Monday, November 26, 2018

Labarin Zuciya A Tambayi Fuska: (Saƙon Dariya Ga Sasanta Tsaro A Farfajiyar Karatun Hausa)

November 26, 2018 0Tunanin Bahaushe na faɗar Allah ɗaya gari bamban, maƙwabcin mai akuya ya sayi kura. Dadaɗɗen tarihin ƙasar Hausa sassarƙe yake da ƙurar yaƙi da gaba da bauta tun gabanin wata duniya ta kutso cikin duniyar ƙasar Hausa. Bayan an yi kare jini biri jini, aka rabu dutsi a hannun riga, sai tunanin a share jini a koma wasa ya haɗu da tunanin faɗan da ya fi ƙarfinka ka mayar da shi wasa, suka hamɓare gwannatin, kar! Ta san kar!, suka kafa sabuwar daular zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Yadda Bahaushe ya yi amfani da wasannin barkwanci wajen kashe wutar gaba da ƙiyayya da yaƙe-yaƙen jahiliyya suka haifar abin a zo a gani a yi nazari ne. Dabarar mayar da dariya da tashin hankali taubasan juna, Bahaushe ya fara kaɗaita da ita, da fice da ita a duniyar baƙar fata. Cikin halin da ƙasarmu take ciki a yau, Hausawa suka fi kowace al’umma….

Sunday, November 25, 2018

Gurbin Ilmi Ga Had’in Kai Da Cigaban Al’umma

November 25, 2018 0Kowace al’umma da ci gaban magabatanta take bugun gaba. Magabata ba su da abin taƙama face alherin da suka shuka na baya na cin moriyarsa. Idan gaba ta yi kyau, ta gyara wa baya hanya nagartacciya. Rashin samun gabaci na gari ke haddasa wa baya doguwar masassara idan ba ta samu kyakkyawar kulawa ba, bakin wuta ya mutu a hannunta. To! Gudun haka ke sa, a koyaushe magabata suka hango baya na ƙwazo abin yabawa sukan shirya mata gagarumin buki na yi mata madalla irin wannan da muka hallara a yau. A mahangar addini da zamani, babu ci gaban da ya fi samun nagartaccen ilmi da zai ciyar da mai shi da al’ummarsa gaba. Naƙalin kafe ilmi a zuciya ya zauna daram! Shi ne ladabi da biyaya ga kogin da aka shawo shi, da masu…..

Noma: Igiya Mad’ura Kaya In An Yi Ba Da Kai Ba Su Watse

November 25, 2018 0Halittun da suka mamaye duniyar matane guda biyar ne: Mutane da dabbobi da tsutsaye da kwari da tsirrai. Mutane tsuntsaye da dabbobi da ƙwari da tsirrai ne abincinsu. Tsuntsaye a kan su suke shawagin biɗan abinci su. Dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da tsirrai suke kalaci. Tsuntsaye a kan su suke shawagin biɗan abincinsu. Tsirrai da toroson Mutane da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari (da nasu) ke rayar da su. Wanda ya jahilci wannan ya yi wa duniya zuwan kare ga aboki. Wanda ya haƙiƙance su bai zuwan sunge duniya ba. Sarrafa rayuwar waɗannan gabaɗayansu, su amfani mazauna duniya, yana ga hannun manoma. Ashe idan aka ce ga ƙungiyar manoma kowa na cikin ko….

Usama Bn Laden: Gwarzo ko ɗan Yaƙi? (Laluben Ma’aunin Gwarzo a Hangen makaɗan Hausa)

November 25, 2018 0


Maƙasudin wannan bincike shi ne, tantance yadda Bahaushe ke kallon jaruntaka da yadda Bature ke fassara ta’addanci. Takardar ta yi garkuwa da Usama bn Laden ta fuskar yadda duniyar Turai ke kallonsa. An yi ƙoƙarin ɗora gutsattsarin maganganun Turai kan Usama ta fuskar zarginsa, da farautarsa, da cewa da suka yi, sun kashe shi, a ma’aunin awon jaruntaka a Bahaushen hankali. Na yi ƙoƙarin laɓewa ga zantukan mawaƙan baka domin su mutane suka fi sauraro, kuma su maganganunsu suka fi naso a zuciyar Bahaushe. Don haka, na gayyato mawaƙa fitattu shahararru goma sha ɗaya su raka ni a fahinta. An tsinto ɗiyan waƙa ashirin da huɗu daga cikin waƙoƙinsu domin yi wa bayanai nagartaccen turke. An zaɓo mawaƙan daga rukunin mawaƙan sarauta da mawaƙan maza da mawaƙan sana’a da….