Sunday, November 25, 2018

Usama Bn Laden: Gwarzo ko ɗan Yaƙi? (Laluben Ma’aunin Gwarzo a Hangen makaɗan Hausa)Maƙasudin wannan bincike shi ne, tantance yadda Bahaushe ke kallon jaruntaka da yadda Bature ke fassara ta’addanci. Takardar ta yi garkuwa da Usama bn Laden ta fuskar yadda duniyar Turai ke kallonsa. An yi ƙoƙarin ɗora gutsattsarin maganganun Turai kan Usama ta fuskar zarginsa, da farautarsa, da cewa da suka yi, sun kashe shi, a ma’aunin awon jaruntaka a Bahaushen hankali. Na yi ƙoƙarin laɓewa ga zantukan mawaƙan baka domin su mutane suka fi sauraro, kuma su maganganunsu suka fi naso a zuciyar Bahaushe. Don haka, na gayyato mawaƙa fitattu shahararru goma sha ɗaya su raka ni a fahinta. An tsinto ɗiyan waƙa ashirin da huɗu daga cikin waƙoƙinsu domin yi wa bayanai nagartaccen turke. An zaɓo mawaƙan daga rukunin mawaƙan sarauta da mawaƙan maza da mawaƙan sana’a da….

                 
Usama Bn Laden: Gwarzo ko ɗan Yaƙi? (Laluben Ma’aunin Gwarzo a Hangen makaɗan Hausa)

---------------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
----------------------------------------------

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Juli, 2011

Tsakure
Maƙasudin wannan bincike shi ne, tantance yadda Bahaushe ke kallon jaruntaka da yadda Bature ke fassara ta’addanci. Takardar ta yi garkuwa da Usama bn Laden ta fuskar yadda duniyar Turai ke kallonsa. An yi ƙoƙarin ɗora gutsattsarin maganganun Turai kan Usama ta fuskar zarginsa, da farautarsa, da cewa da suka yi, sun kashe shi, a ma’aunin awon jaruntaka a Bahaushen hankali. Na yi ƙoƙarin laɓewa ga zantukan mawaƙan baka domin su mutane suka fi sauraro, kuma su maganganunsu suka fi naso a zuciyar Bahaushe. Don haka, na gayyato mawaƙa fitattu shahararru goma sha ɗaya su raka ni a fahinta. An tsinto ɗiyan waƙa ashirin da huɗu daga cikin waƙoƙinsu domin yi wa bayanai nagartaccen turke. An zaɓo mawaƙan daga rukunin mawaƙan sarauta da mawaƙan maza da mawaƙan sana’a da fanɗararun mawaƙa (makaɗan sata). An share fagen nazari da gabatar da ma’aunin gwarzo a al’adar Bahaushe ta fuskar gabatar da sunaye ashirin da Bahaushe kan kira gwarzo/jarumi da su. Daga nan aka gabatar da makaman tantance gwarzo irin su suna (fice), da karɓar taron dangi, da rashin tsoro da rashin raki da wuce gudu. An kakkaɓe wannan bincike da fito da burin kowane gwazo a rayuwarsa cikin gwagwarmayarsa. Haƙiƙa, akwai buƙatar shugabannin duniya su san, kasancewar duniya gida ɗaya a kimiyyance, ba shi ne kasancewarta gida ɗaya ba a fahinta. Yadda yatsun ɗan Adam suke, haka fahintocinsu suke. Yadda rana da wata ke saɓa wa juna, tunanin ‘yan Adam da hasashensu ya zarce haka. Idan haka ne, ina laifin faɗan da ya fi ƙarfinka ka mai da shi wasa?
Madalla da Makaɗa Ɗan’anace da ke cewa:
Jagora: Waye idonka Audun wawa,
          : Ba kai ɗai an ka fara wa sababi,
          : Ko ka yi dariya ba komai.

Gabatarwa:
Hausawa kan ce, lokacin abu a yi shi. Rashin gwama darusanmu da abubuwan da ke aukuwa a duniya zamaninmu wani cikas ne ga basirarmu da ci gabanmu. Abubuwan da ke aukuwa a duniyar zamaninmu sun shafi kowane irin darasi da muke koyarwa domin daidaita akalar bincike da karatu. Domin samun makamar sanin rayuwarmu ya sa ƙasashen Turai suka buɗe kafafen yaɗa labarai irin su BBC, VOA, Jamus, da dai sauransu. Ko kusa, bai kamata a bar mu a baya ba wajen auna nauyin abubuwan da ke aukuwa a zamaninmu da darusan da muke koyarwa na harshenmu. Idan muka tashi tsaye, muka yi wa abubuwa susa gurbin ƙaiƙai darusanmu za su gwada tsawo da kowane irin darasi da ake koyarwa a jami’o’in duniyarmu. Maƙasudin wannan rubutu shi ne, auna nauyin gwarzo da ɗan ta’adda a Bahaushen sikeli ta bakin masana harshe (mawaƙa). Na zaɓi yin haka domin abokaina ɗalibai su san, kowa da buƙin zuciyarsa maƙwabcin mai akuya ya sai kura. Don haka, kowane mutum na da ‘yancin kallon abubuwa ta fuskar al’adarsa.

Taƙaitaccen Tarihin Usama Bn Laden:
An haifi Usama bn Laden a Jedda, Saudi Arebiya ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, 1957, a babban gida na daraja da arziki. Mahaifinsa fitaccen tajiri ne, sanannen ɗan kasuwa, amintaccen ɗan ƙasa. Usama shi ne ɗa na goma sha bakwai ga Laden mahaifinsa. Usama ya yi ilmin addinin Musulunci sosai ya kuma karance boko farin karatu a fannin fasahar zayyanar muhalli. Mutum ne mai kamun kai da kawarci da kishin addininsa matuƙa. Yana da mata uku da ‘ya’ya fiye da ashirin. Gidansu sun mallaki tsabar kuɗi na jari fiye da dala miliyan ɗari huɗu ($400million).
Kasancewarsa wayayyen ɗan kishin addini ya yi hulɗa da ƙasashen duniya da yawa kamar Sudan da Misra da Afgan da Syriya da UK da France da makamantansu. Ya fara hulɗa da ƙasashen Turai a shekarar 1979. Ya haɗa ƙarfi da Amurka (US) aka gargaɗi sojojin Rasha aka yaƙe su suka fita daga mamayar da suka yi wa Afganistan. Da ya ci nasarar haka, ya kafa cibiyarsa ta jihadin kare addinin Allah da masu yin sa a shekarar 1988. Da dakarun Rasha suka miƙa wuya bori ya hau a shekarar 1989, ya koma Makka da zama. Daga Makka ya sake fita zuwa Syria a shekarar 1990. Da Gwanatin Saudiyya ta gayyato sojojin Amurka a ƙasarta, sai Usama ya yi hijira zuwa wata ƙasa. A shekarar 1994 Gwamnatin Saudiyya ta soke sunansa daga cikin ‘yan ƙasarta. Daga nan ya koma Sudan da yammacin Misra (Masar) yana kai da kawo.
A rahotannin Gwamnaitn Amurka, Usama ya fara yaƙar ƙasarta da masoyanta da masu jin tsoronta a shekarar 1995. Daga wannan shekarar Gwamnatin Amurka ke ganin cewa, lallai Usama ne ya yi tsare-tsaren ta’addancin:
i)       Hari a ofishin jakadancinta a shekarar 1996.
ii)      Harin da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka a Kenya a 1998.
iii)     Harin da aka kai wa jirgin yaƙin ruwan Amurka a Tanzaniya 1998.
iv)     Harin da aka kai wa Yemen, 2000.
Tabbas, Usama ya fito ya gaya wa duniya cewa, waɗannan aika-aikar duk ba ya da hannu a ciki. Duk da haka, Amurka ta ba da tukuicin dala miliyan biyar ($5 million) 1999 ga duk wanda ya kawo mata shi. Bayan shekara biyu, 11 ga Satumba, 2006 aka kai mummunan hari a Cibiyar Kasuwancin Duniya da ke Amurka, Usama ya zama wanda ake tuma na farko. Don haka, aka sake ba da ladar dalar Amurka miliyan ashirin da biyar ga wanda duk ya kawo shi a raye ko a mace. Da kyautar ta kasa ciyuwa a shekarar 2011, shugaban ƙasar Amurka Obama ya yi sanarwa sun kashe shi a ƙasar Pakistan.
Idan har a Pakistan aka kashe shi a shekarar 2011, ya mutu yana ɗan shekara hamsin da huɗu (54) a duniya. Idan kuwa hirar da aka yi da shugaban ƙasar Pakistan Musharraf a shekarar (wajajen 2005) a CNN da BBC ta tabbata, Usama ya yi shekara shida da rasuwa a yau 2011, domin ya ce cutar ƙoda ta kashe shi a shekarar 2005. Idan kuwa sakamakon muhawarar majalisar Amurka za a ɗauka, ba a kashe Usama ba, har yanzu tana ƙasa tana dabo. A ra’ayin masu fashin baƙin al’amurran yau da gobe na duniyar zamaninmu, suna ganin sanarwar kashe Usama da Obama ya yi, wani majigi ne aka shirya na yaudarar ‘yan kallo da ya ci nasarar sace hankalin masu ganin Amurka na iya komai, ga su nan dai.

Ma’aunin Gwarzo A Hausance:
Awon gwarzo a idon Bahaushe ya ƙunshi abubuwa biyu: na farko shi kansa gwarzon da aka son tabbatar da gwarzantakarsa, na biyu abubuwan da ya yi da suka tabbatar da zamansa gwarzo. A ma’aunin Bahaushe, ba dole sai gwarzo ya zama jibgegen ƙaton ba, domin sanin ba girma ba dominsa ba azaba. Haka kuma, ba dole sai gwarzo ko jarumi ya buwayi kowa duniya ba, domin makashi maza, maza ke kashe shi. A ganin Bahaushe abubuwan da gwarzo ya aikata za a bi diddiginsu a tabbatar da, ba su saɓa wa daidaitacciyar al’adar rayuwar Bahaushe ba. Idan mutum ya ci nasarar hawan waɗannan matakai na Bahaushe, za a iya ɗora shi a kan kalmomin yabo na nuna tabbacin kasancewarsa gwarzo/jarumi.
Idan sunan mutum ya gota na tsaran zamaninsa. Ya rinjayi na abokan gwagwarmayarsa. Ya gagari na abokan adawa. A al’ada ko da bai fito ya yi kirari ba, za a ji ana yi masa kirari ko ana yabonsa da kalmomi irin su: Namiji, Jarumi, Gwarzo, ɗa, Sadauki, Dakare, Kasko, Katakore, Wandara, Zaki, Giwa, Barde, Gaƙi, Ɓaleri, Buwaye, Gagara Kundila, Gagara badau, Giye, Makaye, Jigji, waɗannan kalmomi ashirin da aka zaɓo ba su kaɗai Bahaushe ke yi wa gwarzo/jarumi kari da su ba, na kawo su a matsayin misali kawai. A ganin masana al’adar Bahaushe, abubuwan da Turai ke danganta wa ga Usama Bn Laden maimaikon su ci fuskarsa da mutuncinsa, sai su daɗa ƙara masa lamba ga idon wasu al’ummomi na duniya musamman Afirka.

Usama Bn Laden Da Ta’addanci:
Laluben tushen kalmar ta’adda a harshen Hausa wani abin so ne ga irin wannan nazari. Wasu masana na hasashen tushenta daga Larabci ne, watau, “ta’ad” wanda nassoshin Alƙur’ani da Hadisai da dama suka ambata. Wasu masana na ganin, tun kafin a haifi uwar mai sabulu belbela tana da farinta. Don haka, kalmar “ta’adda” Bahausa ce kai tsaye, tushen ta daga “ta Adda” ne, wani Bafadan Sarkin Kano. An ce, sunan Bafaden “Adda”. An sa ya kira wani talaka cikin hushi, ya tafi da gatari ya sassare shi, ya zo da gutsattsarinsa ya ce wa sarki, ga aikinka an cika. Tun daga wannan lokaci, idan za a tura wani bawan sarki aiki akan ce, kar ka yi irin, “ta Adda”, watau yadda Adda ya yi wa wancan talaka.
Idan aka rairaye waɗannan ma’anonin za a ga: A nassoshin shari’a ta’addanci na nufin, wuce gona da iri, zarce makaɗi da rawa, shisshigi, ƙetare haddi, wanzar da ɓanna da fasadi da bala’i da waba’i da hasara da rashi da taɓewa mai haifar da salwantar rayuwa, da dukiya, da hana wa zaman lafiya da lumana gindin zama, da share wa ƙaddara da hasara fagen miƙe ƙafafu. Irin wannan ma’anar ta yi canjaras da yadda Turai da duniya ‘yan boko ke kallon ta’addanci. A can da, mai irin wannan rayuwa shi ne ɗan yaƙi mai son a koyaushe ana fitina da faɗa da yaƙi.
Wurin da gizo ke saƙa a nan shi ne, ma’anonin da Turai ke bai wa ta’addanci a yau haka yake, ko yana son gyaran fuska? Babu shakka, duk abin da zai ta da zaune tsaye, babu mai hankalin da zai yi na’am da shi. Duk da haka, ya kyautu a gano abin da ya sa na zaune ya tashi tsaye domin shi ne, Kafurkafur zakaran tsafi wanda ya fi kafiri kafirci. Makaftar da duniyar ‘yan boko ta yi ga zurfafa bincike a kan haka, shi ya sa fassararsu ta ta’addanci ta mamaye duniya aka wayi gari a yau aka yi, kamun kurar kurma, kura kuka, kurma kuka. Da wannan fassarar ta’addanci haka take a kan waɗanda ake kira ‘yan ta’adda a yau, da ba za a samu mai mara musu baya ba. Wa zai so mutuwa? Wa zai so ya kashe wani rai da gangan? Wa zai yi so hasara? Wa zai so rashin zaman lafiya? Wa zai so fitina da yaƙi da hayaniya da hayagaga?
Kalmar “ta’addanci” ta yi kusan ta shige wa Bahaushe duhu domin ta tsufa ƙwarai har an yi kusan a manta da ita. Kalmomin hari, farmaki, alkafura da ƙundumbala sun mamaye haskenka. Harin da aka kai wa Amurka da jiragen sama biyu a watan Satumba, 9/11 watau 11/9/2006. Amurka ta yanke hukuncin Usama bn Laden ne jagoran harin. Da haka aka zartar da hukuncin kisa a kansa da yaƙar duk wata ƙasa mai zaman mutunci da shi. Bisa ga wannan zato Amurka ta dinga amfani da kalmar “ta’addanci” ga Usama da duk wani mai kama ko sifa ko ra’ayi irin na Usama ido rufe. Ba burina bitar harin da aka kai ba, domin masana sun yi rubuce-rubuce da yawa a kai. Burina a nan shi ne, yadda gargajiyar Bahaushe ke kallon yadda Amurka da Turai ke nuna Usama. Haka kuma, yadda Turai ke farfagandar fallasa Usama ya taimaka wajen jawo wa Usama farin jini da ƙauna da so da yarda a zukatan ma’abota addini irin na Usama a bangon duniya. Idan a ganinsu Usama ɗan ta’adda ne, a ganin wasu gwarzo ne, jarumi ne, sadauki ne, domin:
i)                   Ba a bayyana wa duniya laifin da ya yi ba, yaƙarsa kawai ake yi;
ii)                An kasa a kama shi da hannu kamar yadda aka kama wasu shugabannin ƙasashen duniya da aka yaƙa;
iii)             Ya ƙi ya miƙa wuya bale a yi masa tuannuti;
iv)              An kasa gano wurin da yake, duk da barazanar cewa, duniya a hannunsu take;
v)                Bai rufe bakinsa ba tun ranar da aka fara yaƙi da shi har ranar da aka ce, ƙila an kashe shi,
vi)              Abubuwa da suka gudana lokacin da aka ce an kashe shi, sun ƙara sa wasu mutane yanke shawarar lallai dai gwarzo ne ba ɗan ta’adda ba;
vii)           Cece-ku-ce da suka wakana bayan da aka ce an kashe shi sun ƙara sa mutane jin tsoron rahotannin da kafafen yaɗa labarai na Turai ke bayarwa.
A kan waɗannan abubuwa bakwai na so in ɗora tunanin Turai da tunanin Bahaushe a kan matsayin Usama bn Laden a mahangar Bahaushe. Zan taƙaita bayanan a kan abubuwan da Turai suke faɗa a rubuce-rubucensu a kan Usama bn Laden.

Asali:
Bahaushe na ganin, asali wani babban abu ne a rayuwa. Mutumin da ba ya da asali nagari ba zai yi nagartaccen aiki ba. Mai asali nagari ana sa ran ya yi aiki nagari. A faɗar Amurka Usama ya tashi wadataccen gida babba. Gidansu shahararrun masu kuɗi ne ‘yan kasuwa ne da duniyar zamaninsu ta san da su. A wajen uwa da uba da kakani son kowa ƙin wanda ya rasa. A ganin makaɗa Ɗan’anace tun a nan ake samun ɗan ƙwarai wanda Hausawa ke ce wa “ɗa”. Ga abin da ya ce:
Jagora:Mai son miya ya auri tsohuwa,
          :Mai son shimfiɗa ya auri budurwa
          :Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.

Suna:
A al’ada Hausawa na cewa, suna linzami ne, wannan linzami idan mutane da yawa suka ja shi ya fi ɗaukaka. Maimakon Amurka ta yi ta fama da yaƙin sunƙuru har sai ta gano waɗanda suka yi mata ta’addanci, sai ta cire mutum ɗaya, ta ce shi ne. Masu goyon bayanta da masu ra’ayinta da masu tsoronta suka mara mata baya. Cikin ɗan lokaci kaɗan sunan Usama ya fi na Amurka da dukkanin tarayyar Turai ɗaukaka a duniya. Da ma Narambaɗa na cewa:

Jagora: Da ƙauye da birni,
          : Na buƙatar ganin dokin ga,
          : Da yay yi suna,
Yara  : Ga talitta komiy yi suna,
          : Ana tilas shagalin ganinai,
Gindi: Ɗan Mallam ci ƙwallo sarkin gudu,
          : Na yarda da ɗan Hilinge.

Taron Dangi:
Yadda aka gudanar da farautar Usama da jama’arsa na taron dangin sojojin duniya abin lura ne ga Bahaushe. A ƙa’idar Bahaushe, da Balarabe, a fagen daga an fi son a yi ɗai bayan ɗai, gudu guda domin a gane gwarzo, ai don haka ne Ɗan’anace ke cewa Shago:
Ɓaleri ba guda da guda ba”.

A ganin Bahaushe, sai an yi gaba-da-gaba za a gano gwarzo. Don haka ne, Sani Aliyu Ɗandawo ke cewa a waƙar Hashimu:
Jagora: Harsashe makarinka a duka,
Yara: Amma ba gaba da gaba ba.

Idan aka yi wa mutum ɗaya taron dangi, ko an ci nasara a kansa kirari kunya ne domin kashin baƙi sai taro. Idan ko har ya tsaya ya yi daga da su, ya zama gwarzo ko an so, ko ba a so ba, dubi yadda Narambaɗa ke yabon sarkin Kwatarkwashi Alu da cewa:
Jagora: Ba shawagi sa maza yawon duniya,
Yara  : Suna sai da abin hwaɗi ga ‘yan’uwa.
Gindi: Yai halin mazan jiya
          : Ɗan Sanda mai Kwatarkwashi.

A ma’aunin Bahaushe, gwarzo da dubu yake yaƙi ba da mutum ɗaya ba. Fitaccen gwazon nan Janborodo da sarkin Gwandu Halilu ya yi wa waƙa, Sambo Wali ya yi mata tahamisi cewa yake yi:
“Dubu kaka taryewa su kasa wurin zuwa,
Baka da baka doki da doki ka ta ruwa,
Ka kwana cikinsu gaba gaƙi babu garkuwa”.
Idan gwarzo bai kai haka ba, yana da saura, ko da kuwa gwarzon sata ne, kamar yadda Gambo ke wasa Manu Dahin Gumbire cewa:
Jagora: Ko bataliyas soja,
          : Tas shiga daji in gaya maka,
          : Manu Dahi na ɗan taya ta.

Artabo:
Ga alama, idan dakarai suka yi wa gwarzo taron dangi, ba makawa sai an gwabza. Saɓanin al’adar Turai da ta Bahaushe, da an yi wa mutum ɗaya taron dangi an nuna ya buwaya. Idan haka ta auku, buri ya cika an yi ban kwana da duniya, an ce wa lahira, salamu alaikum. Idan abu ya kai gargare haka, suna ya ɗaukaka, an hau buzun zama gwarzo, sai a yi haƙuri da wuya, a fuskanci maza gadan-gadan komi taka zama ta zama. Dubi yadda Narambaɗa ke gaya wa sarki Ibrahimu:
Jagora: Riƙa da gaskiya Ibrahimu,
          : Mai taimakon Allah na nan,
Yara  : Zan ka wa maza gurmani,
Gandi: Madogara na Mallam Iro
          : Uban Yari mai gida Shinkafi.

Da an fara ba hamuta iska, batun sulhu da ban haƙuri ya ƙare. Da dai Turai sun fahinci haka, da ba su yi tunanin fara yaƙi ba. Da an fara yaƙi an rufe ƙofofin tunanin tausayi da tausayawa. Haka kuma, kowane gwarzo so yake kowa ya ɗebo da zafi ya sa bakinsa irin yadda Narambaɗa ke ce wa Sarki Ɗankulodo na Maraɗi:
Jagora: Gadan-gadan na Maiɗaki
Yara  : Mai kwana wurin da yas so shi kwana.
Jagora: Awartaki riƙa ko da zahi
Yara: Sauran maza ka mai she su mata.
Gindi: Ciwon cikin maza Ɗankulodo.
          : Na Yari mai halin Tcagarana.

Babu wani jarumi da zai yarda ya je fagen yaƙi ba da shirin mutuwa ba, domin ya san, ɗayan biyun ne, in a dawo, in a mutu can. Rinjayar da mutuwa ya sa Bahaushe ke gani, gwarzo shi ne wanda a fagen artabu an yi haihuwan guzuma ɗa kwance uwa kwance. Idan aka yi kirarin bindigar ‘yan tauri, ke gawa, mai ke gawa, abin da an ka nuna gawa, gawa uku jere ga juna, to, abu ya yi. Madalla da Kassu Zurmi da ke ce wa Nomau Namagarya:
Jagora: Kyawon faɗa a yo accakwama,
          : A kwaɓa ta baƙi ƙirin
          : Ta ƙare muku can.

A fagen artabo, samun accakwama ba ta’addanci ba ne, a idon Bahaushe. Idan kuma tsuntsun da ya kirari ruwa, ruwa suka ci shi ba a yi ta’addanci ba a fannin yaƙi. Rashin sanin haka ya sa Hausawa suka kasa fahinta Turai a kan yunƙurinsu na yaƙi da ta’addanci cikin salon ta’addanci. Idan aka bari magabta suka haɗa jiki, to, za a ga abu uku sun kau ga gwarzo da jarumi watau tsoro da raki da gudu.

Tsoro:
Gwarzo shi ake tsoro, shi ke ba da tsoro, shi ke sa raki, shi ke sa a ruga a guje. A halin da muka ciki, duk da ganin da Turai ke yi ta gama da tarihin Usama Bahaushe bai ganin haka, tsoron Usama na nan a ƙirazansu har abada domin gwarzo ne. Tsoron da suke ji na Usama a ganin Bahaushe, shi ya ba Usama darajar zaman gwarzon wannan ƙarni, kamar yadda Narambaɗa ke gaya wa Sarkin Gobir Amadu cewa:
Jagora: Jikan Bubakar ba su tsoro,
Yara  : Waɗanga mazaizai na yau
          : Babu mai imai,
Gindi: Amadun Bubakar gwarzon Yari,
: Dodo na Alkali.

Idan aka yi wa namiji taron dangi, ya ƙi ya nuna razana ya cika namiji. A koyaushe, mai yi wa gwarzo kirai yana son ya ɗebe tsoron mutuwa da wahala a zuciyarsa (gwarzo). Dubi yadda Gambo ke kiran tauraronsa da cewa:Gambo: Mi kaka shakka,
          : Ga ni ga ka,
          : Ɗauri ka ka shakka ko kashewa?

Idan namiji ya kantare wuri ɗaya, ya yanke shawarar ga abin da zai yi, to ba ja da baya bale neman shawara. A ko’ina gwarzo yake, idan ya tsai da ƙafarsa wuri ɗaya, sai dai a mutu. Narambaɗa ya ba mu wannan fatawar da yake cewa:
Jagora: Dus sarkin da kas sani,
          : Basaraken da kas sani,
          : Amadu ya hi shi ƙane shiryayye,
          : Babu batun banza.
Yara: Kuma babu sakewa,
          : Kuma in yai tsaye,
          : Ba mai kausai”.
Gindi: Na riƙa ka da girma,
          : Audu ƙanen mai daga,
          : Kan da mu san kowa,
          : Kai mun ka sani Sardauna.
Raki:
Hausawa na cewa, kowa ya ce, ya ce sai ya ce, bai ce ba. To, faɗar ba a ce ba, shi ne raki. Namiji ko an fi shi gaskiya a fagen artabo, tsaye yake yi ya kare ‘yar gaskiyarsa, ba da razana ba, bale raki ko a doka ya kauce, ko ya zuƙe, ko ya kasa rama duka. A kiɗin sata Gambo ya fito da wannan hasashen lokacin da aka koro Bawa Makau garin Gumi ana jifa da duka Gambo ya ce:
Gambo: Ko kan da akai,
          : Mugun mijin ƙasa,
          : Ya kashe kanu sun yi maitan.

Haka ma, a cikin waƙar Hantsi Hore (ɓarawon damma) da aka zuga shi ya je ya sato hatsin mutane aka koro shi, ga abin da makaɗa yake cewa:
Gambo: Hancti shi jefa,
          : Su su jefe shi
          :Har aka zo hilin kiɗinmu.
Maƙasudinmu a nan shi ne, gwarzo ba ya miƙa wuya kamar akuya. Tattare da taron dangin da Turai suka yi wa Usama, ya ƙi ya ba da kai bori ya hau wanda a ganin Bahaushe haka gwarzo ya kamata ya yi, komi taka zama ta zama. Da ba a yi tunanin yi masa taron dangi ba, da za a ci nasara idan aka fuskanci Bahaushe da bayanin Usama a matsayin ɗan ta’adda. Ga al’ada ko akuya aka matsawa tana cizo. Idan tura ta kai bango babu wane na san wane. Rashin tsayawa a kula da ire-iren waɗannan shi ya sa har yanzu Amurka ba ta gamsar da Bahaushe ba a kan bayanin Usama.

Gudu:
Haƙiƙa, a bayanan Bush na farkon a yaƙin ya nuna, Usama ya gudu, ya tsere, ya ɓoye. A maganar al’ada gudun abin kunya ne ga gwarzo. Abin lura a nan shi ne, idan gwarzo ya yi gaba da gaba da abin da yake tunkara, nan ne gudu yake akan kunya gare shi a al’adance. Yaƙi a abokan yaƙi sun fi duba, a ko’ina gwarzo ya garzaya ba guda ya yi ba, farmaki ya je kai. Da, da mutum ɗaya suke faɗa, kamar dambe ko kokuwa, to nan kam gudu ya zama kunya. Alhaji Muhammadu Narayau (makaɗin Dambe) a waƙar wani tauraronsa Almu yana cewa:
Jagora: Kai dai ban da gudu,
          : Ko na gangara gebe na,
Yara : Ko da mutuwa za ta zo ta kwasa.
Gindi: Ya sa maza leɓewa
          : Almu ‘yan maza ka tsoro.

Ranar Wanka Ba A Ɓoyon Cibi:
Abin da ya ba ni sha’awar rubuta wannan takarda shi ne, karatun rahoton kashe Usama da Amurka da Pakistan suka wallafa a intanet. Daga cikin abubuwan da suka faɗa sun haɗa da cewa:
i)                   Sun tarar da Usama cikin gida da iyalansa
ii)                Da aka kai masa farmaki, ya ƙi ya miƙa wuya.
iii)             Matarsa ta ƙi ba da haɗin kai, aka harbe ta ga ƙafa.
iv)              Sojojin Amurka da na Pakistan suka kai harin a gidansa na Islamabad.
v)                An harbe shi ga kai, wajen idonsa ta dama, aka kashe shi.
vi)              Sun isa gidansa da ƙanana jirage sama uku, ɗaya ya lalace aka yi amfani da biyu.
vii)           An ƙi a nuna gawarsa, saboda irin munin kisar da aka yi masa na iya haifar da wata sabuwar fitina.
viii)         Ya ƙi aminta da ya yi saranda ya miƙa wuya (kamar akuya), shi ya sa aka kashe shi.
ix)              An saka gawarsa teku bayan an yi masa salla.
x)                An kama iyalansa, ana ci gaba da bincike.
Waɗannan abubuwa goma su suka fi shahara a kan bayanan kisan Usama. Ga mai hankalin nazari, akwai abubuwan cewa da yawa a ciki, da yake ba su suka dame mu ba, za mu mayar da hankali a kan zuciyar takardarmu. Rahotannin da Amurka ta bayar kan kisan Usama a ganin Bahaushe kamar kirari ne ta ke yi wa Usama na zamansa barde ba kushe shi take yi ba. Da ya yarda aka yi sulhu ko ya miƙa wuya kai tsaye Bahaushe na hangen wata kasawa a ciki.
Ga al’adar Bahaushe, kyawon gwarzo ya mutu ga hannun gwaraje irinsa don haka ne yake cewa, mutuwa kashe mutane ki mutu. Dan’anace ya warware wannan matsalar a waƙar Shago da yake cewa:
Jagora: Ta fi a kashe ka gaba ɗai,
          : Wandara mi kakai da rai ga arna,
          : Ai ko an kashe ka ban ji haushi,
          : Don ɓannar da kay yi ta aka gyara,
          : In ko ka kashe su ka yi gaba ɗai.

Fatar kowane gwarzo ya mutu a kan abin da ya yarda da shi. Idan da so ne samu a kai shi cikin kushewa da kayan faɗansa. Mutuwar Usama a fagen daga ba abin kushewa ba ne a wajen Bahaushe, ai Ɗan’anace ce wa Shago ya yi, da dai ya ja da baya ga mazajen fama a fage.
Jagora: Gara ka je lahira,
          : Kana da naɗaɗɗen hannu,
          : Ko can a samu abokin fama.

Rahoton Amurka ya nuna an yi musayar wuta ta ‘yan mintoci kamar arba’in, sabanin na Pakistan da ya ce, an yi awowi ana luguden aradu. A ma’aunin Bahaushe ko da minti ɗaya aka yi ana ɓarin wuta namiji ya yi namiji.

Buri Ya Cika:
Ga abinda Amurka ta nuna Usama ɗan ra’ayin riƙau ne na addinin Islama. Ita kuwa Amurka ‘yar ra’ayin riƙau ce ta damokraɗiyyar da ke takin saƙa da manufar Usama. A al’adance, ɗan Adam na son ya mutu a kan aƙidarsa ko da an rinjaye shi. Da dai Amurka ta samu sa’ar jawo ra’ayin Usama ya fahince ta, a ci gaba da tafiya tare, kamar yadda suke a da, da za a ce, ta ci nasara. Yanzu da yake an yi kare jini biri jini, ta ci nasarar riƙe aƙidarta, shi ko ya ci nasarar mutuwa da aƙidarsa. A ganin Bahaushe, a ci gwarzo da yaƙi a kama shi, shi ne kasawa, ba a kashe shi ba. Domin makaɗa Ɗan’anace ya ce:
Jagora: Yaƙi ya ci annabawa Shago,
          : Balle ɓaleri mai naɗe hannu”.
Gindi: Kai maza suka sauna,
          : Kiro maƙi gudu mai ban haushi.

Makaɗa Ɗankwairo ya ƙara wa takwaransa ƙarfin guiwa da cewa:

Jagora: Da wulaƙanci gara shahada,
          : Ga Musulmi ba illa ne ba,
Gindi: Ya wuce raini ba a yi mai shi,
          : Amadu jikan Bello Sadauki.

Wannan ɗan waƙar ya ci canjaras da waƙar Gatarin Ɗagutu a wani baiti da yake cewa:
“Shahada muke buƙata,
Ba dogon rai ga wanga tsari ba.”
An ce, a tarihin ƙasar Hausa an samu mazaje masu irin ra’ayin Usama a fagen yaƙi. A shekarar 1906 da Turawan taron dangi suka ci birnin Satiru ta ƙasar Ɗancaɗi Lardin Sakkwato da yaƙi mazajen Satirawa sun ƙi miƙa wuya a kama su kamar akuya, sun zaɓi shahada, Allah Ya yi wasu. Da turnuƙun yaƙi ya kai ya kawo, ga abin da turayen yaƙinsu ke cewa:
Taro: Marafa ya daɗe bai zaka ba,
          : Waziri ya daɗe bai zaka ba,
          :Balle Nasara mai ɗan wando,
:Babban mutum da wandon yara,
: Ku sa kiɗi mazaizai mu gani,
: Ko can gida faɗa mun ka sani,
: Ba mu san gudu ba sai dai a mutu.

Bukatar kowane gwarzo shi ne, in an ɗebi na gashi ya ɗebi na dahuwa, don haka, duk da yake an ƙona garin Satiru mai kimanin mutane dubu goma (10,000) su kuwa sun kashe sojojin Biritaniya tare da jagoran rundunar sojan Major M.G. Hillary don haka suke cewa:
“: Ko an kashe mu babu hasara,
: Ko yanzu mun kashe Hilleri”.

Ƙarshen wasan dai shi ne,+ burin kowa ya cika. Burin Amurka na dasa manufofinta a ƙasashen da ta ke da jin tsoron aƙidojinsu ya cika, burin Usama na samun shahada ya cika. Ƙarshen Turai a cikin saƙonninsu na taya Obama murna suna nuna masa, yanzu yaƙi yake, ba a ce komai ba, an raƙi baƙo ya dawo. Tabbas, da gaskiyarsu, domin makaɗa Ɗan’anace cewa ya yi:
Jagora: Bari murna karenka na kashe kura,
          : Wata rana ka tsinci bindi hanya.

Don haka, har yanzu sai an koma ga tunanin nan na Bahaushe a shafe jini a koma wasa. Dole sai an nemi wata hanyar zaman lafiya a duniya ba ta yaƙi ba. Babu yaƙin da zai iya ƙare duniya, kuma ba ta fuskar yaƙi kawai ake tabbatar da aƙidojin wasu mutane a kan wasu ba.

Sakamakon Nazari:
Ya kyautu a ce, majalisar Ɗinkin Duniya ta fito da wasu nagartattun hanyoyi na sasantawa tsakanin ƙasashe ba ta ƙarfin soja ba. Amfani da ƙarfin soje, bai taɓa kashe wuta sai daɗa turara ta a zukatan waɗanda ke ganin an ci da haƙƙinsu. Haka kuma, tilas, a daina harin bisa kan mai uwa da wabi wajen kwantar da tarzoma da zanga-zanga da tawaye. Bugun gaban da UN ke yi da Amurka shi ke harzuƙa wasu gwaraje su jarraba sa’arsu, in til, in kwal rinin mahaukaciya. Yin hukunci cikin duhu, da zartar da shi lulluɓe, wata hanya ce ta haifar da ta’addanci a duniyarmu ta yau.
Irin fafatawar da gwamnatoci biyu na Amurka Bush da Obama suka yi da Usama ta ƙara ɗaukaka shi bisa ga ɗaukakar da yake da ita a idon Musulman duniya. Maganar kashe shi kuwa wata sabuwar lamba ce aka ƙara danna masa duk da kasancewar ba a yarda sun kashe ba. A taƙaice, wannan fafitikar ta nuna da wuya mutum ya yi kirari da bugun gaba ya ci nasara ga abin da ya sa gaba.

Naɗewa:
Muradin wannan takarda shi ne, jawo hankali masu mulki cewa, duk abin da aka gaya wa mutane yadda yake, suna da damar kallon abin gwargwadon hankalinsu. Ba dole ba ne a ce, fassarar da mai ba da labari zai yi, ita ce wadda mai saurarensa zai yi ba. Haka kuma, al’adun mutanen duniya sun sha bamban. Yadda Bature zai hangi nasara da buwaya da jaruntaka da ƙwazo, ba haka Bahaushe zai hange su ba. Wannan ishara ne ga ma’aikatan jaridun duniya domin su tabbata sun ƙoshi da al’adun harsuna biyu da suke fassara labarai. A ganin Bahaushe, gwarzo ko jarumi shi ne, wanda ya yi tsayin daka ga fahintarsa ko da za a ta jawo masa hasarar rayuwarsa. A Hausance, Usama gwarzo ne da ya mutu da ‘yancinsa. A aƙidar Larabawa cewa suka yi:
Man lam yamut bis saifi maata bi gairi hi,
Tanawwa’atil asbaabu wal mautu waahidun.
Manazarta:

Ali, M.A. (2010) “Effect of War on Terror by the West on Islam and
Muslims” (Sick) Being a draft of M.A Dissertation Submitted to the Department of Islamic Studies, FAIS, UDU Sokoto.

Ali, T. (2002) The Clash of Fundamentalism: Crusades, Jiahd and
Modernity, Verso, London.

Awake, (1987) The New Look of Terrorism, Watch Tower, Lagos.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada, TIWAL Nigeria Ltd, Lagos,
Nigeria.

Bunza, A.M., Ibrahim, S.S. Usman B.B. (2007) Daular Sakkwato,
(Fassarar Sokoto Caliphate na Murray Last). Ibrash, Lagos, Nigeria.

Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa, Ibrash. Lagos-Nigeria.

Gunaratna, R. (2002) Inside Al-Qa’eda, Berkley Books, New York.

Revero, M. (2002) Fake Terror: The Road to Dictorship.

No comments:

Post a Comment