Monday, November 26, 2018

Labarin Zuciya A Tambayi Fuska: (Saƙon Dariya Ga Sasanta Tsaro A Farfajiyar Karatun Hausa)
Tunanin Bahaushe na faɗar Allah ɗaya gari bamban, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Dadaɗɗen tarihin ƙasar Hausa sassarƙe yake da ƙurar yaƙi da gaba da bauta tun gabanin wata duniya ta kutso cikin duniyar ƙasar Hausa. Bayan an yi kare jini biri jini, aka rabu dutsi a hannun riga, sai tunanin a share jini a koma wasa ya haɗu da tunanin faɗan da ya fi ƙarfinka ka mayar da shi wasa, suka hamɓare gwannatin, kar! Ta san kar!, suka kafa sabuwar daular zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Yadda Bahaushe ya yi amfani da wasannin barkwanci wajen kashe wutar gaba da ƙiyayya da yaƙe-yaƙen jahiliyya suka haifar abin a zo a gani a yi nazari ne. Dabarar mayar da dariya da tashin hankali taubasan juna, Bahaushe ya fara kaɗaita da ita, da fice da ita a duniyar baƙar fata. Cikin halin da ƙasarmu take ciki a yau, Hausawa suka fi kowace al’umma….

Labarin Zuciya A Tambayi Fuska: (Saƙon Dariya Ga Sasanta Tsaro A Farfajiyar Karatun Hausa)


Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 0803 431 6508Takardar da aka gabatar a Bukukuwan Makon Hausa na shekarar 2015 na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adwa, Katsina, ranar Litinin 15/06/2015 a Babban Ɗakin Taro na Jami’ar.


Gabatarwa:
Tunanin Bahaushe na faɗar Allah ɗaya gari bamban, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Dadaɗɗen tarihin ƙasar Hausa sassarƙe yake da ƙurar yaƙi da gaba da bauta tun gabanin wata duniya ta kutso cikin duniyar ƙasar Hausa. Bayan an yi kare jini biri jini, aka rabu dutsi a hannun riga, sai tunanin a share jini a koma wasa ya haɗu da tunanin faɗan da ya fi ƙarfinka ka mayar da shi wasa, suka hamɓare gwannatin, kar! Ta san kar!, suka kafa sabuwar daular zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Yadda Bahaushe ya yi amfani da wasannin barkwanci wajen kashe wutar gaba da ƙiyayya da yaƙe-yaƙen jahiliyya suka haifar abin a zo a gani a yi nazari ne. Dabarar mayar da dariya da tashin hankali taubasan juna, Bahaushe ya fara kaɗaita da ita, da fice da ita a duniyar baƙar fata. Cikin halin da ƙasarmu take ciki a yau, Hausawa suka fi kowace al’umma cancanta ga ba da misalin yadda za a sallami tashin hankali, ba tare da ya yi halinsa na tayar wa kowa hankali ba. Bisa ga wannan ƙuduri na sa wa takardarmu take: Labarin Zuciya a Tambayi Fuska. Da fatar za ku ba ni aron zukatanku in labarta muku abubuwan na na ƙunso, mu ga yadda fuskokinku za su ba da labarin abubuwan da aka ɗuɗɗura musu.

Warware Matashiya:
Karin maganganun Hausawa wata babbar makaranta ce, babu ɗalibin da zai ce, “Yau ya sauke karatunta” sai dai a dangane allo, in an kai walan waladaina walan malam na ƙiya. Labari kalmar Larabci ce daga khabar al-akhbar asalin ma’anarsa a Hausa ita ce, sabuwar magana ko ƙaramar magana ko babbar magana ko tsegumi ko tsince ko jita-jita ko yaye-yayen maganganu. Duk waɗannan na iya fassara “labari” a Hausa. Duk da haka, abubuwan da suka ƙunshi tarihi da karatu, magabata na yi musu bugun goro da sunan “kunne ya girmi kaka”. Zuciya kuwa wata babbar tsoka ce daga cikin tsokokin kayan cikin mutum da Bahaushe ke ganin ita ce taskar kowane irin tunaninsa da halayensa da ayyukansa. Fuska wani madubin tantance ɗan Adam ce da ta haɗa da baki da hanci da idanu da goshi da gemu. A ko’ina aka tunkari mutum, fuskarsa ce a bar tabbatar da shi, da ita ake rarrabe shi da waninsa, ita ke sa ya  yi kama da wani, kuma da ita ake fahintar, kama da wane ba wane ba ne.
 A al’adance, ana son fuska ta kasance sakakkiya shimfiɗaɗɗiya domin masana cewa suka yi, “Shimfiɗar fuska ya fi shimfiɗar tabarma. Ba a son fuska da duhu-duhu irin ta majiyi yunwa don haka Bahaushe ke cewa: “Annurin fuska kaurin hanji”. Ba a son a gan ta nugu-nugu wanda zai ba da fassarar talallaɓiyar kashi ba a faɗi ba rai ya ɓaci. Abubuwan da ke sosa rai suna sa fuska baƙi (a al’adance) komai farin jikin mai ita, wanda shi ne musabbabin zancen Bahaushe na cewa; ya sha toka, ko ya sha mur, ko ya yi fuskar shanu domin maraƙi da ya ƙoshi, da yana cikin jin yunwa, duk ba a iya rarrabewa a fuskarsa. Na yarda da kirari sanƙiran Gambo zuwa ga Muhammadu Inuwa Ɗan’maɗacci da yake cewa:
Baƙi ƙirin ɓarin mai toka
Sa ba ka dariya sai tuni
Kowa yag ga dariyar sa ya mutu.

Ma’abota hankali da sun ga waɗanda suka sani da fara’a, fuska turnuƙe, sukan ce, “wane lafiya? Me ke faruwa?” Haka kuma, idan an ga maƙetaci na yaƙar dariya akan tuhumi masiba ta auka wa wani ko wasu. Ire-iren mutanen nan ne da Bahaushe ke cewa: “Mugu ba ka dariya sai ta ɓaci”. A kan kowane hali, yamutse fuska irin ta ‘yan kuwwar gobara, da dabirta ta, kamar wanda aka koro abin zargi ne. Ba a son ta kasance tsaroro irin ta ‘yan tatsar hanji. Idan ta fi ta Nufawa da Kutumbawa kauri ana yi mata zaton artabu. Da mai tambaya zai yi tambaya cewa: Me ke sa a kasa gano makarin mutum? Bayani shi ne, fuskarsa. Me ke sa a fahinci manufarsa? Fuskarsa. Me ke sa a samu tabbacin amincewarsa da yardarsa da ganewarsa? Murmushinsa ko dariyarsa. Waɗannan abubuwa biyu “murmushi” da “dariya” gaɓɓan da ke bayyanar da su a fuska suke liƙe. Don haka, muna da damar mu ce, lallai tunanin Bahaushe na labarin zuciya a tambayi fuska ba shege ba ne da ubansa.

Ƙasar Hausa da Daulolinta:
Idan an ce ƙasar Hausa, wata irin wagegiyar farfajiya ce da za a iya cewa, daji ba ka da gambu. A taƙaice, za mu ce, ƙasar Hausa ita ce:
Farfajiyar da Hausawan asali suka yanke cibi. Makekiyar ƙasar da Hausawa suka mamaye su kaɗai, a nan ciki kakanin kakaninsu suka tsira. Nan suka sami kansu, a nan aka same su. Ba su san wata ƙasa ba sai ita. Ba a san su a ko’ina ba, sai a nan. Ba su yi tarayyarta da kowa ba. Ba ga kowa suka karɓe ta ba, kuma babu wanda ya yi musu masauki a cikinta. Da ita suka tinƙaho, domin ba su san ko’ina ba baya ta. Da ita ake yi musu suna da garuruwansu da daulolinsu da zuriyarsu da addinansu da al’adunsu. A doronta suka kakkafa mazauninsu na din-din-din mannanu ƙuda ya faɗa ƙwarya alewa.

A taƙaice bayani, wannan ita ce ƙasar Hausa. A fashin baƙinta, ta ƙunshi dauloli irin su Kano da Zazzau da Katsina da Zamfara da Gobir da Kabi da farfajiyar Maraɗi da Filinge da Dogon Dutsi, da dai makamantansu. A tarihi, a duniyar baƙar fata, babu ƙabilar da ta kai Hausawa dauloli girkakku. Haka kuma, babu ƙabilar da ta zarce ta faɗin farfajiyar mazauni. Ba a ce ta fi kowace ƙasa dausayi ba, amma a jigawar ƙasa, da karkarar kowace al’umma tana gwada tsawo. A awon yawan jama’a, ko ba a gwada ba, linzami ya fi bakin kaza. A fagen karɓar baƙi, da yi musu shimfiɗar fuska, a duniyar baƙar fata, ba sai Bahaushe ya yi kirari ba, ai ko ba a faɗi ba, sunan mijin iya baba. Idan ana zance harshe mai yaɗo da bunƙasa da barbazuwa duniya kamar iskan hunturu, da an ce, “Hausa” dole a ji shiru mai kiɗin kalangu ya faɗa rijiya! Nagarta da basira da wayo da kazar-kazar sai mu yi na babban mahaukaci mu ce, a ko’ina Bahaushe ya miƙe tsaye ko bai ce uffan ba, an san biri ya yi kama da mutum. Wannan martaba ta sa, a halin yanzu, babu ƙasar da ta kai ƙasar Hausa cika da mutane mabambanta a duniya. Haka kuma, shi ya haifar da ƙyashi da kushewa ga magabta, aka dinga kai mata hare-haren yaƙi. Bugu da ƙari, albarkatunta ya jawo mata yaƙin basasa na cikin gida, tsakanin sarakunanta kowa na ƙoƙarin ya ƙara yawan ƙasarsa arzikinsa ya ƙaru.
Idna za mu kalli hoton ƙasar Hausa sosai cikin taswirar ƙasashen duniya, za mu ga cewa, kwararowar Larabawa Musulmai da Ƙibɗawa da Turawan Mishon da ‘yan mulkin mallaka da Wangarawa da Fulani da wasu ƙananan ƙabilu fassarar sa ita ce, da walakin goro cikin miya. Lalle, dole da dalili ƙuda a warki. Ba a bin mamaki ba ne har yau, martabar ƙasar na nan yadda aka san shi, domin basira da hikimar magabata ta shafe mu, ko ba mu yi kamar su ba, za a ce, ai ɗan gafiya ko bai yi sata ba yana dogon aro. Kai! Tilas a jinjina wa makaɗa Narambaɗa a faɗarsa:

Jagora: Ɗan bajini shi ka zama bajini
          : Yai bobakali yai tozo
Yara  : Ɗan akuya na kallo!
Gindi : Na yaba ka da girma
           Audu ƙanen mai daga
          : Kan da mu san kowa
          : Kai mun ka sani Sardauna.

Zaman ‘Yan Marina:
Ga alama, zaman ‘yan marina shi ne kowa da wurin da ya fuskanta ga abin da yake yi. Daulolin ƙasar Hausa sun yi zama irin wannan saboda adawar yaƙe-yaƙe da ta gabata. Al’ummomin da ke cikinsu ana iya rarrabe su da sunayensu da al’adunsu da kirare-kirarensu. Idan muka nazarce su sosai, za mu gano dalilan da suka haifar da yaƙe-yaƙe da dalilan da suka haifar da sulhu aka zama abu ɗaya. Ga tsarin zuriyar Bahaushe: Bakano, Bahaɗeje, Bakatsine, Bazazzage, Bazamfare, Bagobiri, Bakabe, Bagimbane, Ba’are, Bagube, Badaure, Bamaraɗe, ga su nan dai. Waɗannan kowannensu da karin harshensa, da tsagarsa ta gado da sunan sarautarsa da sunan ƙasarsu da tsarin wasanninsu da yanayin abincinsu da tarihin kakaninsu mabambanta da al’adun matakan rayuwarsu (aure da haihuwa da mutuwa) da bukukuwansu da magungunansu na gargajiya, da tsarin yadda suke raɗa sunayensu. Idan muka kalli waɗannan abubuwa da idon karatu, a ko’ina suka bayyana, dole a samu saɓanin fahimta. Da zarar saɓani ya bayyana, tankiya dole ta shiga, daga nan, zai zare damuttsa da takubba da gaturra da kibau da masu na ɗebe raini da huce haushin juna. A tarihin duniya, babu al’ummar da ba ta ratsi irin wannan jahiliyya ba, don haka Bahaushe ba shi ne farau ba, shege kowa ya yi, ɗan karuwa na faɗa da jikan kwarto.
A wajen ƙasa, Kanawa sun zuba da Jukunawa. Zage-zagi sun zunguri Gwarawa. Katsinawa ba su raga wa Nufawa hakin susa ba. Kabawa sun yi adashin kibau da masu da Fulani. Fulanin ƙasar Hausa sun fafata da daular Borno. Zamfara da Dakarkari sun yi luguden kulake da gaturra. Gobirawa da su da mutuwa ɗan gwaggo da ɗan kawu ne, takubbansu ba su taɓa tsatsa cikin kube ba, don haka yawan yaƙe-yaƙensu sai dai abin da kunne ya ji. Waɗannan yaƙe-yaƙe da zuriyar Hausawa suka yi da ƙabilu maƙwabta da na nesa, shi ya sa ƙasar Hausa take zaman ‘yan marina da maƙwabtanta domin gudun a yi mata girshi. Wataƙila irin haka ce Aliyu Ɗandawo ke yi wa daular Kabi hasashe a bakandamiyarsa ta yaƙi da yake cewa:
Jagora: Bayan shekara dubu biyu
: Sannan Nabane yab bayyana
: Yag gagari Hillani
: Yaf fanshi Kabawa
: Da ruwan kibau da masu
: Ko sun yi ƙulle-ƙullensu
: Ina ruwan sadauki
: Ka dai buwaya ka gagara
: Ko bindiga an tanka ƙari bai tosai.
          Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani
                   : Ila marin rugga
                   : Ɗan Yakubu sa gurfani!

Tirƙashi! Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Idan ba a sa tulun ruwan tobassaka ba aka yayyafa wa turruƙun hayaƙin da makaɗa Aliyu Ɗandawo ya turara a zukatan Kabawa ba, kuna ganin kasuwar Ambursa na sake cika? To! Waɗannan miyaku muke son mu rego yadda magabata suka sa musu bandeji aka ɗaɗɗaure su har suka warke aka wayi gari yau, takubban yaƙi suka koma gidan tarihi, ana regonsu, ana nunin su, ba tare da tunanin rataya su ba.

A Share Jini A Koma Wasa:
A tarihin ƙasashenmu ƙananan yaƙe-yaƙen da aka sha gwabzawa sai dai abin da aka ji amma ba sa lisafuwa. Idan aka dubi irin darzajen da Kabawa suka yi ƙarƙashin Sarki Kanta dole a kame baki. Kaɗan daga ciki, Daular Kabi hannun rigarta na yaƙi ya kai har Nguru a daular Borno. Ƙafan wandonta na kokuwa da mazaje ya tokare Daular  Oyo, ta tsohuwar Daular Oyo. Tsinin kibau na masunta sun ratsa Dahomy sun ziyarci Agadas har Air. Hurjin Mussan Kabi bai bar Nufawa ba, domin har sa su yaɓi da man kaɗe aka yi a birnin Surame. Sarki Kabi Sama kaɗai garuruwan Filani tis’in da tara (99) ya ci da yaƙi. Kanawa sun ɗauko sarkin yaƙi Ɗanwaire Marin Dawa sun ci garuruwa da dama. Gwandu ta ɗauko hayar Garba Gande (Janborodo) domin ya yi mata gambun yaƙi a Ambursa. Yaƙe-yaƙen ƙasashenmu su suka karantar da mu cewa, dole a share jini a koma wasa. A yau kamar ba a yi ba, domin:
Kanawa sun zama abokan wasan Zazzagawa
Kabawa su ne manyan tobassan Fulani
Gobir, da Fulani da Yarbawa da Katsinawa nata ne.
Katsinawa, da Kabawa da Nufawa tobassansu ne.
Gimbamawa da arawa sai lalewa
Katsinawa da Dakarkari ‘yan’uwan juna ne.
Bazamfare da Badakkare an zama ɗan gwaggo da ɗan kawu.

A taƙaice, masana al’ada na ganin yaƙe-yaƙen da al’ummomin ƙasar Hausa suka yi da wasu ƙasashe da kuma tsakaninsu, su suka haifar da wasannin da ke gudana a yau. An riga an fahinci juna, an gama jiki kowa ya san wurin da wani ya kwana. Da wanda ya yi rinjaye, da wanda aka rinjaya, kowa ya miƙa wa zaman lafiya wuya, an riga an karce majinar da ta toshe zuciya, fuskoki sun waye, an shimfiɗa su ga juna sai ‘yan habaice-habaice da ke iya kai da kawo. A shekarar da aka je tarbon sarauniya Kaduna makaɗa Aliyu Ɗandawo ya san, sai an ratsi ƙasar Sakkwato, ya ko san irin artabun ƙarshe da aka yi da Sanyinnawa bayan tamburan yaƙin Fulani da aka karɓe a fagen gumuzu. Don haka yake cewa Sarkin Kabi Mamman Shehe:
Jagora: In tahiya ta kama
          : Ka sa a shirya dawaki
          : A ɗaura damman masu
: Ko suna taya fansa
: Ka tabbata ma maza
: Ba a girsuwan mai ƙarfi
: Ka dai gagara (ka buwaya)
: Don mai da hwaɗi ɓanna na
: Shugaban tahiya sarkin Kabi mai Sudani
: Ila marin rugga,
: Ɗan Yakubu sa gurhwani.
Me ya sa makaɗa ya ce: “Mai da hwaɗi ɓauna na”? Domin an riga an share jini don haka, sai a koma wasa kawai. Kowa ya san ƙarfin kowa, a ba zaman lafiya dama ya ci gaba da wanzuwa a ƙasa. Haka ko aka yi, yau auratayya da kasuwanci da addini da hulɗa da zamantakewa sun kore dukkanin waɗannan abubuwa da ke yi muna barazana mun zama abu ɗaya.

Wasa Da Dariya Ga Bahaushe:
Ba al’ummar duniya da ba a wasa. Babu al’ummar duniya da ba a dariya da kuka da murmushi da shewa da kuwwa da guɗa da kirari. Duk da haka, dariya ta fi amo sosai a tsarin zaman lafiyar al’umma. A koyaushe, a maganganun yau da gobe, akan haɗa kalmomi biyu “wasa’ da “dariya” su ba da kalmomi biyu masu zaman kansu, amma masu ma’ana ɗaya. A al’adance, ko’ina aka ga wasa, ana sa ran jin zarmoɗan dariya. A kowane lokaci aka ga fuska ta kece da dariya, to wasa a aikace ko a lafazance ta gabace ta. Kalmar “wasa” takan ɗauki ma’anoni da dama irin su:
i)                  Wasa da gaɓɓan jiki domin samar da raha da wartsakewa.
ii)               Maganganun raha na motsar da annashawa da tuna baya.
iii)             Wasu ayyukan al’ada na burgewa da samar da raha.
iv)             Wasannin gargajiya da al’ada ta katangance da sunan “wasa”.
v)                Yunƙurin yin wani abu, ba haƙiƙaninsa ba, ko ba da gaske ba.
vi)             Ƙirƙirarrun labarai, ƙagaggun na kunne ya grimi kaka.
vii)          Dabarun fitar da kai cikin tukunya idan ruwa sun ci gwani.
A ɓangaren dariya akwai abubuwan ambato da yawa. A ilmance, a ƙarninmu ita kaɗai ke da ƙungiya ɗaya a duniya, “ƙungiyar Dariya ta Duniya”. Har yanzu, ba mu ji ƙungiyar kuka ko gudu ko kuwwa ko shewa ko guɗa ko gwalo ko jinini ta duniya ba. A al’adance, dariya wata makaranta ce ta zuzzurfan karatun:
i)       Zuciyar mai aiwatar da ita
ii)      Halin da mai yin ta yake ciki
iii)     Shafin da mai yin ta ya buɗa daga cikin shafukanta (14).
iɓ)     Abubuwan da mai ita ya hango gabanin ya yi ta.
ɓ)      Yadda yake cin ta, wani rukuni ne daga rukunan dalilanta.
ɓi)     Da ta bayyana fara’a da bushara sun tabbata, a mabayyanin zance
ɓii)    Ba su taɓa haɗa hanya da kuka ba, kuma ba su taɓa yada zango ɗaya ba.

Fashin Baƙin Dariyar Bahaushe:
Ba Bahaushe kaɗai ke dariya ba, amma kuma yana daga cikin al’ummomin da ke ganin da ita ake gyaran zama na baya a walle. Sanin wahalhalun da ke cikin yaƙe-yaƙe da musibun da suka haifar da bi-ta-da-ƙullin da zai biyo bayan su. Bahaushe a kowace ƙasa ya kafa daularsa, ta kowace irin fuska gwannatinsa ta kafu, yana da manyan ma’aikatun da za su kula masa da walwala, irin ta sakewa, da wanzar da raha, dariya ta baje kolinta a bakunan mazauna ƙasarsa. Daga cikin martabobin dariya ga masana halayyar ɗan Adam a al’adance, akwai:
i)                  Duk wani baƙin ciki ake  ciki da ta bayyana ya kau.
ii)               Duk wata fargaba da ake ji, da an gan ta an samu natsuwa.
iii)             Komai tsauri tsananin mutum, da ta bayyana a fuskarsa, an samu makama gare shi.
iv)             Ba a taɓa yin ta cikin tashin hankali ba, sai nasuwa ta wanzu za ta bayyana.
v)                Bayan ɗan Adam, babu wata halitta mai rai da ke dariya.
vi)             Husuma, faɗa, yaƙi, artabu, zanga-zanga da fito-na-fito da taho-mu-gama cikin fuskar shanu ake kwasar adashinsu, da dariya ta gitta sun tsinke, sai zancen sasantawa.
vii)          Ɗaurewa a ƙi yin ta da’iman rauni ne ga hankali, dogewa da ita juddadun alamar taɓuwar hankali ce.
Ganin irin waɗannan martabobi ya sa Bahaushe ya keɓe babbar farfajiya domin raha da dariya a adabinsa. A adabi da al’adar Bahaushe akwai:
1.                 Makaɗan Ban dariya
i)                  ‘Yan kama
ii)               ‘Yan zari
iii)             ‘Yan kacakaura
iv)             ‘Yan gambara
2.                 Wasannin Barkwanci Tsakanin ƙabilu
3.                 Wasannin Barkwanci Tsakanin masu sana’a
4.                 Wasannin Barkwanci na zumuntar jini
5.                 Wasannin Barkwanci na Takwara
6.                 Wasannin Barkwanci na Jinsi
7.                 Wasannin Barkwanci na Ƙirar Halitta
8.                 Wasannin Barkwanci na Naƙasassu
9.                 Wasannin Barkwanci na dabbobi da tsuntsaye da ƙwari
10.            Wasannin Barkwanci Tsakanin Al’ummomi
11.            Wasannin Barkwanci Tsakanin ƙauyawa da ‘yan Birni
12.            Wasannin Barkwanci Tsakanin Zuriyar Bahaushe
13.            Wasannin Tashe
14.            Wasannin zamantakewa
15.            Wasan Bashirwa
Kowane rukuni muka shiga cikin waɗannan rukuna za mu ga babban fage ne abin nazari. Haka kuma, za mu taras da babban jigonsa shi ne wanzar da raha a zukatan ‘yan kallo da masu sauraro. Da raha ta ratsi zuciya, babbann masaukinta a fuska shi ne gangar baki, babban kogon da dariya ke haramta wa kowane irin abu shigansa idan ta baje kolinta a ciki. Idan muka nazarci waɗannan rukunan wasanni za mu ga, daga cikin adabin Bahaushe, dariya ke da kaso mai rinjaye. Yaƙi da faɗa da gaba wasu lalurori ne da yanayin zamantakewa kan haifarwa, ba su da wani babban gurbi daga cikin gurabun tsaftatacciyar rayuwa. Idan cilas ta haddasa su, sai a ziyarci ɗaya ko biyu (ko fiye) daga cikin waɗannan rukuna a tunkare su a murƙushe su gabanin su tashi. Idan sun riga sun tashi, a yi amfani da su a yayyafa musu ruwa a kashe lagonsu. Idan an riga an gwabza sai su biyo baya da lallashin zukata na a share jini a koma wasa.

Ƙunshiyar Karatun Dariya:
Dariya babbar makaranta ce mai suna: “Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa Gaskiya”. A koyaushe aka buɗe littattafanta ana karatu, fuskokin masu karatu, da ɗaliban ilminta, za su ba da labarin abin da ake ciki. Idan baƙon makarantar ya zo bai san abin da ake ciki ba, ya tambayi karatun aka gaya masa shi ma dole ya dara. Daga cikin manyan darusan da ke ƙunshe cikin dariya akwai:
1.                 Tarihin tuna baya
2.                 Kyautata zamantakewa
3.                 Tattalin arziki
4.                 Zaman lafiya da lumana
5.                 Taskace al’adu nagartattu
6.                 Kakkaɓe ƙurar gaba da takaici da ƙiyayya a zukata
7.                 Karatun duniyar mutane da fahintar junansu
8.                 Danƙon sada zumunci
9.                 Fahintar addini/addinai
10.            Kyautata tarbiya
11.            Kiyon lafiya
12.            Inganta siyasar duniya
13.            Yalwata harshe da ɗaukaka shi da inganta shi
14.            Dabarun yaƙi da dabarun tsagaita/tsakaita wuta.
15.            Kimiyyar ƙere-ƙere
16.            Sanin makamar aiki
17.            Fahintar dokoki da hukunce-hukunce
18.            Dabarun tsaro
19.            Sanin kai da sanin yakamata
20.            Tsaron hankali da mutunci
Abin da ake son mai karatu ya kula shi ne, cikin kowace dariya akwai darasi ga wanda ya yi ta, da wanda aka sa ya yi, da abin da ya sa aka yi dariya a kai. Darusa ashirin da muka tsakuro a nan kaɗan ne ƙwarai daga cikin darusan da ke ƙunshe cikin dariya. Kowane darasi daga cikin darusan idan aka tsaya aka fyace shi sarai, za a tabbatar da cewa ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Bari mu ɗan waiwayi wani fasali daga cikin fasulan da muka fayyace mu gwada tsawonsa da duniyar zamaninmu da muke ciki.

Dabarun Tsaro:
Hausawa na cewa, lokacin abu a yi shi. Halin da muke ciki a ƙarsamu ya kyautu a ce, dukkanin karance-karancenmu da nazarce-nazarcenmu, su tunkari halin da ƙasar da muke ciki su ba ta kyakkyawan agaji. Abubuwan da suka haddasa taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya ba karatun rana ɗaya ba ne, domin ba rana ɗaya suka faru ba, bale wata gwannatin yini biyu,  ta ce, za ta ga bayan su. Tattare da sanin haka, dole mu ce alhakin tsaro ga hannun shugabanci yake domin Hauswa sun ce, wanda duk ya ɗauri kura shi ke da alhakin kwance ta. Idan muka harari tunanin Bahaushe na cewa, “wanda ya ce zai haɗiye gatari riƙe masa ƙota, ina laifin mariƙi ƙota/ɓota da ‘yan kallon yadda za a haɗiye. A koyaushe fitina ta ɓare, Bahaushe na ganin dole shugaba ya sa gaba ya tara, domin mai sanda ke da fasalin bugu. Idan shugaba ya samu kansa cikin rashin kwanciyar hankali ga waɗanda yake jagoranta, ya kula da waɗannan abubuwa ya gani:

Maƙarrabansa:
Tunanin Bahaushe na, ba a mugun sarki sai mugun bafade dole a koma gare shi. Idan an shiga tatsaka mai wuya dabarar shugaba kaɗai ba ta fitar da suhe wuta. Dabarar matasa masu sabon jinin ƙara dagule bakin zare take yi. A riwayar tatsuniyar shugaban ƙasa Zaki da ‘yan ƙasarsa dabbobi abin karatu ne.
Zaki ya umurci kowane ɗan ƙasa ya je ya kashe mahaifansa a manta da duk wani tsohon alkawali a kafa sabon alƙawali a tsarin gwannati. Kowa ya zartar da umurnin da aka ba shi, sai zomo kawai ya je ya gaya wa iyayensa suka ce: “Ka da ya yi, ya ɓoye su. Bayan an gama ta’asa, aka je faɗa zaki ya ce: “Ina son a gina mini babbar fada da ba ta ƙasa, ba ta sama, in dinga lilo ina shaƙatawa”. Ya ƙara da cewa: “Na ba da kwana ɗaya kowa ya je ya yi tunani yadda za a yi. In an kasa kowa ya zo da likkafanin jana’izar gawar kansa”. Da adadi ya cika, kowa ya zo yana hawaye. Zomo ya je ya gaya wa mahaifansa suka gaya masa cewa: “In ka je ka ce, ya fara aza harsashe za ku idar”. Zomo na faɗar haka, zaki ya ƙauyanta da shi neman sulhu.

Wace hauka da wauta da dambala da ɗimancewa ta fi a ba ka wuta ka cinna wa gidanku da ba ka da wani gida sai shi? Bayan ka ƙona shi ina za ka zauna? Bayan ka kashe ‘yan uwanka da ‘yan uwan wa za ka zauna? Wanda ya sa ka ta’asar da sunan wai! Aikin tsaron ƙasa, in ƙasar ta ɓare, ina za ka je? Shi ko ina zai koma? Haba aboki! Ai aiki da hankali ya fi aiki da agogon hannu.

Hankalin Jama’ar da ake Shugabanta:
Dole ne shugaba da waɗanda ke taimaka masa su riƙa sara suna duban bakin gatari. Idan tsaron ƙasa ya yi cin alewar kuturu, ka da a yi zaton talakawa ba su da hankalin sanin ina aka dosa? Tunaninsu a koyaushe shi ne, akwai ranar ƙin dillanci. Game takai da ma’aikatan hukuma a wawuce arzikin ƙasa shi ne musabbabin fitina da yaƙi a kowace ƙasa. Idan talakawa suka fahinci da jininsu ake amfani, a kashe su, za su mayar da amsar tambayar izgili da gatse. Dubi jawabin sarkin kutare da dangaladimansa da talakawansu:
An ce, sarkin kutare ya gaya wa kutare ya kamata a samu ranar da za a daina bara. A shirya kacici-kaci, wanda duk ya ci nasara, a je gidansa a yi liyafar shekara. Sarki ya game baki da Dangaladimansa, ya gaya masa tambayar da zai yi, da irin amsar da zai bayar, domin su tsira da mulkinsu da dukiyarsu. Sarki ya hau karaga ya ce: “Ga tambaya: Wani abu ne ƙato, mai ƙaton kunne, mai ƙaton baki, mai ƙaton ciki shi ake hawa zuwa bara. Mene ne shi”? Aka yi tsit! Dangaladima ya ɗagar da daginsa ya ce, “Na san shi”. Sarki ya ce: “Mene ne”? Dangaladima ya ce: “Kifi”. Sarki ya ce: Kayya! Ba ka gane ba”. Talakawa suka ce: “Wallahi ya gane, kifi ne! Kifi ne!” Dangaladima ya ce: “Wallahi ban gane ba”. Talakawa suka ce: “Wallahi ka gane, kifi ne”.

Na tabbata matsalolin tsaron ƙasar nan ya kusa ga ya kai haka. Da shugabanni da talakawa kowa kallon-kallon yake yi wa juna. Shugaba da kansa ya ce, ya san musabbabin rashin tsaro duniya ta jiya ta yarda. Da baya ya dawo ya ce, bai gane ba kure ya yi, me ake son talakawa su yi in ba zanga-zangar hankali ta fadar sarkin kutare ba? A dai ja sannu, Kabawa cewa suka yi: “Kifi na ganin ka mai jar homa”.

Matsayin ‘Yan Shawara ga Tsaron Ƙasa:
Dole sai shugaba ya rege irin matsyain ‘yan shawara yayin da ƙasarsa take cikin yaƙi. Wani ɗan shawara, tuwonsa kawai yake karewa. Wani a cikin kuɗin sayen makamai yake da nasa rabo. Wani, a fagen artabu yake kallon ganimarsa. Wani, matuƙar babu fitina da yaƙi abincinsa ya lalace. Wani, yaƙin wurin huce haushinsa ga wasu ne domin tsohuwar adawa ta addini da ƙabilanci da ɓangaranci da siyasa da kishi. Tatsuniyar wani Dunya da matansa biyu sun isa misali:
Dunya ya yi amarya, sai ya fita daji neman abincin da za a yi angwanci. Yana shiga wani gungu tarkon ya kama shi. Da matansa suka tarar da shi ɗaure cikin tarko suka kasa fitar da shi. Suka ga lallai an kai ga adadi domin maraice na gwamatsowa masu haƙo na zuwa. Amarya na cewa: “Yi fakaf! Faka! Kaman namiji kake”. Uwar gida na cewa: “Yi lahu! Kaman ka mutu”. Ya bi shawarar amarya tarko ya ƙara ɗaure shi. Ya bi shawarar uwar gida, bai ji tarko ya fita ba. A ƙarshe, ya yanke shawarar bin shawarar uwar gida ya lahe ya ɓoye lumfashi kamar ya mutu. Da mai haƙo ya zo, ya gan shi ya ga mata biyu suna kallo. Ya laluba bai ji alamun rai ba, sai ya ce: “Allah sarki, ya riga ya mutu, ba rabo ba ne”. Ya kwance ya wurgar da shi, shi ko Dunya ya ce: “In ba ka yi ba ni wuri”.

Idan za ku yi mini adalci haka matsalolin tsaron ƙasarmu yake. ‘Yan siyasar da ke cin gajiyar rashin tsaro da ‘yan tsirarrun da ake kashe wa arzikin su ka matsa cewa a ci gaba da ɓarin wuta sai an zubar da ruwan ɓula. Talakawan da musibar ke ƙarewa a kansu, su ke son a zauna a sasanta. Da an bi ta Bafulatani ta cewa, “Saki Sehu kama Jema”, da tuni ƙura ta lafa.

Karen da Duk ya yi Cizo da Gashinsa Ake Magani
Wataƙila wani zai ce, yaya za a yi sulhi da waɗanda ba a san wurin da suke ba? Wa zai yi sulhi da iska? Bayani a nan shi ne, ai ba daga sama abokan yaƙi suka faɗo ba. An san tushensa, an san waɗanda aka kama, da waɗanda aka kashe, da waɗanda ake fafatawa da su. Cikin halin da muke ciki, da masu yaƙi, da waɗanda ake yaƙa, an shiga wani rutsi da ɓaraye suka shiga ga kyanwar da ta haddabe/addabe su.
An ce, kyanwa ce ta hana wa ɓeraye shaƙatawa. A kowane maraice suka dawo da kiyo sai ta kiwace su. Suka yi taro yadda za a fuskance ta. A ƙarshe suka kai ga cewa: “A samo gwarje a ɗaura a wuyanta duk lokacin da ta taso gwarjen da ke wuyanta zai ba su labari su tsere”. Ƙarami daga cikinsu ya ce: “To wa zai je ya ɗaura mata gwarjen”?

Tunanin tsaro ƙasarmu a koyaushe manya ke sussukarsu ɗaka, shiƙa ɗaka, dahuwa ɗaka, sai ta ɓaci a sayo makamai a ba soje da wakilan tsaro, a ce su je su kashe ‘yan’uwansu. Idan an rinjaye su ko suka ga musibar da ke ciki da bita-da-ƙullin da zai biyo baya suka ja da baya a hukunta su. Lokaci ya yi a yi twa-da-twa wankin ɗan kanoma mashaya a hura wuta kowa ya ga rabonsa. A yau, daidai ne a binciki kowa, komai muƙaminsa a hukuma, a tabbata an kai ƙarshen yaƙin da muke ciki domin Hausawa cewa suke yi: “In raƙuminka ya ɓata babu laifi cikin fafitikar nemansa ka leƙa akurki domin ɗebe tababa”.

Ka Da A Je Gyaran Doro A Karya Gadon Baya:
A iya tunaninmu mai ɗaki ya san gefen da ɗakinsa ke tarara haka kuma ba mu da saɓanin cewa, mai baibaya ya san wurin da ya tsohe makwararar ruwa. Akwai rashin adalci ga rabon faɗan baƙauye, kowane yaro a doki kansa a ce, ya yi gidansu, ba tare da bahasi ba, an ce, gobe a zo a ƙara. Haka kuma, mai shiga tsakani dole a tabbata cancantarsa da dacewarsa domin a tura Bakabe sasanta yaƙi tsakanin Gobirawa da Fulani, to! Maganar Gambo za ta yi tasiri:
Jagora: Ko ban hwaɗi ba
          : Wanda ak kusa
          : Dut ya san nuhina
                   (Waƙar Kwastan).
Zumuɗin da ake yi na sawo ƙasashen waje cikin rikicin cikin gida zai iya haifar da rabon faɗan sarkin Aljan:
Shi ya tarar da yara uku na faɗa
Ya kama ɗaya ya jefa matattar rijiya
Ya kama ɗaya ya ƙwaƙwale ido biyu,
Ya kama ɗaya ya karya wuya
Ya ce: “Ba don na taho ba da faɗa ya ɓaci”.
Waɗanda muke ta ƙoƙarin kira su zo su kawo agaji, mu dubi yaya a gajinsu ya kasance Afganistan? Yaya aka kwashe adashin a Iraƙi? Me agajinsu ya haifar a Libya? Wace riba aka ci a Somaliya? Wa ya more cetonsu a Syria? Me ya haifar da fitinar Misra? Ai mun ɗanɗana azabar su da Ujuku ya ƙirƙiro Biafara. Ba bita-da-ƙullinta ne ke biye da wargaza haɗin kan ƙasarmu ba?

Sanin Wurin Bugu Shi Ne Ƙira:
Masana cewa suka yi, mutum duka aikin da ya iya shi ake sa shi, idan dai ba so ake a ja masa wahala ba. Kiyayewa da wannan ya sa Hausawa ke cewa: “Ba a fafe gora ranar tafiya”. Amfanin wakilan tsaro tabbatar da tsaro amma ba su ne tashin hankali ba, ba su san wurin da yake kwana ba, bale su yi masa kwanton ɓauna. Su kansu, idan sun gan shi za a riƙa nesa da nesa karen mai komo. Labarin wani mahauci da ya balbalo a guje ya faɗa motar ‘yan sanda ta sintiri, ya isa babban misali:
An ce, wani mahaukaci ne da abin ya motsa ya dako sura ya daka tsalla ya faɗa motar sintiri ta ‘yan operation wurjanjan ba su tsaya tambayan mafari ba. Nan take da saja da kofur da insifacto suka nemi agajin dugadugansu. Aka tsallake mota da bindigogi da barkonon tsohuwa da inkwa a wofi. Taɓaɓɓen bai ce uffan ba, ya yi kwance ciki motar. Na bar ku da sauran bayani.

Haƙiƙa Hausawa cewa suka yi, mai hankali idan ya ga kurma aguje ba zai tsaya neman bahasi ba, limanci zai yi masa, domin gani ya yi, ba labari aka ba shi ba. Matsara ƙasarmu ba tsaro suka karanta ba, yadda za a harbe waɗanda aka tunzura suka karanta. Sun riƙi bindiga a matsayin tsaro gare su idan suka yi ta’asa, kuma abin barazana ga waɗanda aka tattarwarsa domin biyan buƙatar son ran waɗanda ke kan karagar iko. Da sun san fitina farin sani, da tuni an sasanta a murƙushe kangara. Dubi abin da ya gudana tsakanin tsohon ɗan sane da yara ‘yan sane a kasuwar Sakkwato:
Wani fitaccen ɗan sane tubabbe aka sama wa aikin yi a gidan siminti. Biyan albashinsa na farko ya saka kuɗin aljihun gaba ya shiga kasuwa. Yana shiga ‘yan makarantarsa suka zare su. Ya kama yaron (ɓarawon) ya ɗora a ka, ya doshi bayan kasuwa ya sauke shi ya ce: “Ba ni kuɗina”. Yaro ya ciro kuɗinsa ya ba shi. Ya mare shi, ya ce: “Kawo saura”. Yaro ya ciro wasu, da ba nasa ba ya ba shi. Ya kai wa yaro ƙoso, ya ce: “Ina na aljihun baya”? yaro ya zaro ya bayar. Ya doki cinyar yaro ya ce: “Ina ‘yan rakiyar ƙasa”? yaro ya san in ba ɓarawo ba, babu wanda ya san da aljihun bante, yaron ya yi dariya ya ce: “Shege baba, halama ana da niyyar zuwa hajji bana”? Oga ya ce: “Muna da niyya”, yaro ya ce: “Don Allah a isar da gaisuwarmu ga Manzo (SAW)”.

Idan ba ka san abu ba, yaya za ka tunkara shi? Ƙarshen ta waɗanda ake tsaro sun fi wakilan tsaro sanin yadda ake tsaro. Idan al’amari ya koma kiɗin ‘yan hamsin me za a ce:
:Kai mai kiɗi kiɗa in jiya
: Ba ka da aiki ni ba ni da
: Mu taru mu lalace mu duka.

Naɗewa:
Na tabbata wannan ɗan tsakure zai ba mu hasken cewa, tsaron ƙasarmu ya koma kurar Gardi. Yanzu mun kai kowa ya tsira da karatun bakinsa. Ayau mun kai, da mu da ake tsaro da waɗanda ke tsaronmu kowa ba ya da wani ilmi sai na gudu. Da ganin fuskokinmu an san zukatanmu a yamutse suke. An ƙure tunaninmu da dabarunmu na ɗan bokonmu mun ƙi yarda mu ba da kai bori ya hau. Ai da mun fahinci da ƙyar na tsere ya fi da ƙar aka kama ni sai mu huta da dirkaniya mota cikin randa mu yarda da cewa, da tsohuwar zuma ake magani. Yadda magabatanmu suka shashance takaicin yaƙi da dariya da barkwanci, dole mu yarda da cewa, da yau, da gobe, da jibi, da gata, da citta, duk daga jiya aka fara ƙidayarsu. Da ƙarfi soje ke murƙushe yaƙi, da yaƙin Biafara bai sake fitowa da sabon salo ba a yau. Karkashe abokan adawa da tarkwatsa musu iyali da gidajensu ba shi ne ruguza aƙidarsu ba, domin har gobe akwai Satirawa cikin ƙasar Hausa. Ka sani, na snai, kun sani, da ba don zurfin tunanin magabata ba, wa ya isa ya haɗa Babarbare da Bafulatani da Bagobiri da Bakatsine da Bakabe da Banufe da Kambari da Bakyange daula ɗaya, a yi hidima da sabga iri ɗaya har da auratayya, Bakabe ya yarda ya yi kiran salla Bafulatani ya yi limanci a ƙare salla Bagobiri ya yi wa’azi? Kai jama’a! Tsaron ƙasarmu na hannumu. Mu ke tsaron, mu ke ɓata tsaron. Ku tambayi makaɗa Narambaɗa me ya ce:
Jawabi: Ga abu nan a hwaɗi
Yaro  : Babu mai hwaɗi sai ƙus-ƙus-ƙus!
          : Akai da shi
Jagora: Wa ka hwaɗi?
Yara  : Kai ɗan baka hwaɗi.
Jagora: Wai baya ka ƙwazon tunkuɗe gaba
Yara  : Shi Allah ba yarda shikai ba,
          : Mai sharri shi ɗai yaka biya.
Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci!
Yara  : Karen ɓuki bai ɗau shawararka ba.
          : Shi maganar giwa yaka tsare
Jagora: Ku ce ma biri
Yara  : Duk dabbar da ac cikin daji,
          : Giwa taka biya.
Gindi : Ya ci maza ya kwan shina shire
          : Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
Jagora: Kai magana an ce maka: “Tsaya”.
Yara  : Ka sake an ce maka: “Bari”.
Jagora: Kai magana ka san ba a son ta
Yara  : Ka ƙi bari, waz zan mahaukaci?
Gindi : Ya ci maza....

(Ku harari waɗannan ɗiyan waƙa da kyau ga shugabancin mu na yau).

No comments:

Post a Comment