Monday, October 14, 2019

Hausa Da Hausawa A Duniyar Кarni Na Ashirin Da Ɗaya (Amsa Kiran Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) Ga Ranar Hausa Ta Duniya – Litinin 26 Ogusta, 2019)

October 14, 2019 0


Mutanen da ke magana da “Hausa” a matsayin harshen gado uwa da uba, kaka da kakanni su ne ‘Hausawa’. Samun tussan asalinsu na tun fil azal a garuruwan da Hausawa suka kafa, wata hujja ce ta zama Bahaushe. “Bahaushe” tilo ne na mai magana da Hausa a matsayin harshen gado, “Hausawa” jam’i ne na “Bahaushe”. A binciken magabatanmu, ‘Bahaushe’ shi ne:

Gaskiya A Кi Ki, A So Ki

October 14, 2019 0


Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta wannan waƙa ranar 8 ga watan Ogusta, shekara ta 2019. Tana da adadin baituka arba’in da biyu (42). Ta kasance ‘yar ƙwar huɗu.

Tsaro A Nijeriyar Кarninmu: Lokacin Abu A Yi Shi

October 14, 2019 0Tunanin Bahaushe a kan tsaro ya shafi tsaron lafiyar jiki da rayuwar da ke ɗawainiya da ita; tsaron ƙasa da tattalin arzikinta; wadatuwar abinci da ayyukan yi ga masu tsaro da ƙasar da ake ɗawainiyar tsarewa. Ke nan, tunanin Bahaushe na faɗar ‘tsaron kaya ya fi ban cigiya’, ya tabbatar da kasancewar tsaro makamin farko a rayuwar ɗan Adam. A fashin baƙin tsaro za mu ce, shi ne, samun walwala da sakewa da more wa ƙasa ga ɗan ƙasa, da samun cikakkiyar natsuwa da za ta gargaɗi kowace irin barazana da fargaba da tashin-tashina ga ‘yan ƙasa da baƙin da suka baƙunce ta. Samun wannan cikakken aminci shi ne tsaro ga ƙasa.

Folklore And Economic Security In Nigeria: (Alhaji Gambo Fagada a Radical Whistle Blower in Financial Crimes and Economic Genocide Matters)

October 14, 2019 0


Gambo was born in Fagada Babba, Mayyama Local Government, Kebbi State, Nigeria. His real date of birth is still under the cloud, but he claimed to be Seventy years old (70) as at 2002/2003. He died in the year 2016. By his oral testimony, he might be between 85/86 years old by the year 2018/2019 respectively. His pen name is Alhaji Muhammadu Gambo Mai Waqar Varayi. He was an accidental singer as he did not learn the art of singing from any singer of his contemporaries.

Wane Ne Narambaxa? Ibrahim Narambaxa Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)

October 14, 2019 0


‘Narambaɗa’ laƙabi ne da ake yi masa ga karyar farautarsa da ya yi wa suna Rambaɗa. An haife shi a garin Tubali shekarar 1890. Sunansa na yanka Ibrahimu, sunan mahaifinsa Buhari Maidangwale, sunan kakansa Abdulƙadir, sunan mahaifiyarsa Riba.[1] Sunan kakarsa mace Binta. Mahaifinsa Babarbare ne daga ƙasar Nijar, mahaifiyarsa mutunniyar Badarawa ce gidan Sarkin Makaɗa Ɗangwamna. Don haka, Narambaɗa

Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo

October 14, 2019 0


Asalin Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci. A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa bayi, don haka a ƙasarsu aka fara yaga wasiƙar Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’ suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar Karbala abin kula ne.

Wurin Da Babu Ƙasa Nan Ake Gardamar Kokuwa (Sharhin Littafin: Da ‘Yan Nijeriya da Buhun Gero Wa Ya Fi Yawa?)

October 14, 2019 0


Hausawa na cewa: “Komi ya ɓace maza ka biɗo shi”. Babban tunaninsu a kan haka shi ne, wuyar aiki ba a fara ba. A kowane lokaci mutane ke jayayya ana buƙatar raba gardama. Idan sa-in-sa ya yawaita, gaskiya ce ba ta bayyana ba. Da ta leƙo, ita ce raba gardama. Labarin masu yunƙurin fayyace da buhun gero da ‘yan Nijeriya wa ya fi yawa, ya bice duniyar kafafen yaɗa labarai na BBC da ƁOA da RFI da jaridun ƙasa da kafafen yaɗa labarai na jihohi. Da masoyansu, da masu mamakinsu, da masu musunsu, da masu adawa, dole su yarda da cewa, wannan al’amari ya gawurta kuma ya yi tasiri ga duniyar lokacinmu. Ganin irin ƙwazon matasan da suka assasa wannan batu, suka ba lokacinsu, da tunaninsu, na ganin sai sun kuranye yanar da ke ciki, ya san a yi wa wannan takarda taken: Wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokuwa”. Yanzu sai a biyo mu a ji ina salka ka tsatsa.