin Allah da Hadisan ManzonSa (SAW). Kawar da kai ga yaƙinin ganin wata a kan kowane irin dalili saki zari kama tozo ne. Annabi (SAW) bai ɓoye komai a saƙon manzancinsa ba. Da wane dalili za ka bar umurninsa ka bi sabaninsa?

Saturday, December 29, 2018

Kifi Na Ganin ka Mai Jar Homa!

December 29, 2018 0


Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ƙe”. An gina ta da baitoci talatin da uku (33) an kammala ta Alhamis 16/01/2014 da ƙarfe 11:05 na dare a Arkilla, Wamakko jihar Sakkwato. Babban abin da ke hana wa ruwa gudu a rayuwar ‘yan Adam ita ce hassada. Jiyewa mutane, da ƙin su da ɓata su da kushe cigabansu da rena ƙwazonsu da wulakanta nasarorinsu da shafa musu kashin kaji duk hassada ke haifar da su. Ɓata lokacinka na ƙoƙarin nuna cikas ga wani ba kai ba, shi zai ba da damar a gano babban cikas da ke a ƙirjinka na hassada. Me zai hana idan ka san ba yabawa za ka yi ba, ka sa wa bakinka takunkumi? Da ka bi wannan shawara, ka huta, an huta da kai.

Laifi Tudu Ne

December 29, 2018 0


Waƙar ƙwar uku ce, babban amsa amonta “na”. Yawan baitocinta saba’in da shida (76). An kammala ta ranar 10/06/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. Mai yawo lisafin laifukan mutane da leƙen kasawarsu da ƙoƙarin ci musu zarafi da muzanta su bai tsaya da kyau ya karanci nasa hali ba. Don haka, waƙAr take hararar abubuwan da mahasada da magabta da ‘yan sa ido da ‘yan sai-mun-gani ke ƙoƙarin kai hari ga marubucinta. A ganin Bahaushe, mutum duk ɗan tara ne. Da akwai ɗan goma, da shi ya kamata ya yi wa ‘yan tara kallon kifi na ganin ka mai jar koma (homa). Kama kanka! Wanda ke cikin ta tsaka mai wuya, ina ya ga bakin kirari?

Allah Ba Ka Da Dole

December 29, 2018 0An tsara waƙar a tsarin ‘yar tagwai. Babban amsa amonta “wa”. An tsara ta cikin baitoci saba’in da tara (79). An kammala ta ranar Jmu’a 25/1/2013 a Sakkwato. Addu’a ce da godiya ga Allah ga irin taimakonSa ga bayinSa ga tsallake tarkon miyagun abokan zaman zamani. Godiya ga Allah wajibi ne ga kowane bawa, bale wanda Allah Ya kuɓutar da shi ga tarkon makircin abokan ƙarshen zamani “kifi ku ci ‘yan’uwanku”. Allah Ya yi muna tsari da tsarinSa. Amin!

Kaska

December 29, 2018 0Waƙar Kaska mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta hamsin da takwas (58). An kammala ta ranar Lahadi 30/6/2013, a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa Katsina. A ganin Kaska, siyasar zamani ta demokraɗiyya ita ta jefa ƙasarmu cikin musibun da take ciki a yau. Siyasar zamani ta tarwatsa saraua da masarautu. Ta gigita addini da mabiya. Ta muzanta malaman addini, da ma’aikatan hukuma. Ta ɓata wa talaka tunani. Ta sagarta matasa maza da mata. Ta danbala ‘yan kasuwa. Ta yi wa gaskiya idon marurugiya aka yi wa ma’abotanta ƙofar raggo. Da dai an koma ga tsarin da wanda ya yi halittu. Ya shirya wa halittunSa, da abu ya fi.

Gaskiya Ina Laifinki?

December 29, 2018 0


Wannan waƙar ‘yar tagwai ce. Babban amsa amonta “ya”. Yawna baitocinta arba’in da biyar (45). An kamala ta Talata, 3/7/2013, a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. A irin hasashenta, babu abin da ya fi gaskiya daɗi a duniya. Tsohuwa ce da gidan kowa ana sha’awar ta, kuma duk wurin da aka rasa ta ko aka hana ta zama ko aka ba ta tsoro wurin ya ɓaci. Farfaɗo mata da martabarta ta samu sakewa a zamaninmu shi kaɗai ne zaman lafiyarmu da kwanciyar hankalinmu. Rashin ba ta masaukin ƙwarai shi ya lalata zamaninmu.

Kashi Ya Game An Sake Rabawa

December 29, 2018 0


Waƙar mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta saba’in da uku (73). An kammala ta ranar Jumu’a 19/05/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina. Saƙonta gargaɗi ne ga ma’abota riƙo da kira zuwa ga sunnar Manzo (SAW) da su gyara zama ciyawa ta ci doki. Abubuwan da aka kora a da, a yanzu ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Idan maƙoƙo ya fito a bakin zabiya zancen waƙa da zaƙin murya ya ƙare. Ina laifin wanda ya gaya maka bakinka na wari ka nemi ruwa da asawaki ka wanke ɗoyin ya kawa! Matuƙar imani na ƙaruwa da raguwa, to, namu ya ragu. Allah Ya cece mu.

Gyara Kayanka

December 29, 2018 0


Wannan waƙar ‘yar ƙwar hudu ce. Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta ashirin da takwas (28). An kammala ta ranar Jumu’a 28-05-2013 a garin Katsina, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa. Kira take ga jama’a da su guji giba da tsegumi da yaɗa ji-ta-ji-ta da hassadar abokan zama. Ta yi wa zunɗe da raɗa da kwarmato da an-yi-an-ce da sa ido zangazanga. Matuƙar aka ba su tsoro suka guje wa wuraren shawagin ‘yan Adam, za a samu zaman lafiya.

Jiya Ba Yau Ba

December 29, 2018 0Wanda duk ya ga jiya, ya san yau na buƙatar agajinmu. Ganin irin riƙon sakainar kashi da na yau ke yi wa al’adunmu na jiya shi ya tunzura ni rubuta wannan waƙa. Masu gani dole sai an sa su, da masu ganin ba a yi sai da su, sun yi kuskure. Hausawa sun ce, wanda ya riga ka barci dole ya riga ka tashi. Idan za a yi koyi da gabaci ba za a ci wahalar sakamakon bin son rai ba. A ganina, har gobe mazan jiya guntun igiya ne, ko kun ruɓe akwai ranarku. Matasan yau kuwa man kaza ne, in rana ta yi su narke.

Ta’aziyyar Kaftin Umaru Ɗan Suru

December 29, 2018 0


Na rubuta wannan waƙa ranar Talata 11 ga watan Disamba na shekarar 2012. Na yi ta ne a Sakkwato. A lokacin ina aiki a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato Nijeriya.

Friday, December 28, 2018

Anya Dai! Mu Taka Sannu

December 28, 2018 0


Ga alama abubuwan da magabata suka hanga bisa ga nassohin bayyanar ƙarshen zamani sun yi kere a zamaninmu. Manya da ƙananan alamomin tashin duniya sun yi wa zamaninmu dumudumu. Maƙasudin wannan waƙa jawo hankalin masu hankali a kan sake bitar waɗannan abubuwa da idon basira. Ganin irin nisan da muka yi ya sa na kira mu da muryar: Anya Dai! Mu Taka Sannu. Na rubuta ta ranar alata, 28-01-2014, 11:38pm, a Katsina.

Katsina: Rumfar Hausa, Gamji Matattarar Tsuntsaye

December 28, 2018 0


Burin wannan tattaunawa fito da irin gurbin da ke ga Katsina da Katsinawa a farfajiyar karatun Hausa, a duniyar ilimin Hausa jiya da yau. An waiwayi gurbin ƙasar Katsina cikin ƙasar Hausa da dangantakarta da sauran ƙasashen da Hausawa ke bugun gaba da su. An ƙyallaro haihuwar boko, da yadda Katsina ta agaza wa naƙudarsa, da karɓar biƙinsa da yayensa. Gudunmuwar fitattun marubutan adabi irin su Alhaji Abubakar Imam da takwarorinsa, da addibbai irin su Shata, an kakkaɓe mata ƙura. An harari manyan makarantu bakwai da ke agaza wa karatun Hausa a Katsina. Takardar ta yi nazarin yadda Katsina ta ƙwace kambun karatun Hausa daga shekarar 1967-2014...

Shugabancinmu Da Cigabanmu: A Tsarin Ƙasarmu

December 28, 2018 0

Mahalicci halitta da Ya nufi ƙaga halittocinSa da Ya shimfiɗa su a duniyarmu da muke zaune, a kan tsarin shugabanci ya tsara abinSa. Buwayayye Ya wanzu gabanin kowa da komai. Tun a nan, mai hankali ya san ana karantar da shi muhimmancin gabaci. Ya mamaye komai da komai bayan da Ya halicci komai da komai. A nan, ana yi muna hannunka mai sanda, ga martaba irin ta gabaci. Zai ci gaba da wanzuwa bayan fakuwar duk wani wanzajjen abu a bangon duniya. Wannan ishara ce ta tabbatar mana da cewa, umurnin gabaci na aiki da furuci sun cancanci su soke aiki da furucin duk wani….

Tsakanin Kabi Da Sakkwato: Kar Ta San Kar Aljani Ya Taki Wuta (Daular Kabi A Ma’aunin Bakandamiyar Buda Ɗantanoma)

December 28, 2018 0Farfajiyar ƙasar Hausa tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin Bahaushe: Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[1][1]. A Kano, Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir, Jangwarzo ya hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna fintinkau. A Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin wannan takarda kallon Daular Kabi a dunƙule, tare da baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar bakandamiyar mawaƙin masarautarsa Buda Ɗantanoma mai take: “Gagara Ƙarya Sadauki; Sama Gwarzon Alƙali”. Alƙiblar nazarina ba ta rena...

Ido Mudu Ne, Ko Bai Ci Ba Ya San Abin Da Ke Cika Masa Tumbi

December 28, 2018 0


Ƙoshin lafiya shi ne makamin farauto kowane irin amfani a rayuwa. Wadataccen hankali shi ne maganaɗisun zamantakewa. Ilmi wani babban gamji ne na hutawar masu lafiya da hankali, domin more abubuwan da lafiya da hankali suka kalato. Haƙiƙa, biri ya yi kama da mutum, a tarihin farfajiyar ƙasar Illela, ba a taɓa taro na nuna farin ciki a kan samun ƙoshin lafiyar mutanen Illela ba. Ko shakka babu, ba mu taɓa taruwa a Illela ba domin bukin kasancewarmu masu hankali. Cikin…….

Gaskiya: A Tunanin Bahaushen Karin Magana

December 28, 2018 0


Tunanin Bahaushe na faɗar: “Lokacin abu a yi shi,” wata babbar makaranta ce mai fannonin karatu da yawa. Ga al’adar ɗan Adam, kowa na son gaskiya, don haka dukkanin fafutukar ɗan Adam a duniya, gaskiya yake yi wa ita. Ma’anar gaskiya a kowace al’umma bai saɓa ba. Ɗan yunƙurin da nake son in yi shi ne, leƙo inwar gaskiya cikin wani ɗan sashen adabin baka wato “Karin Magana”. Kayan cikin tunanin Bahaushen Karin Magana suna da dangantaka ta ƙuƙut da al’adarsa da tunaninsa a duniyar zamaninsa. Ganin irin halin da ƙasarmu take ciki, na ƙoƙarin

Barazanar Zamani Da Mutuwa Ga Harshen Hausa

December 28, 2018 0Hausawa na cewa zamani riga ce, wanda ya ƙi saka ta ya kwana huntu. Daga cikin wasiyyar marigayi Muhammadu Hambali Jinju akwai bincike, rubutu da talifi. Wanda duk ya zauni Farfesa Hambali zai san mutum ne mai kama jiki, mai kishin Hausa da Hausawa, mai ƙwazon ganin Hausa ta ci gaba, mai sha’awar koyar da Hausa da Hausa, mai ƙoƙarin ganin an fassara wasu ayyuka na wasu ilmuka zuwa Hausa domin amfanin Hausawa. A koyaushe  yakan gaya muna, ku kama jiki, ku yi bincike in mu ne yau, ba mu ne gobe ba. Yau 2014 maganarsa ta zama nashin ƙasa babu kure. Don haka nake son in jinjini wasiyar bisa ga barazanar zamani da mutuwa ga sha’anin bunƙasa da ci gaban harshen Hausa a duniyar karatun boko.

Mathematical Heritage In Hausa Number System: (A Proposal for TeachingMathematics using Nigerian Languages)

December 28, 2018 1


The main objective of this research is to study the relevance of indigenous languages in teaching science education in Nigeria. The paper is very particular to the teaching of Mathematics in Hausa language in the predominant Hausa speaking community (northern Nigeria). In its purview, the paper specifically concentrates on numerals and numbers in Hausa counting system. It is common knowledge that in the field of Mathematics, numbers are among the basic ingredients in Mathematical operations. In order to strengthen the arguments enunciated in this paper, ten international languages were selected. The languages are; three European languages (English, French and German), three African languages (Arabic, Fulfulde and Zarma) and three Nigerian languages...

Hausa Culture And Islam: A Letter to Hausa-Muslim Youth of Today and those yet Unborn

December 28, 2018 0

In human history, there will be no progress without readiness. If yesterday was history, today will soon be a story by tomorrow.  To balance the equation of our development, we must know our past, be conscious of our present, to get ready for tomorrow’s challenges. The so-called sophisticated scientific and technological advancements of the modern world of the 21st century stated from time immemorial with series of modification and amendments before it reaches the level of its present state. This is directly telling us, whatever we named modern “today” passes through the ancient period of what we called tradition, norms, folklore or culture before it is scientifically....

Thursday, December 27, 2018

Malammai

December 27, 2018 01.                 Ni kiri Rabbana Jalla mai iko sarkin sarauta duka,
Sarkin nan da yay yo dare rana sammai da ƙassai duka,
Wanda Ya ƙaddaro rayuwa mutuwa ikonSa ce Maiduka,
Ba makawa ga bayi kiranKa buwayayye gwanin ɗaukaka,
          Mai ilmin da ya kewaye komai da saninSa yat tabbata.

2.       Nasa sani gwani fil azal yake komai ba ya ɓoye Masa,
          Babu kure bale mantuwa wane wahami ya riskan masa,
Shi yat tsara kaiNai da ilmiNai haka mun ka iske masa,
Ba ma shisshigin binciken ilminKa da istiwa’i bisa,
  Ɗan ilminmu bai kai ba, in mun ce mu yi, nan yake barkata.

3.       Don haka mumini ba ya ɗanga ba ya bugun gaban ya sani,
Taka sannu Modibbo, hayya da cewa: “wane mi yas sani”,
Allah Ya faɗa ba sani tari a cikinmu sai ƙanƙani,
Wanda ka taƙaman ya iya ƙarshe sai ya yi da na sani,
  Bil’amu yak karantar da mu masani duka bai wuce karkata.

Lokacin Abu A Yi Shi In Ana Son A San Shi

December 27, 2018 0


1.                 Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay yi komai a lokacinai,
Yay yi hukunci bisa yardaTai,
     Ga lokaci wa ka karkare shi?.

2.                 Bisa yardaTai ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u Ya yi,
Da fasullan shekara da yay yi,
     Na lokaci ba a gurgasa shi.

3.                 Shi dai waƙaci a kiyaye shi,
In ya zo ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya gurgusa shi,
     Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.

Zaɓi Abokin Zama

December 27, 2018 0


1.       Da sunan Ilaahu gwani karatu ya fara,
          Tsaya ɗan’uwana ga salati mu ƙara,
Buƙata mu samu tabarraki gun Tabara,
          Zaman duniyarmu da lahira mun biɗe shi.

2.       Karatunmu yau ga zaman abota ya raɓa,
Kiyaye zama bisa ƙa’ida kar a saɓa,
Da hulɗa da zance kar a kwaso a kwaɓa,
          A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.

3.       Abota zaman yarda da ƙauna aminci,
Ka cuɗanni in cuɗe ka ne ba butulci,
A baki da zuci a jittu shi ne zumunci,
          A koyaushe ɗaya ƙaunar yakai ɗaya ya gan shi.